Conversation (Hausa)

Hira tsakanin Aliyu da Abokin sa Musa a kan Zaɓe

Hira tsakanin Aliyu da Abokin sa Musa a kan Zaɓe

Hello, Ladies and Gentlemen, good morning to you all.
Maza da mata, barkan ku da kwana.

In today’s lesson, there is a conversation between two friends, Aliyu and Musa.
A darasin yau akwai hira ne a tsakanin abokai biyu, Aliyu da kuma Musa.

Without any delay, let us listen to them attentively.
Ba tare da ɓata lokaci ba, bari mu saurare su dakyau.

Aliyu

You are welcome my friend. Good morning.
Abokina barka da zuwa. Barka da kwana.

Musa

Yeah, good morning. How are you?
Yauwa, barka da kwana. Yaya kake?

Aliyu

I am fine. What about you?

Musa

I am fine too, thank you.
Nima ina lafiya, nagode.

Aliyu

My friend long time, where were you?
Abokina kwana biyu, ina ka shige ne?

Musa

I am there at one side. I didn’t go any where.
Ina nan agefe ɗaya. Banje ko ina ba.

Aliyu

You are there, but not at your house.

Musa

Why do you say that? Do I have some where to go apart from my house?
Meyasa kace haka? Inada wani wurin da zan tafi ne baya ga gida na?

Aliyu

You were not being seeing for long time, that is why.
Ba a ganin ka ne kwana biyu, shine yasa.

Musa

If there is nothing to do, there is no need to be loitering about on the street.
Idan babu wani abinyi, ai babu bukatar ayita gararanba akan titi.

Aliyu

Really, that is good. But how preparation of election?
Haƙiƙa, to yayi kyau. Amma yaya shirye-shiryen zaɓe.

Musa

It is in progress, and the time is approaching.
Ana nan anayi, ga lokaci yana ta matsowa.

Aliyu

My friend who is your candidate?
Abokina wanene ɗan takarar ka?

Musa

Which candidate are you talking about? Is for the presidential, senatorial or representative?
Wane ɗan takarar kake magana? Na shugaban ƙasa, ko sanata ko kuma majilissar wakilai?

Aliyu

No, I am talking about presidential candidate.
A’a ina magana ne aka ɗan takarar shugaban ƙasa.

Musa

I don’t reach the decision yet. But I am praying to God to grant us the best among them who will be justifying. But not the one that we are going to regret at the end.
Ban yanke shawara ba tukuna. Amma ina nan ina addu’ar Allah Ya bamu wanda zayyi adalci. Amma ba wanda zamuyi nadama aƙarshe ba.

Aliyu

That is a good idea. I myself too, I don’t propose any one yet. Just I am praying may God decide the best one among them even from which party he is.
Wannan dubarace mai kyau. Ni kaina na ban yanke shawara akan kowannen su ba. Kawai dai ina addu’ar Allah zaɓar mana mafi alheri daga cikin su koda kuwa daga kowace jam’iyar ne yake.

Musa

May God bless our country. And may the elections be started peacefully and completed peacefully.
Allah dai Yasa afara zaɓuɓukan lafiya akuma ƙare lafiya.

Aliyu

Ameen, may God accept our supplications.
Amin, Allah dai Ya amshi addu’o’in mu.

Musa

Honestly speaking I am pity for Nigerians, because they are always willing to insist and stand with some politicians, but the politicians are always willing to cheat, deceive and disappoint them at the end.
Maganar gaskiya ina tausayawa ƴan Nigeria. Saboda burin su kullum su nace su goyawa wasu ƴan siyasa baya, su kuma ƴan siyasar kullum burin su shine su cucesu, su yaudare su kuma basu kunya aƙarshe.

Aliyu

That is before, we now get the solution. The solution is prayer.
Wannan ada ne, yanzu mun samu mafita. Mafitar kuwa shine addu’a.

Okay, this is what I have for you today, let us be together in the next coming lesson.
To abinda nazo muku dashi kenan ayau, mu kasance tare adarasi mai zuwa.

Thank you == nagode.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Back to top button