Learn

Me ake nufi da irregular verbs a cikin karatun turanci?

Menene Irregular verbs?

Mai karatu barka da zuwa, barka da sake ganinka a shafin nan. Shafin nan namu shafine dake kawo muku bayanai da darussan koyan turanci da kuma ƙa’idojinsa a sauƙaƙe.
A darasin nan za mu yi bayani game da IRREGULAR VERB.

Table of Contents

Kaman yadda ake iya gani a sama, mun kasa bayanin gida-gida zuwa gida biyar – ta yadda mai karatu zai fahimci darasin cikin sauki. Domin haka sai a yi ƙasa a ci gaba da karatu.

1. Menene verb?

Verb shine aikatau.
Aikatau shine duk wani aiki na motsa jiki ko wata gaɓa.
Ayyukan motsa jiki su ne kaman: yin tafiya (to walk), koyo (to learn), karatu (to read), kuka (to cry), girki (to cook), yekuwa (to scream), tafawa (to clap), zaunawa (to sit) da sauransu.

Misali na farko:

(a) I walk to school everyday.
Na kan je makaranta da kafa kullum.

(b) He walked to school yesterday.
Jiya, ya je makaranta da kafa.

Misali na biyu:

(a) She reads novels at nights.
Ta kan karanta littattafai duk dare.

(b) Fati read two novels last week.
Fati ta karanta littattafai biyu satin da ya wuce.

Misali na uku:

(a) We learn English at schools.
Mu na koyon turanci a makarantu.

(b) They studied English at college in 2008.
Sun karanci turanci a kwaleji a shekarar 2008.

Misali na huɗu:

(a) You sit on a red chair.
Ka na zaune saman jar kujera.

(b) Kabiru sat on a green chair.
Kabiru ya zauna saman koriyar kujera.

Misali na biyar:

(a) Aliyu claps to his friends.
Aliyu ya na tafawa abokan sa.

(b) He clapped to her when she arrived.
Ya tafa mata lokacin da ta iso.

A misalan da ake iya gani a sama, waɗanda ke layin (a) su ne a lokacin da ke ci. Waɗanda ke cikin (b) kuma misalai na lokacin da ya shuɗe.

2. Menene regular verbs?

Regular verbs ayyuka ne na yau da kullum. Wato ayyukan da wajen rubuta su a lokacin da ya shuɗe ƙarshen su bai canzawa. Domin su na ƙarewa da ‘ed’ ko ‘ied’. Misali,
daga ‘kill’ zuwa ‘killed’ ko daga ‘jump’ zuwa ‘jumped’ ko kuma daga ‘fry’ zuwa ‘fried’.

ALSO READ: Menene antonyms a cikin karatun turanci? (Antonyms words)

3. MISALIN REGULAR VERBS

Kafin mu yi misali, bari mu ga yadda ake rubuta regular verb.
Idan kalmar aiki ta ƙare da harafin ‘y’ sai a cire shi a sa ‘ied’. Misali, kalmar ‘try’ ta ƙare da ‘y’ sai a cire sa, kalmar za ta zama ‘tr’ sannan a sa ‘ied’ a wajen ‘y’ ɗin, kalmar za ta koma ‘tried’.

Misali:

Wet shirts dry in the sun.
Jiƙaƙƙun riguna kan bushe a cikin rana.

My shirts dried in the sun.
Riguna na sun bushe a rana.

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci


Idan kuma kalmar aiki ta ƙare da harafin ‘e’ kawai sai a kara ‘d’ a ƙarshen ta. Misali, daga ‘create’ zuwa ‘created’ ko daga ‘smile’ zuwa ‘smiled’.

Misali:

These balls bounce off the wall.
These balls bounced off the wall.

Idan kuma kalmar aiki ta ƙare da daya daga cikin harufan baƙi, kawai ‘ed’ ake ƙarawa a ƙarshen ta. Misali, daga ‘slap’ zuwa ‘slapped’ ko daga ‘kick’ zuwa ‘kicked’.

Misali:

I play football everyday.
Na kan yi kwallon kafa kullum.

I played football last year.
Na yi kwallon kafa shekarar da ta ƙare.

ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU

4. MENE NE IRREGULAR VERBS?

Su kuma irregular verbs, suma ayyuka ne na yau da kullum. Sai dai su wajen rubuta su a shuɗaɗɗan lokaci ba su da wata tsayayyar ƙa’ida.
Regular verbs tsayayyar ƙa’idar rubuta ta su ita ce su na ƙarewa da ‘ed’ ko ‘ied’. Su kuma irregular verbs ba haka suke ba.
Misali, daga ‘see’ zuwa ‘saw’ ko daga ‘think’ zuwa ‘thought’.

ALSO READ: Me ake nufi da Dis prefix a cikin darasin turanci?

5. MISALIN IRREGULAR VERBS

Kaman yadda bayani ya gabata, irregular verbs ba su da wata ƙa’ida da ake bi wajen rubuta su. Domin haka akwai waɗanda gaba daya basa canzawa wajen rubuta su a shuɗaɗɗan lokaci da lokaci mai ci.

Misali:

1. I cut fire wood rarely.
Ban cika faskara ice ba.

I cut some fire woods yesterday.
Na faskara wasu itatuwa jiya.

2. They let him go out at nights.
Su kan barshi ya futa da dare.

We let him go out last night.
Mun barshi ya futa daren jiya.

Idan aka lura a misalan nan kalmomin ‘cut’ da ‘let’ ba su canza ba. Yadda suke a shuɗaɗɗan lokaci haka suke a lokaci mai ci.

Sauran misalan su ne:

1. You speak to me often.
Ka na yawan yi mun magana.

You had spoken before she arrived.
Ka yi mun magana kafin ta iso.

2. She teaches biology at University.
Ta na karantar da biology a jami’a.

She taught biology in 1999.
Ta karantar da biology a shekarar 1999.

 

Menene irregular verbs a turanci?
Menene irregular verb?

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

5 Comments

  1. Gsky inajin dadi sbd haduwana da wanga shafin na karu sosai wlh allah karama lapiya da dawkaka malam muna karuwa sosai akan harkar turanci malam inaroko da arika kawo mana audio na koyon turanci murika ji muna sauraro daga dalibin ka yakubu ibrahim woje jos plateau state kahuta lpy malam ngd b

Leave a Reply

Back to top button