Bambanci tsakanin It’s da kuma Its a cikin karatun turanci
Menene Bambanci tsakanin ( ITS da IT’S)?
ITS dai yana ɗaya daga cikin “ Possessive pronouns” wanda suke nuna mallakar wani abu. Duk tafiyar su ɗaya da waɗannan kalmomin (Her, His)
Misalin ITS
Its size {Girman shi}
Its paint {Fentin shi}
Its taste {ɗanɗanon shi}
Its shape {Surar shi}
ETC
ALSO READ: Bambanci tsakanin Sometime, Some time, da kuma Sometimes a turanci
Idan kuka lura zaku ga an ce “Girman shi” kunga ana batu ne akan girman wani abu, to kenan abun shine ya mallaki girman . Allah ya sa kun gane!
Misali ;
Her baby bite with its teeth.
Yarinyar ta tana cizo da haƙwaran ta.
(IT’S teeth) na nifin haƙwaran ta. Wato haƙwaran yarinyar, kun ga anan ana nifin yarinyar ce ta mallaki haƙwaran tinda dai a bakin ta suke.
ALSO READ: Learn English, Yadda ake amfani da “Could” a turanci
Note ; Ana amfani ne da kalmar ‘IT’ idan ba a san jinsin abu ba. Kada kuga na ce yarinya, ze iya zama yaro ma. Irin idan ku ba ku san jaririn mace ne kokuma na muji ba ne, se kuyi amfani da ‘IT’ mai makon ‘He’ ko ‘she’
Sai kuma it’s
(It’s) kuma wani nau’in rubutu ne, kokuma nace salon rubutu wanda aka fi sani da “Contractions”. yanayi ne wanda ake taƙaita rubutu yadawo kaɗan ta hanyar jona kalmomi biyu. Sannan kuma “contractions ” suna da yawa, dan sunfi guda ashirin. Amma mu kawai zamuyi dubane zuwa ga wanda muke tattaunawa akai.
ALSO READ: Menene Ma’anar Punctuation Mark a cikin karatun turanci?
IT’S; yana ɗaukar abubuwa guda biyune.
1. It’s = It is
2. It’s = It has
Misalansu a Jimlance!
1. It’s not my fault ✔
2. It is not my fault ✔
Ba lafi na ba ne
IT’S; kamar yadda na faɗa a baya, ya kan ɗauki ma a’nar ‘IT HAS’. Gane hakan ya danganta da yanayin jimlar da akayi amfani da shi a ciki.
Misali nabbiyu game da (It has)
1. It’s nothing to do with my sister.
Wato abunda yake ƙunshe acikin wannan shine “ It has nothing to do with my sister”
Wanda yake nifin
Babu ruwan ƴar’uwata.
ƴar’uwata bata da hannu a ciki.
2. It’s been ages since we last visited them.
Yayi shekaru tinda muka kai musu ziyara.
Shima dai wannan ɗin bata sauya zani ba, kamar yadda ku ka gani a baya yana nifin (it has)
ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci
Note; wani ze ga kamar idan aka rubuta (It’s) kawai ba ze’iya gane wanne ake nifi ba acikin guda biyun ba (It is ko It has) da ma wasu masu irin wannan siffa biyun.
To wannan abune me-matiƙar sauƙi, kawai yanayin sauran kalmomin da suka biyo zaku yi sabida suna da bambancin da zaku’iya ganewa. Amma balallaine a fahimta yanzu ba sedai’idan munyi (Verbs da tenses) wata kila.
Idan akwai me tambaya game da abunda mukayi zan kasance a wadace domin na amsa ta‼️