Yanda zaka iya turanci

Dabaru 13 da Yakamata Kayi Amfani dasu Domin Inganta Turancin ka

Ganin Yadda Dalibai da Sauran Al’umma Sukan Gaza Yin Magana da Wannan Yare na English, Yasa a Yau Shafinku Mai Farin Jini na Karatunturanci Zai koyar daku Wasu Dabaru guda 13 da zasu taimaka muku Matuka Wajen Ganin kun iya zazzaga Turanci, kamar Turawa masu Jan Kunne,

 

 

 

Ga Dabarun Kamar Haka :

 

 

1•  Domin Yin Magana da Ingantaccen Turanci, a matsayinka na mai koyo yanada Kyau kadinga Amfani da Kalmomi masu Sauki fagen yin Maganarka, Kada Kace lallai sai kayi Amfani da Manyan Kalmomi, Kabi a hankali lokacin yin Magana da Manyan Kalmomin Yana tafe a nan gaba Kadan.

 

 

2• Ka tabbatar Kasan Ma’anar Dukkannin Kalmar da Zakayi Amfani da ita, kuma Yanada Kyau ka koyi Yanda ake furtata daidai.

 

 

3• Idan zakayi magana kadinga caccanza kalmomin, kada kadinga Amfani da kalma Daya a Kowanne lokaci, Misali idan Yau kayi Amfani da Kalmar Yes gobe sai kayi Amfani da Of course tunda dukkanninsu ma’anar su Daya.

 

 

4•  Kada Kadinga Jin Tsoron Furta wata Kalma,  Saboda Jin Tsoron furtata Zai hana ka furtata daidai, kadinga yin maganarka cikin kwarin gwuiwa.

 

 

5• Idan kana Magana kada kadinga Dauka cewar ba Daidai kakeba , A’a koda ana yimaka dariya ka cigaba da Maganarka, Wataran Zaka bawa wadanda Suke Maka Dariyar Mamaki.

 

 

6•Kadinga yin Amfani da Gajerun Jimloli Kuma masu kayatarwa, Saboda hakan Zai janyo hankalin masu sauraren Maganarka Sosai.

 

 

7• Kada Kaji Tsoron Magana a gaban Wanda Yafika Iya Turanci ko kuma Wani Wanda Yake Sama dakai, Kaidai kadinga Kokarin yin Amfani da kalmomin da Kake Ganin Sun dace da kafurta musu, kuma Amfanin yin magana a gaban nagaba dakai Shine : Zaka dinga Samun Gyara daga gareshi da Zarar kafurta kalma ko Jimla ba daidaiba, Wanda hakan Zai taimaka maka Matuka Wajen Inganta turancin ka.

 

 

8• Kada Kadinga Fushi ko Bata Rai a Lokacin da Kake magana, Saboda Murmushi da sakin fuska suna Bada taimako Matuka Wajen Furta kalamanka daidai, batareda Yawan Samun kuskureba.

 

 

9•Kadinga natsuwa sosai a duk Lokacin da Zakayi magana da Turanci, kuma Idan so samune yanada Kyau ka kasance tsaf-tsaf, Saboda Tsafta tana Kawo natsuwa Kwarai da Gaske.

 

 

10•  Idan Yakasance zakayi Magana da Turancine a Gurin da Mutane suka taru da Yawa ko Gurin Taro, Kadinga Lura Matuka da Kalmomin da Zaka Furta dakuma maganganun da zaka fada, kuma yanada Kyau kasamu masaniya Akan Irin Tambayoyin da Zasu biyo Baya, Bayan kammala jawabinka.

 

 

11• Kada ka tsawaita Maganarka a Lokacin da kakewa Al’umma Jawabi,  kadinga lura da lokaci, kuma ka dakata da Jawabanka da Zarar Kaga mutane sun fara Gajiya da Surutunka, Kada Kabari har sai sun tsayar dakai da Kansu.

 

 

12•  Katashi tsaye kuma ka natsu a Lokacin da Zakayi wa Al’ummar da suka halarci  Wani taro Jawabi, kuma Kada kayi Kokarin Sukar Wani Saboda kalmomin cin mutunci basuda Dadi koda kuwa da Yaren Turanci aka furtasu.

 

 

13• Ka lura da Yanda Kalmomin turanci suke caccanzawa daga Present tense zuwa Past tense dakuma Future tense.

 

To Anan Zamu Dakata a Wannan Rubutu Namu na yau,

 

 

Dafatan dai Rubutun ya Kayatar daku, Kusanar damu ta Akwatin Comment dake Kasa, Kuma Kusanar da Abokananku Domin Suma Suzo su Karanta su Amfana.

 

 

 

Mungode da Ziyartar Karatun turanci.

 

 

 

 

Naku a Kullum : Miftahu Ahmad Panda.

 

 

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button