KalmomiKaratun Turanci

Wasu daga cikin kalmomin Hausa masu ma’anoni guda uku

Wasu daga cikin kalmomin hausa masu ma’anoni guda uku

A darasin yau zan fara kawo kalmomin Hausa ne masu ma’anoni kamar uku ko fiye da ukun a turance. Da kuma yadda ake samun banbanci wajen amfani dasu a cikin jimlolin Turanci.
Ga kalmomin-

1. Farawa
begin
start
commence

Cigaba
continuation
develop
progress

Riba ko karuwa
propite
earn
gain

Kiyawa
refuse
reject
denny

So
like
love
want

Amsa
receive
collect
accept

Yanzu zan kawo misalai cikin jimloli.

Begin
Start
Commence

Wadannan kalmomin duk suna nufin farawa. Kuma kusan kowacce tana iya hawa gurbin wata.

Misali-
The projects will begin next week
Ayyukan zasu fara ne satin gaba.

The projects will start next week
Ayyukan zasu fara ne satin gaba.

The projects will commence next week.
Ayyukan zasu fara ne satin gaba.

Continuation
Develop
Progress

Wadannan kalmomin suna nufin cigaba. To amma wajen amfani dasu a cikin jimla yana iya banbanta.

Misali-

Progress da kuma develop suna iya tafiya tare. Wata tana iya hawa gurbin wata. Saboda su biyun suna nufin cigaba da ake samu a harkokin yau da kullum.
Amma continuation yana nufin cigaba ne irin na aiki.

Misali-

A country can not develop when there is injustice.
Kasa bazata cigaba ba idan akwai rashin adalci.

How would you expect a progress, while you are not truthful?
Taya zaka sa ran cigaba ayayin da kai ba amintacce ba ne?

Since the work was abandoned, there is no effort for continuation.
Tunda akayi watsi da aikin, babu wani kuduri na cigaba.

Profit
Earn
Gain

Duk suna nufin karuwa ko riba.
Kuma kusan ana iya amfani dasu a jilma daya.

Misali-
Don’t wast your time on what there is no profits.
Kada ka bata lokacin ka akan abinda bashida riba.

Being I with him, I earned a lot.
Kasancewa ta tare dashi, na karu sosai.

She is working as a slave, but she doesn’t gain anything.
Aiki takeyi kamar baiwa, amma bata karu da kome ba.

Refuse
Reject
Denny

Wannan duk suna nufin ki ko kiyawa.
To amma “denny” tafi tsauri akan sauran. Saboda ita byan kiyawar kuma tana nufin karyatawa. Don kana iya fadawa mutum magana bazai yadda ba amma bazai karyata ka ba.

Misali.

For how many times that I used to advise you, but you reject?
Sau nawa nake shawartar ka sai kaki?

I asked him to escort his sister, but he refused.
Na nami ya raka ‘yar uwar sa sai ya kiya.

Even if you denied my suggestion, you are not supposed to denny what I have said.
Koda kaki shawara ta, to bai kamata ka karyata abida na fada ba.

Like
Love
Want

Wadannan duka suna nufin so. To amma kowacce akwai irin son da yafi dacewa da ita.

Misali-
Anfi amfani da “like” ne awajen so da akeda manufa akansa. Kamar kaso abu don kyau ko inganci ko wani dalili na daban.
Amma “love” tafi karfi sosai. Saboda ana iya amfani da ita a so mai sharadi watau “conditional love”. Kuma ana iya amfani da ita a son da ba ayi masa sharadi, shine son da akeyi don Allah, watau “unconditional love”

Ita kuma “want” ana amfani da ita ne a so irin na bukata, kamar ina so kazo, ina son naje dadai sauran su.

Ga misali-
I like him for his wiseness
Ina son sa ne saboda wayon sa.

I like it for it’s quality.
Ina son abin saboda ingancin sa.

Just I love you for God’s sake.
Kawai Ina son ka, ko ina son ki, ko ina son ku ne saboda Allah.

She said she loves you for your patience and kindness.
Tace tana son ka ne saboda hakurinka da kuma kirkin ka.

I want to advise you.
Ina son na shawarce ka

I want you to come to my office.
Ina son kazo ofis nawa.

Receive
Collect
Accept

Wadannan duka suna nufin amsa.

Amma “collect” da kuma “accept” suna iya zuwa da wata ma’anar a cikin wata jimlar. Saboda “collect” bayan amsa kuma tana nufin tattarawa.
Hakama “accept” bayan amsa tana nufin yarda.

Misalai
I received my salary since last week.
Na amshi albashi na tun satin da ya wuce.

Please when ever you get a chance, let you come and collect your money.
Don Allah duk lokacin da ka samu dama kazo ka amshi kudin ka.

We want to collect more information.
Muna son tattara bayanai.

Please tell him to come and accept what I promised him.
Don Allah ka fada masa yazo ya amshi abinda nayi masa alkawari.

Just you have to accept and proceed, that is all.
Kawai ka yarda awuce wurin, shine kawai.

This is what I have for you today.
Be with me for another new lesson next time.
Thank you.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button