Kalmomi

Sabbin kalmomi da ma’anarsu da kuma yadda ake amfani dasu

Sabbin kalmomi da ma’anarsu da kuma yadda ake amfani dasu

Kar ku manta kofa a buɗe take ga wanda bai fahimci wani abu a cikin wannan shafin ba

A wannan darasin zamu kawo kalmomin turanci ne tare da fassara su, da kuma yadda zaka sanyasu a cikin jimla(sentence)

ALSO READ: Kalmomin turanci da fassarar Hausa


Sanin kalmomi dayawa na yaren da akeson koyo shine mataki na farko wajen ji da kuma fahintar yaren. Saboda idan kasan kalmomi dayawa akowane yare, to zakaji abinda ake fada koda bazaka iya mayarwa ba.
Mataki na biyu, idan kasan kalmomin, sa annan sai ka koyi yadda akesa su a cikin magana.
Mataki na ukku shine bayan kaji yaren kuma kana fahintar sa, sai kuma kasan yadda zaka iya gane manya da kuma kananan kurakurai.

Ga kalmomin

CONTENTIOUS – RIGIMA

The rights sharing division agreement, was the most contentious issue for decades.
Yarnejeniyar rabon hakkin madafu, shine babban lamarin da yajawo rigima tun gommen shekaru (DECADE – Shekara 10)

Example: one decade – shekara goma.

Twodecades – shekaru ashirin.

DECADES SHEKARU goma-goma sau dayawa)

ALSO READ: Yadda ake furta kalmomin turanci a cikin sauki


SEDITIONBATANCI

He was arrested in accusation of sedition.
An kama shi ne akan zargin kalaman batanci.

INCITING – TUNZURA

His speech incited his supporters to violated the Law.
Maganar sa ce ta tunzura magoya bayansa suka karya doka.

STRESS  – DAMUWA

The sympathy and the stress for death of his brother made him to became thin.
Juyayi da kuma damuwar rasuwar dan uwansa ne yasa yasa ya rame.

CONTROVERSIAL – RIKITARWA

This is a controversial issue, so that it couldn’t be judged easily.
Lamari ne mai rikitarwa, don haka baza a iya yanke hukunci cikin sauki ba.

ARGUMENT – MAHAWARA

Really he has presented an argumentative motion.
Lallai ya gabatar da kudurin da za ayi mahawara

SPECULATION – JITA-JITA

There has been widespread speculation about his resignation plan.
Akwai yaduwar jita-jita agameda shirin retayar sa.

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci


POSSESSION – MALLAKA

The Students are all in possession of an English books.
Dukkan Daliban sun mallaki littattafan turanci.

ACHIEVEMENT – MORIYA

We didn’t attained any achievement under the leadership of our Chairman as we expected.

Babuwata moriya da muka ci akarkashin shugaban mu kamar yadda muka zata.

SUITABLE – ZABABBE

Thank you for visiting us at this suitable time.
Godiya abisa ziyarar mu a wannan zababben lokaci.

COLLABORATE – HADIN GWIWA

Police collaborate with other security personnel to end the insecurity.
‘Yan sanda sun hada gwiwa da wasu jami’an tsaron don kawo karshen rashin tsaro.

PROTECT – KARIYA/KARE

As desert is approaching,
to protect our farm-lands we must plant more trees.
Yadda hamada ke matsowa, don mu kare gonakan mu, dole mu shuka itatuwa dayawa.

ENSURE – TABBATAR

You have to ensure that I am around before you come.
Sai ka tabbatar ina nan kafin kazo.

PREVENT – HANAWA

Many were prevented entering the room.
Dayawa aka hana shiga takin.

ALSO READ: Bambancin kalmomin dake karewa da -NCE da kuma -NT


SUSPEND – DAKATAR

He was suspended for sabotaging the Team.
An dakatar dashi saboda yiwa kungiya zagon kasa.

POSTPONE – DAGA
The meeting was postponed to give the attendances more time.
An daga taron ne don ba mahalartan isasshen lokaci.

PRECAUTION – RIGAKAFI
The drastic measures were taken for precaution for the spread of the virus.
An dauki kwakkwaran mataki don rigakafin yaduwar kwayoyin cutar.

SATISFY – GAMSUWA
I am fully satisfy with your character.
Na gamsu sosai da halayar ka.

MEDIATE – SHIGA TSAKANI
You are responsible to mediate a deal on an escalating dispute between the two countries.
Kai kakeda hakin shiga tsakani a rikicin dake habaka a tsakanin kasashen biyu.

GREET – GAISHE DA
Let you go and greet your Sister.
Je ka gaishe da ‘yar uwar ka.

GREAT – BABBA
This is a very great problem.
Wannan babbar matsala ce.

PULL – JA
Pull the rope well
Ja igiyar sosai.

FULL – CIKA
The calabash is full of water
Kwaryar ta cika da ruwa.

ADVISE – SHAWARTA
I want to advise you.
Ina son na shawar ce ka

ADVICE – SHAWARA
I need your advice.
Ina neman shawarar ka.

LET – BARI
Let us go and see him
Bari muje mu ganshi.

LATE – MAKARA
Why are you always coming late?
Meyasa kullum kake zuwa a makare?

ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU


THINK – TUNANI/ZATON
I think you are not yet ready
Inajin baka shirya bane tukuna.

SINK – NUTSEWA
If you are not good for swimming, it is easy to sink.
Idan baka iya iyo ba, abune mai sauki ka nutse.

SORE – KURAJE
She is coughing, because her throat is sore.
Tana tari, saboda makogoronta yayi kuraje.

SAW. – AN GANI/ZARTO
I saw him hiding behind the wall.
Na ganshi yana boyewa bayan a katanga

SAW – ZARTO
He cuts the timber with saw.
Da zarto (minshar) yake yanka katako.

DEAF – KURMA
You keep silent like a deaf.
Kayi shiru kamar kurma.

DEEP – ZURFI/NISA
The well is very deep.
Rijiyar tanada zurfi sosai.

DEEP -NISA
He has gone deep, he can’t hear you.
Yayi nisa bazai ji ka ba.

LUCK – SA’A
Good luck to you.
Allah Ya bada sa’a

LACK – RASHIIN
He said he couldn’t buy a new phone, because of lack of money.
Yace bazai iya sayen sabuwar waya ba saboda rashin kudi.

WET  – DANYE/JIKAKKE
I can’t wear a wet trouser.
Bazan iya sa jikakken wando ba.

WAIT. – JIRA
I can wait for you,if you want to go with me.
Zan iya jiran ka, idan kana son tafiya dani.

Sabbin kalmomi da ma'anarsu da kuma yadda ake amfani dasu
Sabbin kalmomi da ma’anarsu da kuma yadda ake amfani dasu

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button