Banbanci tsakanin lorry da kuma truck a turanci
Banbanci tsakanin lorry da kuma truck a turanci
Maraba da sake shiguwa shafin Koyon Turanci A Saukake. A cikin wannan darasin zamuyi ne akan banbanci dake tsakanin kalmar “lorry” da kuma “truck” a cikin turanci
Wasu kan yi tambaya cewa su kan karanta a littattafai, jaridu, da mujallu; babbar mota akan kirata lorry, a wasu littattafan kuma akan rubuta truck. To wai ya ya abun yake ne?
Wannan ba wani abu ne mai wahalar ganowa ba. Domin a turanci akwai kalmomi da ake kira synonymous. Wato mabambanta kalmomi masu ma’ana iri ษaya. To waษannan kalmomin ma haka suke, sai dai inda abun yake shine:
LORRY ๐ฌ๐ง (BrE)
Lorry na nufin babbar mota kaman Daf, Iveco, Man diesel, Mark da makamantansu. Amma fa a turancin Birtaniya.
TRUCK ๐บ๐ธ (AmE)
Hakama, truck na nufin babbar mota kaman Daf, Iveco, Man diesel, Mark da makamantansu. Amma fa a turancin Amurka.
๐ฌ๐ง Lorry ๐ lorries๐๐๐
๐บ๐ธ Truck ๐ trucks ๐๐๐
MISALI:
๐ฌ๐ง We have delivered the goods by lorry.
๐บ๐ธ We delivered the goods by truck.
๐ณ๐ฌ Mun kai kayan da babbar mota.
๐ฌ๐ง In Nigeria mostly goods are transported between South to North in lorries.
๐บ๐ธ In Nigeria mostly goods are transported between South to North in trucks.
๐ณ๐ฌ A Nigeria mafi akasarin kayayyaki a kan ษakkosu daga kudu zuwa arewa a manyan motoci.
Ka da dai a manta ayi subscribe na channel ษin mu mai suna Nura Mahadi dake YouTube.