KalmomiKaratun Turanci

Yanda zaka yi amfani da kalmar “Would” a harshen turanci

Yanda zakayi amfani da kalmar Would a turanci

Anayin amfani da kalmar “would” a matsayin (past tense) din “will” alokacin da za’a fadi abun da wani mutum daban yafadamaka.
Misali; Musa said he would come tomorrow. ( musa yace zaizo gobe)
To kunga awannan jimlar, musa yariga yafaɗi zaizo, amma wanimutumne daban yake maimaita abunda musan yariga yafaɗa ma’ana wani mutum ne yake faɗama wani mutum daban abun da musa yariga ya faɗa.
Idan mutum yana maimaita abun da wani yace ana kiranshi (reported speech).

Misali; she told me she would contact you later. ( Tafaɗamun zata kira ki /ka anjima).
Karkumanta muna maganane akan “WOULD”. Hallaudai awannan jimlar (sentence) ana faɗin abunda wata tafaɗama watane kokuma wani .

  • Ana iya amfani da kalmar “WOULD” wajan yinnuni da sakamakon wani abu kokuma yin tinanin yadda abu zaikasance (tsammani).

Misali; He thought that the derive WOULD take two hours. (Yayi tsammanin cewa tafiyar/ tuƙin zai dauki awa biyu).
To awannan jimlar kalmar tayi nunu dacewa wani mutum ya (tsammanci) cewa tafiya zata ɗauki tsayin awa biyu.

Misalina biyu; Hurry up! It would be problem, if we get there late. (Hanzarta! Zaizama damuwa idan muka isa a makare).
wannan jimlar kuma tayi nuni dacewa sakamakon rashin hanzartawa za su iyayin latti/makara.

Misali na uku; He would look better with cover shoe.
kalmar “would” a wannan jimlar tana nuni dacewa da’ace yasaka takalmin da zai rufemai ƙafarsa (sauciki) to faa shigarsa zatafi bada ƙalau/ kyau. To kunga annan anyi tinanine akan abunda zaifiyi masa kyau.

Za’a iya amfani dakalmar “would “ wajan kwatanta yiwuwar aukuwar wani abu da’ace wani abu yafara faruwa da farko.

Misali; she would not have been tired, if she had gone to bed earlier.
(Bazata kasance agajiyeba da’ace ta kwanta da wurwuri/wuri).

To kunga annan yayi nuni dacewa da’ace ta kwanta da wuri to bazatatashi agajiyeba.

Anan an kwatanta cewa da’ace barci da wuri ya fara aukuwa tofa zaiyiwu tatashi ba’a gajiyeba.

Ana iya amfani da kalmar “would ” wajannuna fata kokuma son faruwar wani abu (sonsamu) .

Misali; I wish you would let me alone.

Awannan jimlar kuma kalmar tana nuni da cewa shi zaifijindadi abarshi shikadai kokuma ace da sonsamune abarshi/ta shi/itakadai.

Ana iya amfanida kalmar “would” wajannuna wani mutum bashi da niyar yin wani abu kokuma yaƙiyin wani abu.

Misali: he would not apologise, even though he knew he made a mistake.

Anan kuma “would not or wouldn’t” za’a iya cewa anyi amfani da ita a matsayin “refuse” (ƙinyin wani abu)

Misali; He refused to apologise, even though he knew he made a mistake.
(Yaƙibada haƙuri dukdacewa yasan yayi kuskure).

To anan kalmar “wouldn’t “tayi nuni dacewa yaƙi bada haƙuri.

Ana iya amfani da kalmar “would” wajan yin magana ko tambaya cikin girmamawa.

Misali; would you accompany me to market tomorrow please?
Za’a iya ɗaukar magananr a matsayin kamar wadda tayi maganar tace(dan allah zaki/ka ɗan rakani kasuwa gobe)?

A wannan jimlar (sentence) kalmar tanayin nuni da anyi tambayarne cikin girmamawa /tausasawa.

Misalina biyu; would you pay my school fees please?
(Kamar ace dan allah zakaɗan biyamun kuɗin makaranta) ?

Misali na uku; would you shut the door for me please?
(Dan allah ko zakaɗan rifemun ƙofa)?

za’a iya amfani da kalmar would wajan tambayar mutum abunda yakeso (ra ayinsa akan wani abu) kokuma abunda yake so abashi.

Misali ; my son, would you like to take tea this morning or something else?
(Yarona kanason shan shayi dasafennan kokuma wani abudaba kakeso)?

Za’a iya amfani da kalmar “would ” wajan yin kintace (tinanin yadda abuzaizama (kasance).

Misali if i should ask you, what would you say about his exams paper?

I would say he cannot afford the required mark.
(Idan zan tambayeki/ka mezaki/kace akan takardar jarabawarsa?

To ansar zata iya zama kamar ace:

(Zan iyacewa bazai iya kawo abunda ake buƙataba)
To anan kintace akayi wanda balallaibane yazama gaskiya.

ana iya anfani dakalmar “wouuld” wajan bada shawara.

Misali; I would not write the exams, if i were you.
(Da’ace not ceke bazan rubuta jarabawarba).

Wannan yanuna kamar itama ana shawartartane da karta rubuta.

ana iya amfani dakalmar “would ” wajannuna wani abu dayake faruwa akai akai wanda yashuɗe (wato abunda yake faru akai akai daa amma yanzu baya faruwa)

Misali ; Malam muhammad would always be the first teacher to come to school, when i was schooling.

(A wannaan jimlar kuma kalmar tanan nuna cewa lokacin tana karatu akwai wani malaminsu wanda kullum shine farkon xuwa makaranta).

Anan zan dakata.
Duk wanda yakeda tambaya zai iyayi.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button