nouns

Me ake nufi da Regular Plural Noun a cikin karatun turanci

Meaning of regular plural Noun in Hausa

Barka da sake kasancewa a cikin wannan shafin na Karatunturanci, awannan darasin zamu kawo Ma’anar Plural Nouns ne tare da yanda ake samar dashi, shafin karatunturanci shafine da kokarin kawo darussan turanci a cikin sauki.

ALSO READ: Menene antonyms a cikin karatun turanci? (Antonyms words)

Menene Noun?

Kafin mu shiga cikin darasin yakamata musan Menene Noun , Atakaice dai Noun shine sunan kowani abu, idan mukace kowani abu kenan ya hada da sunan mutum, sunan dabba, sunan gurare, har ma da sunayen abubuwa (things)

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci


ALSO READ: Me ake nufi da Dis prefix a cikin darasin turanci?

Menene singular Noun?

Singular Noun shine sunan da yake nuni ga mutum, guri, dabba, kowani abu guda daya tilo , Atakaice dai Singular Noun yana nufin abinda yake guda daya ne. Bari mu kawo misali:

There is one book on my table and one pen on my chair – Da akwai littafi guda daya akan teburin da kuma abin rubutu guda daya akan kujera ta.

Kaga a wannan jimlar kalmomin “book”, “Table”, “pen”, da kuma “Chair” duk singular Noun ne, saboda dukkannin su kalmomine da suke nuni ga abu kwara daya tilo

ALSO READ: Menene Ma’anar compound Noun da Hausa?


1. Singular Noun zai iya kasance wa sunan mutum, misali:

 • Abdullahi
 • Maryam
 • Father
 • Mother

2. Singular Noun zai iya kasance wa sunan guri, Misali:

 • City – birni
 • Town – gari
 • Country – kasa
 • Sea – teku

3. Singular Noun zai iya kasance wa sunan abubuwa, Misali:

 • Bicycle – Keke
 • Computer – na’ura mai kwakwalwa
 • Letter – wasika

Menene Plural Nouns?

Plural Noun shine sunan Mutane, gurare, dabbobi, ko kuma abubuwa wanda yake sama da guda daya

Atakaice dai plural Noun shine sunan da yake guda biyu ko sama da haka

Yawanci ana karawa kalmar Singular Noun wasu haruffa ne domin su zama plural Noun, Misali ana karawa Singular Noun harafin “S” don ya zama plural Noun. Misali:

 • Girl – yarinya     Girls  – ‘yan mata
 • Boy – yaro.         Boys – Yara (masa)
 • Rat – bera.         Rats – beraye
 • Town – birni      Towns – butane

ALSO READ: Yadda ake gane singular and plural na verb a turanci

Yanda ake samar da plural Noun

1. Wasu daga cikin plural Noun ana samar da sune ta hanyar karawa Singular Noun harafin “s”, kamar dai yanda nakawo Misali a sama,

Nouns
Singular Nouns Plural Nouns
 Car – mota  Cars – motoci
 Bag – jaka  Bag – jakuna
 Table – teburi  Tables – tebura
 House – gida  Houses – gida je
 Dog – kare  Dogs – karnuka

 

ALSO READ: Yadda ake furta kalmomin turanci a cikin sauki


2. idan karshen Singular Noun ya kasance yana fitar da sautin “Sh” a karshe (wato irin Kara da lasifika take yi), Atakaice dai irin wadannan sautin /s/, /z/, /ʃ/, /ʒ/, /tʃ/ or /dʒ/ , ana samar da plural dinsu ne ta hanyar karawa kalma “es”, Idan kuma kalmar ta kare da “e” ne sai a karawa kalmar “s” kawai. Misali

 

 • kiss – kisses – /ˈkɪsɨz/
 • dish – dishes – /ˈdɪʃɨz/
 • witch – witches – /ˈwɪtʃɨz/
 • judge – judges – /ˈdʒʌdʒɨz/

3. Idan kalmar Singular Noun ta kare da harafin “f” ko kuma “fe” , ana samar da plural din su ne ta hanyar canza harafin “f” ko kuma “fe” din, sai a sanya haruffan “ves” ko kuma “es” . Misali:

Singular Noun plural Noun Fassara
 Life  Lives  Rayuwa
 Wife  Wives  Mata
 Wolf  Wolves  Kerkeci
 Thief  Theives barayi
 Leaf  Leaves ganyayyaki
 Knife  Knives wukake
 Hoof  Hooves Kofa to
 Scarf  Scarves  Kallabi

Amma da akwai wasu kalmomin masu karewa da “Fe” ko kuma “f” wanda kawai harafin “s” ake kara masu, ba tare da an cire harafin “f” ko “Fe” ba. Misali:

Singular Noun Plural Nouns Fassara
 Roof  Roofs Rufin saman daki
 Chief  Chiefs  mutum mai
Babbar matsayi
 Belief  Beliefs Imani

ALSO READ: Menene Bambanci tsakanin Present participle da kuma Past participle a turanci?


4. Idan singular Noun ya kare da harafin “o” kuma harafin dake bayan “o” din harafine (consonant), kawai za’a kara haruffan “es” ne a karshen kalma, Misali:

Singular Noun Plural Nouns Fassara
 Potato  Potatoes Dankali
 Hero  Heroes Jarumi
 Mosquito  Mosquitoes   Sauro
 Tomato  Tomatoes Tumatur

Amma kuma da akwai kalmomin da suke karewa da “owanda kawai harafin “s” ake karawa. Misali:

Singular Noun Plural Noun Fassara
 Photo  Photos Hoto

5. Idan singular Noun ya kare da harafin “o” kuma harafin da yake bayan “o” din wasali be (vowel), to kawai zamu kara harafin “s” a karshen kalmar. Misali:

Singular Noun Plural Noun Fassara
 Radio  Radios  Rediyo
 Video  Videos  Bidiyo

ALSO READ: Kalmomin Turanci masu haruffa uku (Three letters words)


6. Idan singular Noun ya kare da harafin “y” , sannan kuma letter da yake bayan ” y” din harafi ne, kawai zaka canza harafin “y” dinne, sai mu sanya haruffan “ies” a karshe. Misali:

Singular Noun Plural Noun Fassara
 Party  Parties Bidiri/walima
 Lady  Ladies  mata
 City  Cities  Birane
 Country  Countries  kasashe
 Puppy  Puppies kananun karnuka
 Family  Families  Iyalai

Amma kuma idan harafin dake bayan “y” din wasali ne (vowel), kawai zaka kara harafin “s” ba tare da ka cire harafin “y” din ba. Misali:

Singular Noun Plural Noun Fassara
 Day  Days Ranaku
 Toy  Toys  Yatsu
 Boy  Boys Yara(maza)
 Key  Keys  Mukullai
 Donkey  Donkeys Jakai
 Holiday  Holidays Hutu

Wadannan kalmomin sune ake kira da regular plural Noun, zamu dakata anan, sai kuma a darasi na gaba zamuci gaba Insha Allahu

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Leave a Reply

Back to top button