Adverbs

Wasu daga cikin kalmomin bayanau (Adverbs) a Turanci da fassarar hausa

Barka da warhaka, a cikin wannan darasin zamu kawo wasu daga cikin kalmomin bayanau wato adverb tare da fassara a harshen Hausa

ADVERBS: these are words that are used to show how actions take place or took place, they tell us more about how SUBJECT does or did an action.

Wayannan nau’in kalmomi ne wayanda ake amfani da su wajan nuna yadda aiki yake faruwa kokuma yadda aiki ya faru, hakan yana mana bayani akan yadda mai yin aiki yake kokuma ya gabatar da aiki.

Yawancin ADVERB suna karewa ne da (-LY) amma kuma ana samun ADJECTIVE yan kadan wayanda suke karewa da (-LY).

Yawanci ana amfani da ADVERB ne a karshen jimla, amma kuma akwai wasu kalmomin ADVERB wayanda a tsakkiyar jimla ake saka su.

She often sees me.

We always understand him.

The boys frequently make a noise in the class.

Lura: Galibi Kalmomin Adverbs suna karewa ne da “LY” , amma kuma akwai wasu kalmomin da basu karewa da “LY” kuma adverb ne

Misali

Abdul works hard – Abdul yana aiki tukuru

kaga a wannan Jimlar “HARD” shine adverb, amma kuma idan kun Lura bai Kare da “LY” ba.

Yanzu zan kawo maka wayanda suka fi shahara domin a san yadda ake amfani da su. Gasu kamar haka:

Kalmomin Adverbs of Frequency

 Adverb of Frequency yana faɗa mana sau nawa aiki ya faru. Ga wasu daga cikin kalmomin Adverbs of Frequency.

 • Always – koda yaushe
 • Usually – Galibi
 • Normally – kamar yanda aka saba
 • Generally – gabaki daya
 • Sometimes – a wasu lokutan
 • Occasionally – a wasu lokutan
 • Rarely – mai faruwa jifa-jifa
 • Never – ba mai yiwuwa ba

Kalmomin Adverbs of Manner

Adverb of Manner bayanau ne mai nuna yadda aiki ya faru ko yakasance. Ga wasu daga cikin kalmomin Adverbs of Manner
 • Gently – a mutunce
 • Straight – kai tsaye
 • Angrily – a cikin fushi
 • Carefully – a tsanake
 • Hungrily – a yunwace
 • Well – da kyau
 • Fast – sauri
 •  Gladly – cikin murna
 • Daringly – cikin gangan i

Kalmomin Adverbs of Time

Adverb of Time shima bayanau ne da yake faɗa mana wani lokaci ne aiki yakan faru. Ga wasu daga cikin kalmomin Adverbs of Time.
 • Today – yau
 • Yesterday – jiya
 • Tonight – da dare
 • Then – sannan
 • Now – yanzu
 • Finally – a ƙarshe
 • Previously – a lokacin daya gabata
 • Recently – abinda bai jima da faruwa ba
 • Eventually – daga karshe
 • Early – na farko
 • Yet – tukunna
 • Still – har yanzu
 • Soon – bada jimawa ba
 • Since – tun
 • Later – daga bisani
 • Before – kafin
 • After – bayan

Kalmomin Adverbs of Place

Adverb of Place bayanau ne da yake bayyana mana a inda aiki ya faru. Ga wasu daga cikin kalmomin Adverbs of Place.
 • Above – fiye da
 • Behind – a baya/a gurin
 • Over – Fiye da
 • Back – komawa baya
 • Far – nesa
 • Up – sama
 • Down – ƙasa
 • On – a kai
 • Below – ƙasa da

Da akwai wasu kalmomi da suke a matsayin Adverbs of Place sune irinsu: Somewhere, Nowhere, Everywhere, Anywhere.

Kalmomin Adverbs of Degree

Adverb of Degree shima bayanau ne da yake gaya mana gwargwadon, nisan, darajar, girman, maƙurar da aiki ya kai. Ga wasu daga cikin kalmomin Adverbs of Degree.
 • Very – matuƙa/Sosai
 • Enough – isash she
 • Too – wanda ya wuce kima
 • Just – dai dai da
 • Quite – Sosai
 • Almost – kusan
 • Extremely – mai tsanani

Wasu daga cikin kalmomin Adverbs tare da fassara a cikin harshen Hausa

Abnormally – abinda ake tsammani
Diligently – cikin halin sanin ya kamata
Hopelessly – Mara tabbas
Accidentally – a cikin hatsari
Amazingly – abin ban mamaki
Deliberately
Highly – Matuka
Adversely – Mai kawo cikas
Mysteriously – Mai sarkakiya
Delightfully – Mai faranta rai
Honestly – cikin gaskiya
Nearly – Kusa-kusa/ Saura kiris
Ultimately – Hakika
Nervously – Cikin fargaba
Roughly – cikin Fushi
Never – Ba Mai yiwuwa ba
Rudely – cikin fitsara
Nicely – Da kyau
Safely – cikin tsira
Noisily – cikin hayaniya
Scarcely – abinda bazai Iya faruwa ba
Unfortunately – cikin rashin Sa’a
Seemingly – kamar
Sadly – Cikin Fushi
Delightedly – A cikin farin ciki
Officially – a hukumance
Daringly – cikin ganganci
Only – kadai/kawai
Angrily – a fusace
Seriously – a cikin mummunan yanayi / Dauka Abu da muhimmanci
Upward – Fuskantar samu
Actually – Hakikani
Selfishly – cikin san rai
Always – Koda yaushe
Enormously – Mai girma
Anxiously – cikin fargaba
Equally – Dai-dai wa dai-da
Interestingly – abin Sha’awa
Arrogantly – Mai girman kai
Especially – musamman
Bashfully – Ɗar-ɗari
Inwardly – wanda yake a ciki
Awkwardly – a cikin yanayin jin kunya
Irritably
Beautifully – a cikin kyakkyawar yanayi
Eventually – daga karshe
Stupidly – Sakare
Jealously – kishi
Shyly – cikin jin kunya
Bitterly – cikin jin haushi
Exactly – hakikani
Cleverly – Mai kwazo
Frightfully – mai matukar muni
Lively – Zaunanne
Closely – Rufaffe
Fully – Cikakke
Furiously – mai ban haushi
Longingly –
Generally – Gabaki daya
Loosely – sakwa-sakwa
Commonly – shahararre
Generously – mai karamci
Loudly – Da ƙara sosai
Continually – mai faruwa kowani lokaci
Gently – a mutunce
Coolly –
Gladly – Cikin farin ciki
Courageously – mai tattare da karfin hali
Openly – Buɗaɗɗe
Urgently – cikin gaggawa
Tightly – ɗaurarre
Reluctantly – a cikin rashin So
Too – Wanda ya wuce kima
Repeatedly – wanda akai ta mai-mai tawa
Tremendously – Mai girma
Youthfully – ƴan matanci/ Samartaka
Righteously – Na kwarai
Sharply – Cikin sauri
Usefully – Mai amfani
Uselessly – Mara amfani
Painfully – Mai raɗaɗi
Shrilly – Mai ƙara
Correctly – Dai-dai
Usually – galibi
Patiently – cikin hakuri
Silently – cikin shiru
Perfectly – Gabaki ɗaya
Vaguely – wanda ba’a tabbatar da ko menene ba
Slowly – a hankali
Vainly – mara amfani
Smoothly – mai santsi
Valiantly – cikin karfin hali
Politely – cikin ɗa’a
Softly – Mai laushi
Vastly – Sosai
Unhappily – Rashin farin ciki
Potentially – mai yiwuwa
Sometimes – a wasu lokutan
Viciously – shegantaka
Powerfully – mai karfin iko
Soon – Bada jimawa ba
Victoriously – Mai nasara
Promptly – nan take
Speedily – cikin sauri
Majestically – na zati
Cruelly – mai halin mugunta
Daily – na kullum
Happily – cikin farin ciki
Rarely – mai faruwa jifa-jifa
Terribly – matuka
Readily – wanda ya shirya
Thankfully – abin godiya
Wrongly – abin kuskure
Really – Hakika
Thoroughly – gabaki daya
Yearly – Shekara-Shekara
Mockingly – cikin tsokana
Heavily – Da yawa
Regularly – mai faruwa kullum
More – Mai yawa
Deeply – Matuka
Helpfully – mai taimako
Hard – mai wahala
Bleakly – gurin da ba komai
Excitedly – abin farin ciki
Blindly – cikin makanta
Desperately -cikin son abu ido rufe
Extremely – mai tsauri
Blissfully – cikin matsanancin farin ciki
Boldly – karfin hali
Famously – a yanayin da akafi sani
Immediately – nan take
Suspiciously – cikin mamaki
Ferociously – mai firgitarwa
Sweetly – mai zaƙi
Tonight – Da daddare / cikin dare
Determinedly – ƙudurta
Swiftly – nan take
Quizzically – yi kamar zakayi tambaya, amma kuma sai ka fasayi
Harshly – cikin zalunci
Wisely – cikin wayo
Rapidly – cikin sauri
Wonderfully – cikin ban mamaki
Badly – cikin rashin kyau
Adventurously – cikin son yin ganganci
Easily – cikin sauki
Innocently – wanda baida laifi
Bravely – mai jarunta
Far – nesa
Briefly – cikin sauri
Fast – Sauri
Brightly- cikin haske
Increasingly – idan abu yana karuwa
Briskly – mai aiki da kuzari
Broadly – Mai faɗi
Fervently
Knavishly
Calmly – a tsanake
Fondly – cikin matsananciyar Soyayya
Fiercely – cikin ɗaure fuska
Helplessly – wanda bai samu mataimakansa ba
Carefully – a tsanake
Foolishly – cikin sakarci
Carelessly – nuna rashin kulawa
Fortunately – cikin sa’a
Frankly – a yanayin gaskiya
Less – karanci
Certainly – Ba tare da kokwanto ba
Stubbornly – tantiri
Lightly – mai haske
Cheerfully – tsallen murna
Freely – a kyauta
Absently – rashin kasancewa a wuri
Likely – abu mai yiwuwa
Afterwards – Daga baya kuma
Clearly – Sarai
Almost – kusan
Properly – dai-dai yanda ake tsammani
Vivaciously – mai rufin asiri (mace)
Eagerly – cikin kosawa
Punctually – mai faruwa akan lokaci
Sternly – Tsatstsaura
Accusingly – cikin yin zargi
Proudly – cikin alfahari
Strictly – akan yanayi mai tsauri
Warmly – mai ɗumi
Suddenly – Kwatsam
Supposedly – A bisa harsashe
Well – Da kyau
Instantly – a nan take
Tomorrow – Gobe
Abruptly – abinda ya faru kwatsam ba zato ba tsammani
Wadannan kadan kenan daga cikin kalmomin bayanau,

 

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Leave a Reply

Back to top button