Letter writing in Hausa

Yadda ake rubuta wasikar formal letter | Formal letter in Hausa

Koyon rubutun wasika

Yadda ake rubuta wasikar formal letter

Barka da shiguwa shafin Karatunturanci, a wannan darasin zamuyi shine akan yanda ake rubuta wasikar formal letter da turanci cikin sauki

Menene Formal letter da Hausa?

Formal Letter : Letter ne da muke rubutawa ga Shugaban kasa ko gwamna, ko minister, ko Ciyaman, ko kuma wasikun Kasuwanci, ko wasikar neman aiki ko neman wani Abu, da dai sauran makamantar haka.

Kamar yanda ake definition dinshi a turanci.

Formal Letter : is a letter written to a person who has no relationship by blood or friendship with the writer, Usually elderly person.

Formal Letter: wasika ne da ake rubutawa wani wanda bashi da Alaka ta jini ko abota da marubucin, yawanci ana rubuta wa manya ne.

KA’IDOJIN NA YANDA ZAKA RUBUTA WASIKAR FORMAL LETTER. 

kowace irin Wasika irinsu informal letter, Semi-formal Letter, Sunada ka’idojin yanda zaka rubuta wasikar su, to haka zalika ma Formal Letter yanada ka’idar yanda zaka rubuta wasikar ka,
ka’idojin kuwa Sune :

1. The address of writer (Addresser)
2. The Date. 
3. The Recipient address (Addresse) 
4. Salutation (Greeting) 
5. Tittle (Heading) 
6. Introduction 
7. Body Of The Letter. 
8. Conclusion 
9. Subscription 
10. Name & Signature 

Wadannan Sune ka’idoji na rubuta wasikar formal letter.
Ga bayaninsu daya-bayan-daya :

1. The address of writer : is the address of the person writing the letter, which must be written in a block form and be placed in upper write hand side of the letter.

Wato adireshin Mai Rubutu : shine adireshin marubuci (shi kanshi wanda yake rubuta letter din), Wanda dole ne a rubuta tashi a cikin jeri, kuma manya, ana rubuta tashi ne a saman shafi ta gefen dama.

2. The Date:- The date is written, as usual, on the next line below the address.

Wato Date shine ake kira “Kwanan wata” a Hausance
Kwanan wata ana rubutashine a layin kasa na adireshin ka.
A takaice dai adireshi ya kunshi sunan layi ko Lambar gida da kuma sunan unguwa, sunan gari, a takaice ma har da sunan kasa, idan wasikar za’a aika waje ne

Sannan kuma har wa yau rubuta adireshi ya rabu gida biyu

Wato akwai abinda ake kira “Block Style” Sannan kuma akwai “Slanting Block” 
Ga bayaninsu daya-bayan-daya

1. Block Style:- shi Block Style shine adireshin da zaka rubuta shi ba tare da karkata ba, Ga Misalin adireshin a kasa.

Box 59, Sabon Gari L.G.A
Kano State,
15 April 2020.
Wannan adireshin shine muke kiranshi da Block Style.

Slanting Block:- shikuma adireshin da muke kira Slanting Block ko Slanting Form shine adireshin da ake rubutashi a Karkace.
Ga misalinsa a kasa
Box 59, Sabon Gari L.G.A
Kano State,
15 April 2020.

Sannan kuma karka manta kowani layi akan sanya Comma (,) Sannan kuma a layi na karshe wato Date shine kawai zaka sanya Full Stop (.)
kamar dai yanda kuka ga na rubutashi to Hakane yakamata kayi naka adireshin.

3. The Recipient address:- This is an address of the person the letter is written to, it’s placed as next to the addresser in the left hand side of a sheet.

The Recipient address – wasu suna kiransa da ADDRESSE duk dayane :- shikuma Recipient address adireshine na wanda ake rubuta wa letter din, shikuma ana rubutashine bayan kammala addresser (adireshin Mai rubutu) ta gefen hagun shafin paper.
Ga Misali na wanda ake rubutawa wasikar.

The Commissioner Of Police,
Force Headquarters,
2,3,5 Joy way,
Lagos.

Shima wannan adireshin dolene a rika sanya Comma (,) a karshen kowani layi, Sannan kuma a layi na karshe saika sanya Full Stop (.), kamar dai yanda kuka ga na rubuta.

4. The Salutation:- After the receiver’s address comes Salutation, The Salutation for formal letter is usually “Dear sir” or “Dear Madam”

The Salutation:- yana nufin gaisuwace wanda take nuna girmamawa da kuma matsayin da mutumin yake dashi, ana rubuta Salutation ne bayan ka rubuta Addresse (wato adireshin wanda zai kar6a wasikar)  a kasanshi
yawanci akanyi amfani da wadannan Kalmomin wajen Salutation a FORMAL LETTER.

Dear Sir (idan ya kasance mutumin na miji ne)
Dear Madam (Idan ta kasance mace ce)

Sannan kuma anaso idan zaka rubuta Kalmar Dear Sir ko Dear Madam, yakasance harafin farko da Babban harafine, abinda nake nufi kada kazo rubutawa ka rubuta “dear sir” ko “dear madam” idan kayi haka to kayi kuskure (Wrong)  , Sannan kuma bugu da Kari zaka iya amfani da Mr ko Mrs,
Mr – idan yakasance namijine.
Mrs – idan yakasance mace ce.

Lura:- Bambancin su kawai shine Karin “S” da akayi,

Sannan kuma zaka iya fadan sunan mutumin da zaka aikawa wasikar idan kasan sunanshi
Misali.

Dear Mr. Tijjani,
Dear (Dr) Mrs. Nafisat,

Sannan kuma karka manta shima Salutation ana sanya mashi Comma (,) kamar yanda kuka ga nima na sanya mashi, wato Dear Sir, ko Dear Madam,  ko kuma Dear Mr. Tijjani, Ko Dear (Dr) Mrs. Nafisat, ina fatan duk an fahimci Wannan

5. Tittle (Heading) :- shikuma abinda ake nufi da Tittle ko Heading, shine zaka rubuta taken abinda zakayi rubutune akasanshi, Sannan kuma kar kamanta wasikar Formal Letter wasikace wanda zaka rubuta wa nagaba da kai, saboda haka ba’a bukatar ka tsawaita dogon bayani akan Tittle, kawai kadanyi rubutun wanda kasancewa shine wasikar dazaka rubuta akai.

Shi Tittle zaka iya rubuta shi da manyan Haruffa, sannan kuma zaka iya rubutashi da kananun Haruffa, anaso kaja masa layi idan kayi amfani da kananun haruffa, amma kuma idan da manyan haruffa kayi amfani zaka iya barin shi haka ba tare da kaja masa layi layi ba.
Ga Misali na yanda ake rubuta Tittle

THE SOCIAL EVILS PLAGUING MY COUNTRY 

DAMAGE OF CABLES. 

INDISCIPLINE IN SCHOOLS 

RE-TELEVISION SET PURCHASED 

Idan kuma da kananan haruffa zakayi sai kaja masa layi, MISALI.

Corporal punishment in schools. 

Complaints against the teaching staff. 

Application for the post sales manager. 


Ina fatan an fahimci Wannan.

6. introduction :- Shima dai Introduction ba’a so mutum ya dan tsawaita sosai, kawai anaso ne ka tafi Kai tsaye zuwa abinda zaka rubuta, kada ka tsaya tambayar ya iyalai ko lafiyarsa, kawai anasone ka tafi Kai tsaye zuwa abinda kake da bukatar rubutawa, Saboda karka manta idan akace wasikar Formal Letter wasikace wanda zaka rubuta wa nagaba da kai, wata kila ma wanda zaka rubuta wa wasikar akowani lokaci yana cikin aikine, kaga kuwa idan yaga introduction dinnaka zai 6ata mashi lokaci kawai zai zubar da Takardar nakane a kwandon Shara, kaga ta dalilin haka zaka iya rasa abinda kake nema, kaga anyi biyu babu kenan.
saboda haka idan zaka rubuta Introduction a formal letter ka Takaita rubutunka.

7. The Body Of The Letter:- This is a formal letter and we have to go straight to the point, There’s no room for personal Details and Sentiments which are commonly found in informal Letters.

Shima Body of the letter Ba’a bukatar ka tsaya wani dogon turanci, kawai shima anaso Kai tsaye ka fadi bukatar ka.
Shi Formal Letter ba kamar Informal Letter bane, saboda shi Informal Letter shine wasikar da zaka rubuta irin maganar da kaga dama, amma shi Formal Letter ba’a yin haka, Sannan kuma ba’a bukatar a a formal letter ka riqa hadawa da irinsu IDIOM (Salon magana) ko kuma PROVERB (Karin magana), a’a shi Formal Letter anasone ka tsaya ne kayi rubutu cikin girmamawa da kuma ladabi.

8. Conclusion:- Shi conclusion shine idan kazo rufe wasikarka, sai ka rubuta cewa ayi maka abinda kake nema a cikin kaskantar da kai

9. Subscription:- for most official or Formal letters, The subscript below acceptable,
Your Faithfully
Your Sincerely

Shi Subscription shine Kalmar da ake sanyawa bayan kammala rubutun wasikar ka, yawanci Kalmar da aka amince kayi amfani dasu a Formal Letter / Official Letter Sune
Your Faithfully
Your sincerely

10. Name & Signature:- shikuma wannan zaka rubuta sunan Kane da kuma sa hannu wato “Signature” ana rubutashine a kasan Subscription, kuma duk a bangaren dama, wani lokaci kuma zaka iya rubutawa ta bangaren hagu

Lura:- a duk lokacin da zaka rubuta sunanka anasone ka rubuta cikakken sunanka (Kada ka rubuta sunan ka kadai) anasone ka rubuta da sunan ka da kuma sunan maghaifinka, Sannan kuma sai kayi signature a kasanshi

How to write formal letter in Hausa?

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Leave a Reply

Back to top button