Koyon TensesTenses

Me ake nufi da Present Continuous Tense? | Koyon tenses

LEARN TENSES: PRESENT CONTINUOUS TENSE

Zamu iya amfani da “present continuous tense” don ya nuna abu yana kan faruwa (yanzu), sannan kuma bai gama faruwa ba. atakaice dai abinda yake faruwa yanzu kuma ba’a gama ba shine ake kira present continuous tense

ga Misali:

I am waiting – ina jira.

abinda wannan Jimlar take nufi shine har yanzu ina jira kuma bam bari ba

I am speaking – inayin magana

itama wannan Jimlar tana nufin har yanzu ina yin maganar kuma bam bari ba

They are dancing on the stage – Sunayin rawa akan dabin

Galibi kowanne “present continuous tense “ yana ginuwane ta hanyar amfani da wadannan Haruffan “is”, “am” da kuma “are”, Sannan kuma kowacce Kalmar aiki na present continuous tense yana karewa ne da “ing”. Misali kamar Kalmar “Writel a present continuous tense zamu kara ing ya zama “Writing”, kunga an kara “ing” kenan. ga dai formula na present continuous tense kamar haka :

He/She/It + is + gerund verbs.

You/We/They + are + gerund verbs

I + am + gerund verbs

Nasan mutane da yawa zasuce to Menene gerund verbs?

Gerund verbs wasu Kalmomin aiki ne wanda akowani lokaci suke karewa da ing, Danna link din dake kasa domin karanta Darasinmu akan “gerund verbs” dalla-dalla”

 PRESENT CONTINUOUS TENSE NEGATIVE.

Zaka saka SUBJECT sannan kasa AM/IS/ARE, daganan sai kasa (NOT) sai abu na ƙarshe shine ƙarawa verb ING:

I am not playing = Ba wasa nake yi ba.
We are not playing. = Ba wasa muke yi ba.
You are not playing. = Ba wasa ka/ki/ku ke yi ba.
They are not playing. = Ba wasa suke yi ba.
Ali and Ja’afar are not playing.
Ali da Ja’afar ba wasa suke yi ba.

He is not playing. = Ba wasa yake yi ba.
She is not playing. = Ba wasa take yi ba.
It is not playing. = Ba wasa ya/take yi ba (=abinda ba mutum ba)
Ali is not playing. = Ba wasa Ali take yi ba.

 

PRESENT CONTINUOUS TENSE POSITIVE QUESTION.

Zaka juya (am/is/are) ya koma farko sannan se ka saka Subject ya dawo na 2 sekuma verb mai ING, abu na ƙarshe shine alamar tambaya (?):

I am playing. = Am I playing?
We are playing. = Are we playing?
You are playing. = Are you playing?
They are playing. = Are they playing?
Ali and Ja’afar are playing.
Are Ali and Ja’afar playing?

He is playing. = Is he playing?
She is playing. = Is she playing?
It is playing. = Is it playing?
Ali is playing. = Is Ali playing?

 

 

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button