EnglishKaratun Turanci

Gabatarwa Game da Ma’anar English Language? (Darasin farko na koyon Turanci)

Wannan shine shimfida ko kuma darasi na farko a game da yaren Turanci (English language), a cikin wannan darasin zamuyi bayani akan ma’anar English da kuma samuwar yaren Turanci, sannan kuma insha Allahu a darussan da zasu zo a cikin wannan shafin zamu rika kawo hanyoyi da mutum ya kamata yabi domin kwarewa a iya magana da wannan yare na Turanci. Saboda haka abu na farko abinda ya kamata shine mu fara sanin ma’anar English Language,

Menene English Language?

A duk lokacin da mukaga wadannan kalmomi na English Language zamuga kalmomi ne guda biyu. Wato Akwai English, sannan kuma akwai Language.


yanzu bari mufara Dana farkon, wato English

ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU


What is an English – Menene Turanci.?

English is the second language than mother tongue. Nowadays is regarded as a general language all over the world. English is the form of speech or expression of our colonial master’s (British)

Turanci shine yare na biyu baya ga yaren uwa. A zamanin nan kuma an rikeshi a matsayin yare na duniya gaba daya. Turanci wata sifface ta magana ko baiyana ra’ayi na masu gidan mu wanda suka mulkemu (Turawa)

ALSO READ: HANYOYI (3) DA SUKE HANA MUTUM YA IYA TURANCI DA WURI


What is a Language – Menene Yare?

Language is the medium of communication through which we express our emotions, ideas and thoughts to our fellow people.

Yare shine hanya ko kafa ta sadarwa, wanda daga ita muke bayyana abinda yake zuciya ko wata fikira ko tunani ga sauran mutane.

Language is mainly composed of letters which stands for signs and sounds.

Yare ya kunshi bakake da wasula, wanda suke matsayin alamu da kuma sauti.

ALSO READ: Me ake nufi da Affixation a cikin darasin turanci?

The letters of a Language are treated as alphabet of that language (Bakake da wasula na kowane yare sune haruffa na wannan yare.)

English language has 26 letters. (Yaren turanci yanada haruffa guda 26.)

Alphabets in English are divided into vowels and consonants. (Turanci yanada haruffa da suka rabu zuwa biyu akwai wasula da bakake.)

Wasula sune: (a, i, o, u, e)
Bakake kuma sune: (b, c, d, f, g, h, j, k, l, m, n, p, q, r, s, t, v, w, x, y, z)

ALSO READ: Menene Ma’anar Nahawu (grammar) da turanci


Wannan shine farkon karatunmu a cikin wannan, Atakaice dai mun fara yin maku gabatarwa ne game da turanci kafin mufara yin darasi akan yanda za’a koyi turancin. Ina fatan dai kowa ya fahimci wannan darasin namu, idan ma baka fahimta ba, sai ka biyo mu ta group dinmu na facebook, kayi tambayarka aciki, mukuma da zaran mun gani zamuyi gaggawan baka amsa, ko kuma kayi mana comment Karku manta ku cigaba da kasancewa da wannan shafin domin cigaba da samun darussanmu akai akai
ko kuma Ku tuntubemu ta wannan email din:

Info@karatunturanci.com.ng

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button