Koyon TensesTenses

Menene Simple Past Tense?

LEARN TENSES: SIMPLE PAST TENSE

Abinda ake nufi da simple past tense

shine abin aka riga akayi kokuma aka gama babu sauran sa ayanzun.

Let us compare example with manman shata musician and composer.

Bari mu kwatanta misali da manman shata makadi kuma mawaki.

Manman shata was a Nigerian musician and composer. He lived from 1960 to 1995. He started composing at the age of 5 and wrote more than 300 pieces of music. He was only 35 years when he died.

Manman shata makadi ne kuma mawakin Nigeria. Ya rayu daga 1960 zuwa 1995. Yafara waka kimanin shekaru biyar sannan ya rubuta fiyeda wakoki guda dari uku 300. Kwata kwata shekaran sa talatin da biyar 35 alokacin da ya rasu.

Wato wannan misali ne kawai nayi don kugane amma bawai haka tarihin manman shata yake ba, mun dai bada labarin abunda yashude ne wato past simple tense.

wasu daga cikin Kalmomin simple past sune kamar haka :

Lived/started/wrote/was/died dukkan su past simple ne.

Sau dayawa past simple yana karewa da (ed) wato regular verbs/Aikatau mai bin tsari kenan.

For example/amisali

He invited them to our party but they dicided not to come.

Ya gayyace su zuwa wurin patin mu amma sun yanke shawarar bazasu zoba.

The police stopped me on my way home last night. Polisawa sun tsaidani akan hanyata ta tahowa gida jiya da dare.

She passed her examination because she studied very hard. Taci jarrabawar ta sabida ta jajirce wurin yin karatu.

Idan kun lura duka wadan nan labarine dangane da abunda yawuce.

Amma wasu dayawa daga cikin verbs din irregular ne wato wadanda basa bin tsari kuma past simple dinsu baya karewa da (ed) yanzu amisali

(Write – wrote) Shata wrote more than 300 pieces of music.

Shata ya rubata fiyeda wakoki guda 300 dari uku.

(See – saw) we saw Khamisu in town few days ago.

Munga Khamisu acikin gari kwanakin baya da suka wuce.

(Go – went) I went to school three times last week.

Naje makaranta sau uku satin da yawuce

(Shut – shut) it was cold, so I shut the window.

Akwai sanyi shi yassa narufe taaga.

Sannan acikin tambaya ko negative sentence zamuyi ampani da did/didn’t gamida infinitive ( enjoy/see/go etc)

Normal Questions Negatives I enjoy, you enjoy? I didn’t enjoy Na more shin ka more? Nikam ba more ba

She saw did she see? She didn’t see – Ta gani shin ta gani? Itakam bata ganiba

They went they go? They didn’t go – Sunje su shin sun tafi? Sukam basu tafi ba

Did you go out last night? -Shin kafita waje a daren jiya?

Yes, I went to cinema but I didn’t enjoy the film much – kwarai, naje gidan film amma ban more film din sosai ba.

They didn’t invite her to the party, so she didn’t go – Basu gayyace ta zuwa wurin patin ba, sabida hakane bata jeba.

Sannan mukula yayin da akace (do) shine main verb acikin magana, alal misali

What did you do at the weekend? – Me kakeyi a hutun sati?

Kada kace (what did you at the weekend?)

I didn’t do anything. Banayin komi.

Kuma kada kace ( I didn’t anything)

Past tense din is/am/are sune was/were:

I/he/she/it past tense din su shine Was

We/you/they past tense dinsu shine Were

Amma bazamu amfani da (did) ba a negative ko kuma tambaya ba gamida was/were

I was angry because they were late – Naji haushi sabida sunyi letti

Was the weather good when you were on holiday? – Shin yanayin yayi dadi kuwa sadda kake/kike/kuke hutu?

They weren’t able to come because they were so busy – Basu samu zuwaba sabida sunada ayyuka sosai.

Did you go out last night or were you too tired? – Shin kafita waje adaren jiya kodai kagaji sosai?

Alhamdulillah nan zamu dakata

Allah yasa mu fahimta, kuma Allah yasa mukoyi turanci kamar yadda muka koyi yaren mu.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button