Common mistake in English

Kalmomin da ake amfani da su domin maye gurbin VERY

Kalmomin da ake amfani da su domin maye gurbin VERY

Assalamu alaikum, jama’a. Barkan mu da warhaka da kuma sake haɗuwa a wani sabon darasi mai matukar muhimmanci ga dalibai da sauran waɗanda ke sha’awar koyan turanci. Kamar dai kullum yau ma, mu na ɗauke da wani darasi da zai gyara ko saitawa daliban turanci kurakuran da suke aikatawa a cikin maganganun su ko rubuce-rubucen su.

Wannan kuskure shine yawaita yin amfani da kalmar VERY domin bayyana wata siffa ko wani mataki da wata siffa ta kai. Abu mai kyau a na ce masa “good” a turanci. Idan kuma kyan sosai ne, sai a haɗa kalmar “good” tare da “very” domin nuna cewa wannan kyan sosai ne. To yawan yin amfani da irin wannan tsari na rubutu ko magana ƙwararru a ilimin turanci na ganin cewa kuskure ne. Domin akwai wasu kalmomi da a karan-kansu su na ƙunshe da wannan ma’ana – kuma da su ya kamata a yi amfani.

Kaman kalmar “excellent” ita kaɗai ta na nufin “very good” kalmar “serene” na nufin “very calm” kalmar “filthy” na nufin “very dirty” kalmar “gorgeous” na nufin “very beautiful” da dai sauransu. Indai akwai wata kalma guda ɗaya da za ta bayar da ma’ana irin wacce kalmomin da ake haɗawa da VERY su ke bayarwa, to ya fi kamata a yi amfani da wancan kalmar sama da wata kalma tare da VERY.

Abun nufi shine idan abun ya na a matakin da aka saba to sunan sa kaɗai ake ambata. Amma idan kuma matakin sa ya wuce yadda aka saba, sai ayi amfani da kalmar VERY tare da wata siffa domin nuna matakin da wannan abun yake. Ko a Hausa a maimakon ka ce “mai kuɗi sosai” gwara ka ce “attajiri” hakama “ƙaƙƙarfa” na nufin “mai ƙarfi” “babba sosai” sai a ce “ƙato”.

Bari mu ga irin waɗannan kalmomi tare da kalmomin da ke maye gurbin su.
Very angry – furious
Very bad – atrocious
Very big – huge
Very cute – adorable
Very happy – ecstatic
Very hard – arduous
Very risky – perilous
Very shiny – gleaming
Very short – brief
Very shy – timid
Very strong – forceful
Very weak – frail

Yanzu kuma bari mu ɗauki waɗannan kalmomi ɗaya bayan ɗaya mu yi bayani tare da misalan su.

1. Very angry
Very angry na nufin jin haushi sosai. Akan yi amfani da kalmar furious domin maye gurbin very angry.

Misali
I am very angry for being late.
I am furious for being late.
Na ji haushi sosai saboda makarar da na yi.

He was very angry after the match.
He was furious after the match.
Ya ji haushi sosai bayan tashi daga wasan.

2. Very bad
Very bad na nufin maras kyau sosai. Akan yi amfani da kalmar atrocious domin maye gurbin very bad.

Misali
The situation is very bad.
The situation is atrocious.
Yanayin ya yi muni sosai.

The food was very bad.
The food was atrocious.
Abincin ya ɓaci sosai.

3. Very big
Very big na nufin babba sosai. Akan yi amfani da kalmar huge domin maye gurbin very big.

Misali
Whale is a very big sea creature.
Whale is a huge sea creature.
Whale halittar ruwa ce mai girma sosai.

Elephants are very big animals.
Elephants are huge animals.
Giwaye manyan dabbobi ne.

4. Very cute
Very cute na nufin kyau sosai. Akan yi amfani da kalmar adorable domin maye gurbin very cute.

Misali
Her picture was very cute.
Her picture was adorable.
Hoton nata ya yi matukar kyau.

They bought a very cute car.
They bought an adorable car.
Sun siyo mota mai matukar kyau.

5. Very happy
Very happy na nufin farin ciki sosai. Akan yi amfani da kalmar ecstatic domin maye gurbin very.

Misali
We were very happy to meet you.
We were ecstatic to meet you.
Mu na farin ciki sosai domin haɗuwa ku.

You are very happy with the results.
You are ecstatic with the results.
Ka na farin ciki sosai da sakamakon.

6. Very hard
Very hard na nufin wahala sosai. Akan yi amfani da kalmar arduous domin maye gurbin very hard.

Misali
Mathematics is a very hard subject.
Mathematics is an arduous subject.
Lissafi darasi ne mai matuƙar wahala.

The homework was very hard.
The homework was arduous.
Aikin gudan mai matuƙar wahala ne.

7. Very risky
Very risky na nufin kasada sosai. Akan yi amfani da kalmar perilous domin maye gurbin very risky.

Misali
Climbing a mountain is very risky.
Climbing a mountain is perilous.
Hawa tsauni na da babbar kasada ce.

Walking in jungles is very risky.
Walking in jungles is perilous.
Tafiya da ƙafa a cikin ƙungurmin daji na da matuƙar haɗari.

8. Very shiny
Very shiny na nufin jin kunya sosai. Akan yi amfani da kalmar gleaming domin maye gurbin very shiny.

Misali
Our shoes are very shiny.
Our shoes are gleaming.
Takalmanmu su na kyalli sosai.

The new car is very shiny.
The new car is gleaming.
Sabuwar motar na kyalli sosai.

9. Very short
Very short na nufin taƙaitacce sosai. Akan yi amfani da kalmar brief domin maye gurbin very short.

Misali
The explanation is very short.
The explanation is brief.
Bayanin a taƙaice yake sosai.

Her holiday is very short.
Her holiday is brief.
Hutunta taƙaitacce ne sosai.

10. Very shy
Very shy na nufin jin kunya sosai. Akan yi amfani da kalmar timid domin maye gurbin very shy.

Misali
She is very shy.
She is very timid.
Ta na jin kunya sosai.

Why are you very shy?
Why are you timid?
Me ya sa kake jin kunya sosai?

11. Very strong
Very strong na nufin karfi sosai. Akan yi amfani da kalmar forceful domin maye gurbin very strong.

Misali
The wind was very strong.
The wind was forceful.
Guguwar na da matuƙar ƙarfi.

Lion is a very strong animal.
Lion is a forceful animal.
Zaki dabba ce mai matukar ƙarfi.

12. Very weak
Very weak na nufin yin rauni sosai. Akan yi amfani da kalmar frail domin maye gurbin very weak.

Misali
The old man was very weak.
The old man was frail.
Tsohon ya rauni sosai.

The boy is very weak after his recovery.
The boy is frail after his recovery.
Yaron ya yi rauni sosai bayan warkewarsa daga jinya.

  1. Waɗannan su ne misalan yadda za a rage yawan amfani da kalmar VERY, domin inganta turanci. Idan da mai tambaya sai ya yi ƙasa wajen comment ya rubuta – idan Allah ya sa mun sani za mu ba shi amsa.

Leave a Reply

Back to top button