Pronoun

Menene Personal Pronoun a cikin karatun turanci?

Menene Personal Pronoun a cikin karatun turanci?

Personal Pronoun ɗaya ne daga cikin wakilan suna kamar dai yadda a ka gani a darasin da ya gabata. Personal Pronoun su ne mafi shahara, domin su ne waɗanda mukafi sanin su a matsayin wakilalan suna sakamakon su ne mu ka fi amfani da su a maganganun mu na yau da kullum .

Personal pronoun wakilan suna ne da ke temakawa mai magana / rubutu don ya fayyace wa masu sauraron shi ko karanta rubutun shi a kan shi karan kanshi ya ke magana ko wanin shi, sannan akan mace ne ko namiji. kuma suna da yawa [mutanen ko abubuwan da yake maganar a kai] ko kuma guda ɗaya ne—dadai sauransu.

Za mu ga cikakkun jawabai idan mun shiga cikin darasin in sha Allah.

Misalan Personal Pronoun

 1. I
 2. It
 3. Us
 4. He
 5. We
 6. Me
 7. She
 8. Her
 9. Him
 10. You
 11. They
 12. Them

Da fari ya kamata mu san cewa kafun mutum ya san yadda ake amfani da personal pronoun daidai dole akwai wasu abubuwa da sai ya san su, domin su kamar dokoki ne da ke temakawa wajan yin amfani da Personal pronoun ɗin daidai.

— Abubuwan sune kamar haka

 1. Number
 2. Person
 3. Gender
 4. Case

1. Number

‘Number‘ shine yawan abu. Dole ne sai an kiyaye da yawan abu (thing), mutum (person) ko dabba (animal) da ake magana a kan su. Wato ‘Singular’ ko ‘Plural’ (Me yawa ne kokuma guda ɗaya ne? ) domin idan abu, mutum ko dabba guda ɗaya ne akwai na shi kalmomin ‘Personal pronoun‘ ɗin, sannan idan suna da yawa ma akwai waɗanda za a yi amfani da.

Kalmomin Singular sun haɗa da;

 1. I
 2. It
 3. He
 4. Me
 5. She
 6. Her
 7. Him

Kalmomi Plural sun haɗa da;

 1. Us
 2. We
 3. You
 4. They
 5. Them

2. Person

Person na nifin mutum. Mutum kuma ya kasu kashi uku a giramar Ingilishi.

Ga su kamar haka;

 1. First person
 2. Second person
 3. Third person

1. First person

First person shi ne mutum na farko, wato wanda ya ke yin magana. Misali, kamar ni idan ina yin magana toh ni ne First person, sabida haka duk kalmar da zan yi amfani da ita dole ta kasance daga kalmomin First person ɗin. Yayin da mu ke magana, maganar mu na tafiya ne tare da ɗaya daga cikin waɗannan nau’ukan person uku da mu ka gani.

Ga misalansu;

 1. I
 2. Us
 3. Me
 4. We

First person ya kasu gida biyu;

 1. 1. First person singular
 2. First person plural
1. First person singular

First person singular shi ne mutum na farko kuma guda ɗaya (1) . Wato idan ya kassance maganar da ka ke ka na magana ne akan kanka, ba waninka ba. Sannan kai kaɗai ne ba tare da wani ko wasu ba. Toh za ka yi amfani da kalmomin da ke nuni da mutum na farko guda ɗaya.

Ga su kamar haka;

1. I
2. Me

2. First person plural

First person plural shi ne mutum na farko amma fiye da ɗaya (1)— Ka na magana amma magana kake a kan kai da kuma wani ko wasu. Wato ba a kan kai kaɗai kake batun ba, kai da wani ko wasu ne kuke magana akan abun da kukan yi (simple present), ku ka riga da kuka yi (Past forms ) ko ku ke kan yi (Present continuous) ko za ku yi (Future) kai da wani ko wasu ne to se ka yi amfani da kalmomin pronoun da ke a wannan siffar ta First person plural.

Kalmomin sun haɗa da;

1.Us
2. We

2. Second person

Second person shi ne mutum na biyu. Wato abokin magana. Idan ka na magana da wata, ita wannnan da kuke maganar — Indai magana ka ke a kan wani abu da takan aikata, ko take aikatawa, ko take kan aikatawa ko ma za ta aikata nan gaba ko ka ke umarta ta aikata, ko dai wani nau’i na magana muddin dai maganar da itan ka ke yi toh za ka yi amfani da kalmomin 𝗦𝗲𝗰𝗼𝗻𝗱 𝗽𝗲𝗿𝘀𝗼𝗻.

Ga kalmar kamar haka;

1. You

Second person sun kasu kashi biyu:

 1. Second person singular
 2. Second person plural
1. Second person singular

Second person singular shi ne mutum na biyu amma mutum ɗaya wato kamar yadda na yi jawabi a ‘Second person’ kenan, amma se abokin maganar ko abokiyar maganar sun kasance guda ɗaya tal!

Ga kalmar kamar haka.

1. You

2. Second person plural

Second person plural Shi ma dai mutum ne wanda ake hira da shi. Sedai ba mutum ɗaya ba, da ga mutum biyu zuwa sama. Idan abokan hira sun fi ɗaya, to lallai-lallai wajan yin amfani da kalmar da za ta daidaita da mumun na biyun sai an yi amfani da kalmar ‘Second person plural’.

Ga kalmar kamar haka.

1. You

3. Third person

Third person kuma shi ne mutum na uku—wato wanda ‘First person‘ da ‘Second person’ ke magana a kan shi.

Misali; Ni da nake magana ni ne mutum na farko(First person). Ku da kuke saurare na ko kuma muke maganar tare, ku ne ‘Second person‘ sannan mutumin (person), dabbar (animal), wajen (place) ko abun (thing) da muke maganar a kan shi ko a kan su, sune ‘Third person‘.

Ga kalmomin su kamar haka;

 1. Them
 2. They
 3. Him
 4. Her
 5. She
 6. He
 7. It

Third person ya kasu kashi biyu;

 1. Third person singular
 2. Third person plural
1. Third person singular

Third person singular; Shi ne mutum na uku guda ɗaya, wato mutin da, ko dabbar da ko kuma wajan da ake magana akan shi sannan ya kasan ce guda ɗaya tal!

Ga misalansu;

 1. Him
 2. Her
 3. She
 4. He
 5. It
2. Third person plural

Third person plural shi ne mutum na uku masu yawa. Wato sun zarce guda ɗaya, sannan a kan su ne ake magana. Ba su ne ake magana tare da su ba kamar yadda muka gani a baya.

Ga misalansu;

 1. Them
 2. They

3. Gender

Gender shi ne jinsin abu ( thing), mutum (person) ko dabba (animal) . Toh se an san jinsin abun, mutumin ko dabbar, kafin a san kalmar da zai dace da ita, Koda yake a yaren turanci yawancin abubuwa (things) wasu lokutan ma da dabbobi (animals), ba a cika la’akkari da su a matsayin abubuwa ma su jinsi ba, hakan ne ma ya sa yawanci ake amfani da (IT) a magana domin nuni da su, da kuma (ITS) domin nuna mallakin su kamar yadda za mu gani darrusan da za su zo nangaba in sha Allah.

Rabe raben gender

Gender — Wato Jinsi sun kasu gida uku (3) zuwa huɗu(4)

1. Masculine —> Jinsin maza;

Misali;

 1. Tailor —> Tela na miji
 2. Author —>marubuci
 3. Wizard —> maye
 4. Dadai sauransu……

2. Femine —> Jinsin mata

Misali;

 1. Seamstress —> Tela mace
 2. Authoress —>Marubuciya
 3. Witch —> Mayya
 4. Dadai sauransu……

3. Commom —>Jinsin da yake na maza da mata

Misali;

 1. Teacher —> Malami/ Malama
 2. Student —> Ɗalibi/ Ɗaliba
 3. Child —> Yaro/ Yarinya
 4. Dadai sauransu……

4. Neuter —>Jinsin da ba namiji ba, ba mace ba.

Misali;

 1. Orange —>Lemo
 2. Watch —>Agogo
 3. Phone —>Waya
 4. Dadai sauransu……

4. Case

Idan aka ce ‘Case‘ to a na magana ne akan kasancewar kalmar ɗaya daga cikin waɗanda ake sanya su a matsayin Subject a cikin jimla ko kuma a matsayin Object. Wato shine yayi aiki ko kuma akan shi akayi aikin.

Dukkannin waɗannan kalmomin pronoun guda goma sha biyu da na bayar wajan misalai sun rarrabu zuwa waɗan da ake amfani da su a matsayin Subject ko Object da ma waɗanda ake iya amfani da su a wajaje biyun (Subject da Object). Wato a taƙaice dai ilahirin waɗannan misalai da na bayar kama daga NUMBER zuwa GENDER zuwa PERSON har zuwa CASE.

A taƙaice dai idan a ka ce Subject a dokar yaren Ingilishi na girama, a na nifin wani abu (thing), ko wani mutum (person), ko wata dabba (animal) — wanɗanda Sukan aikata,(Simple present) ko Suka riga da suka aikata (Past forms ) ko suke kan aikatawa (Present continuous) wani aiki acikin jimla.

Misalan Subject pronoun

 1. They
 2. You
 3. She
 4. We
 5. He
 6. It
 7. I

Idan kuma aka ce ‘Object’ ana nufin wanda aikin Subject ɗin ya aukawa (Ya faru da).

Misalan Object pronoun

 1. Them
 2. Him
 3. You
 4. Her
 5. Me
 6. Us
 7. It

Wannan shi ne jawabi a taƙaice kenan, domin akwai dogon bayani dangane da ‘Subject‘ da kuma ‘Object‘ in sha Allah nan gaba zan yi.


Note:
kalmar YOU na na daga cikin ‘Singular pronoun‘ sannan ta na daga cikin ‘Plural pronoun’ hakan na nifin za mu iya amfani da ita akan ‘mutum na biyu guda ɗaya’ da kuma ‘mutum na biyu fiye da ɗaya’.

Sai kuma kalmomin YOU ɗin da kuma IT, za ku gan su a ‘Subject pronoun‘ da kuma ‘Object pronoun‘, toh dukkan su su biyu ana iya amfani da su a matsayin Subject ko kuma Object. Eh ana iya amfani da su a duka wajajen guda biyu kuma hakan shi ne daidai.

Idan abu ya kasance wanda ba a san jinsin shi ba (Neuter) sai a yi amfani da IT. Wasu lokutan kuma harma da dabbobi akan yi amfani da IT akan su, sai dai akwai jawabi me ɗan zurfi da zan yi akan hakan idan na samu dama in sha Allah.

Ban kawo misalai a cikin jimloli ba ne sabida rubutun zai yi yawa sosai idan na yi hakan, sabida ko wacce jimla sai na sake jawabi a kan ta bayan fassara ta, kun ga kenan rubutun zai kusa ninka wannan, kuma dama kamar wannan ɗin ma ya ɗan yi yawa ko🙄?

Toh amma kuna da damar haɗa jimloli da kowacce daga cikin misalan da na bayar sannan ku yi tambaya a kan jimlar da ku ka haɗa ɗin a sashin tsokaci (Commen section). Idan kuma akwai abun da ba ku gane ba se ku tambaya.

Iya kacin abun da Allah ya ba ni damar kawowa kenan dangane da personal pronoun, sai mun haɗu a darasi na gaba. Idan akwai kurakurai da aka gani a cikin wannan darasi sai a yi mun gyara dan Allah

A huta lafiya……
Hussain Abdullahi

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Leave a Reply

Back to top button