Koyon TensesTenses

Me ake nufi da future perfect tense a cikin karatun turanci?

Me ake nufi da future perfect tense a cikin karatun turanci

LEARN TENSES: FUTURE PERFECT TENSE

A darasinmu na Tenses da mukeyi bangaren Future tense, inda a darasinmu daya gabata a cikin wannan shafin munyi bayani ne akan Future tense, da kuma Future continuous tense, saboda haka a wannan darasin zamuyi bayani ne akan Future Perfect Tense

Menene Future Perfect Tense?

Shi Future perfect tense yana nuna cewa a lokaci mai zuwa ma’ana nan gaba, abinda zai faru ko ya afku zai zama anyi shi an gama, galibi Future perfect tense yana nuna hasa she ne na abinda ake sa ran za’a soma shi a lokaci kaza mai zuwa, a kuma gama shi a lokaci mai zuwa.

Shi Future perfect tense yana zuwa ne tare da “Will” ko “Shall” don ya nuna cewa aikin zai faru ne anan gaba, Sannan kuma sai a hadashi da kalmar auxiliary verb, wato “have” don a nuna gamawar aiki, Sannan kuma sai kalmar past participle na main verb ya biyo baya

ALSO READ: Yadda ake gane singular and plural na verb a turanci

Yadda ake hada Future perfect tense a positive sentence

Da farko dai zaka saka “subject” ne, sai ka saka “will”, sai ka saka “have”, sai ka saka kalmar past participle a karshe (kuna iya duba darasin na past participle a cikin wannan shafin), ga formula a takaice: S + will + have + past participle + ….

duk inda kaji ance “Subject” yana nufin mai aiki acikin jimla, a takaice dai Subject zai iya kasancewa suna (noun) ko wakilin suna (pronoun), yanzu bari mukawo misali na future perfect tense a cikin jimla

Nasir I. Mahuta will have finished that Sirrin crypto next month = Nasir I. Mahuta wata mai zuwa zai riga ya gama rubuta littafin Sirrin crypto

Karin bayani: Idan mukayi duba a wannan jimlar Nasir I. Mahuta ana sa ran zai gama rubuta littafin Sirrin Crypto a wata mai zuwa

He will have heard about the death of his father by ten o’clock tomorrow = zai gama jin zancen mutuwar mahaifin sa gobe da karfe goma

Karin bayani:- kaga wannan jimlar ma yana nuna cewa ana zaton gobe zuwa karfe goma tuni labarin mutuwar mahaifinsa taje masa

You will have finished the building by this time next year = Zaka riga ka gama wannan ginin a irin wannan lokacin shekara mai zuwa

Karin bayani: kaga a wannan jimlar ana hasashen cewa zai gama gini a shekara mai zuwa, duk a cikin future tense, wato aikin da zai faru nan gaba, saboda hakane ma yake zuwa da kalmomin “Will” ko “Shall” domin ya nuna mana cewa aikin sai nan gaba zai faru, Shikuma aikin (verb) yazo da sigar aikin da ya wuce, saboda ana nufin an gama aikin

ALSO READ: Sunayen Bishiyoyi/Itatuwa (Trees) da turanci zuwa harshen hausa
Me ake nufi da De Prefix a cikin karatun turanci?

Yadda ake hada future perfect tense a negative sentence

Da farko zaka saka “Subject” (wato mai aikin) a farkon jimla, sai ka saka “will”, sai ka saka “not”, sai ka saka “have”, sai kuma ka saka kalmar “past participle” a karshe, ga formula a takaice S + will + not + have + past participle + … bari mu kawo misali a cikin jimla

He will not have heard about the death of his father by ten o’clock tomorrow = Ba zai gama jin labarin mutuwar mahaifinsa ba gobe da karfe goma

Yadda ake hada future perfect tense a Question form

Da farko zaka saka kalmar “will” a farkon jimla, sai ka saka “subject”, sai ka saka “have”, sai ka saka kalmar “past participle” a karshe, ga formula a takaice: Will + s + have + past participle + … bari mu kawo misali a cikin jimla

will you have heard about the death of your father by ten o’clock tomorrow? = Shin zaka gama jin zancen mutuwar mahaifinka gobe da karfe goma?

MASU ALAƘA: Menene simple future tense da hausa?
Me ake nufi da future continuous tense a cikin karatun turanci?
Me ake nufi da future perfect continuous tense a cikin karatun turanci?

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button