part of speech (Hausa)Verb

Menene Phrasal verbs a hausa?

Wasu da yawa sun iya turanci Amman in anyi musu magana da wasu kalmomi irinsu phrasal verbs idiomatic expression Ko euphemism words Sai su kasa reply so akwai solutions
Phrasal verbs Yana da matukar amfani sosai ba kaɗan ba
A 100% na verbs 80% Duk phrasal verbs Kuma da su ake amfani yau da kullum yanzu zanyi bayani Mai gansarwa akanshi insha Allahu

MENE NE PHRASAL VERBS?

Phrasal verb hanyace da ake hada kalmar verb da preposition, domin gina wata sabuwar kalma mai sabuwar ma’ana.
Misali “take” ya na nufin rikewa, ko dauka, ko kulawa, ko sha kamar na ruwa da sauran ma’anoninsa. Sai kalmar “off “ ta na nufin opposite ko opposition. Idan ka hada “take” da “off” kalmar za ta dauki sabuwar ma’ana.

Misali acikin jimla

 1. Our plane takes off tonight.
  Ma’ana: jirgin mu zai tashi a daren yau.
 2. Take your shoes off before enter.
  Ma’ana: ka cire takalmanka kafin ka shigo.

A misalai biyu dake sama “take off” ya zo da ma’anoni daban-daban. Duk phrasal verb za ka samu akalla ya na da ma’anoni guda biyu ko uku zuwa sama. Amma akan samu masu ma’ana guda dayan ma, sai dai ba su da yawa.

Types Of Phrasal Verbs

Phrasal verb an rabasa gida biyu, akwai SEPARABLE da kuma INSEPARABLE.

SEPARABLE PHRASAL VERBS:

Seperable phrasal verbs, su ne phrasal verbs din da ake iya raba tsakaninsu da wata kalma. Wato a tsakanin kalmar verb da preposition ake sa wata kalma musamman objective. A misalai biyu dake sama, za mu ga a misali na biyu tsakanin kalmar “take” da kalmar “off” na rubuta “your shoes” kenan an raba tsakaninsu da wata kalma.

INSEPARABLE PHRASAL VERBS:

Inseparable phrasal verbs su ne phrasal verbs din da ba a iya raba tsakaninsu. Wato tsakanin kalmar verb din da preposition ba iya sa komai, a misalai biyu dake sama, a misali na farko tsakanin kalmar “take” da “off” ban rubuta komai ba domin ba a iya raba tsakanin su.

ABIN LURA ANAN SHINE:
Akan samu kalma daya ta phrasal verb ta zamo separable, wani lokaci kuma inseparable. Wato idan ta zo da wata ma’ana separable ce. Haka kuma inseparable ce da wata ma’anar daban da ma’anar farko.

Kaman kalmar phrasal verb ta “take off” ta kan zo separable, kuma ta kan zo a inseparable. Idan ta zo a tsakaninta ba a sa komai ba, ta kan dauki ma’anar “fly” wato tashi sama na jirgi, ko tsuntsu. Amma idan kalmar tazo a tsakanin ta an sa wata kalma, ma’anar za ta koma “remove” wato cirewa.

Kalmomin phrasal verbs ba su da wata ka’ida da ake amfani da ita wajen gano ma’anoninsu, sai dai yanda aka koyar da kai, ko kuma ka gani a kamus (dictionary). Phrasal verb ya na da wahala hatta wasu daga cikin turawa kan rikitar da su. Sannan mafi yawa kalmomin da ake hada su da preposition din “up” su kan zo a matsayin umarni.

Misali:

 • Hey, Nura eat up your food!
  Ma’ana: kai Nura ci abincinka
 • Abdullahi get up!
  Ma’ana: Abdullahi tashi.

.

 • Fati sweep up this room!
  Fati ki share dakin nan.

MISALAN PHRASAL VERBS:

Get away – wannan kalma ta na da ma’anoni hudu ko sama da haka.

 • i. ta na nufin tafi ka kyaleni; ko kyaleni.
 • ii. ka buya, ko guduwa, ko kaucewa wani dake neman kamaka.
 • samun hutu a makaranta ko wajen aiki.

ga misalansu acikin jimla

i. I don’t know why she got away from me.
Ma’ana: ban san me ya sa ta kyaleni ba.

ii. The crimals had got away when the policemen arrived at the scene.
Ma’ana: ‘yan sandan sun isa wajen da aka aikata lefin, yayin da tuni masu lefin sun riga sun gudu.

iii. He thinks, he gets away at Kano, with his family.
Ma’ana: ya na tunanin tafiya hutu Kano tare da iyalensa.

Make up – ta na da ma’anoni biyu ko sama da haka.

 • i. kwalliya
 • ii. hada wani abu ko kirkirar wani abu.

Misali acikin jimla

i. Your make up, makes me to laugh.
Ma’ana: kwalliyarki ta na ban dariya.

ii. This Tea is made up of water, sugar and Lipton.
Ma’ana: wannan shayin an yi shi ne da ruwa da sukari da kuma ganyen shayi na Lipton.

Go off – ta na da ma’anoni sama da biyu:

 • i. fashewa kamar ta bomb.
 • ii. lalacewar abu kaman abinci.

Misali acikin jimla

i. A huge bomb goes off.
Ma’ana: wani babban bam ya fashe.

ii. Mum I can’t eat this food, because it went off.
Ma’ana: Mama abincin nan yalalace, shi ya sa ba zan iya ci ba.

Call off – sokewa, musamman wani abu da aka sa lokaci za a yi.

Misali acikin jimla

The Minister has called off the meeting due to social distance.
Ma’ana: ministan ya soke taron saboda dokar ba-da-tazara ta coronavirus.

Look out – ta na da ma’anoni kaman haka:

 • i. duba ka gani
 • ii. ka lura (gargadi)

Misali acikin jimla

i. Look out the table and you will see my book.
Ma’ana: duba kan teburin za ki ga littafi na.

ii. Hey my friend, look out there are passing cars down this street.
Ma’ana: abokina ka lura akwai motoci masu wucewa a layin nan.

Interestingly we don’t use phrasal verbs as much when we write in formal communication like in a speech but in normal spoken English about 80 percent of our verbs are phrasal verbs.
Phrasal verbs are both very common in English conversation but also very confusing for a people who don’t understand them that’s why studying phrasal is very important if you Want to really improve your English skills.

Here are some phrasal verbs
Please try to read them and make sure you memorise them because they are common

 • Put up with =Tolarence
 • Get at=contact
 • Getting at =means
 • Look around=search
 • Look for=seeking
 • Come back =return
 • Feeling down=depressed
 • Break into=inter {illegally)
 • Hold up=wait
 • Turned out=attend
 • Come along=accompany
 • Talk over=descuss
 • Set back=delay
 • Take away=remove
 • Turn off= stop
 • Turn on=start
 • Write off=concel
 • Written for =apply
 • Cup of tea=concerned/palaver
 • Back up=support
 • Ask for=request
 • Be back=retur
 • Get up=rise stand
 • Cut up=fell

Please duk abinda mutum Bai ganeba yayi tambaya Kuma ka ɗauki biyu kayi misali da su
Wannan ana yawan amfani da su Ko a cikin films ne ma mutum Sai yarasa miye suke nufi
Inba ka san ma’anarsuba bazaka taba ganewaba Ko da mutum yayi Maka magana da su saboda sun canza ma’ana a yadda mutum ya sansu

Ya kamata muna practice don muyi improving na turancin mu

One Comment

Leave a Reply

Back to top button