Kalmomi

Yanda zakayi amfani da kalmomin “Will” da kuma “Shall” a turanci zuwa Hausa – Kalmomi

Yadda zakayi amfani da kalmomin “Will” da Kuma “Shall”

Maraba da sake kasancewa acikin wannan shafin na Karatunturanci
Now we are going to discuss about WILL and SHALL

Zamuyi ampani da I’ll (I will) yayin da muka yanke shawaran yin wani abu a dai dai lokacin da muke maganan. Misali

Oh, I have left the door open, I will go and shut it. – Kash! na bar murfin kofa a bude, zanje na rufeshi

What would you like to drink? I will have an orange juice, please. – Me kake so kasha? Yi hakuri, ina da jus na lemo.

Did you phone Aisha? Oh no, I forgot, I will phone her now. – Shin ka kira Aisha? Kash A a, na manta, ama yanzun zan kirata.

Idan kun lura duk abinda muka fada abune da za’a Aikata shi ayanxu, kuma baza muyi amfani da past simple ba misali, (I go and shut the door) wannan baiyi ba sam. Sai dai muce (I will go and shut the door)

Sau da yawa zamu iya amfani da (I think I will) dakuma ( I don’t think I will) misali

I feel a fit hungry, I think I will have something to eat. – Ina jin guntuwar yunwa, nayi tinanin insamu wani abu inci.

I don’t think I will go out to night, I’m too tired. – Bana tinanin zan fita waje da dare, agajiye nake sosai.

Acikin maganan turanci negative din (will) shine ana amfani da won’t ( will not) Misali

  I can see you are busy, so I won’t stay long. – Naga kanada aiyuka, dan haka bazan jima ba.
  Kuma baza zamuyi amfani da (will) ba yayin da muka yanke shawara ko shirya yin wani abu nan gaba. Misali

   I’m going on holiday next week – zanje yin biki sati mai zuwa, kada kace ( I will going to)

    Are you working tomorrow? – zakayi Aiki gobe?
    Kuma kada kace ( will you work)
    Kuma zamu iya amfani da (will) a irin wannan yanayin da zamu kawo misali yanzun.

    • Offering to do something – Taimako/hadaya zuwa yin wani abu. Misali
    • That bag looks heavy. I will help you with it. – Jakan nan dagani tayi nauyi, zan taimaka maka dangane da jakan
    • Agreeing to do something – yarda zuwa yin wani abu. Misali
    • You know that book I lent you. Can I have it back when you finished with it? – Kasan littafin nan ara maka nayi. Shin zan samu ka dawomin dashi idan kagama dashi?
     Of course, I will give it to you this afternoon. – Eh mana, zan kawo maka dashi da yamma, kuma kada kace (I give it to you)
    • Asking somebody to do something – tambayar wani zuwa yin wani abu, wato (will you)
    • Will you please be quiet? I’m trying to concentrate – Shin zakayi hakuri kayi shiru, ina qoqarin tattare wa.
    • Will you shut the door, please – Shin zakayi hakuri ka rufe kofar?

    Zamuyi amfani da won’t (will not) domin muce wani yaki Aikata wani abu.

    • I have tried to advice her but she won’t listen. ( she refuse to listen) – Nayi kokarin bata shawara amma bata sauraraba (taki ta saurara)
    • The car won’t start. I wonder what’s wrong with it. ( the car refuse to start) – Motar bata tashi ba, nayi mamakin meye matsalar ta, ( motar taqi tashi)

    Sannan sai (Shall l?) (Shall we?) Anfiye anfani da “Shall” wurin yin tambaya kodai bada shawara haka. Misali

    • Shall I open the window (do you want me to open the window?) – Shin zan bude taaga? ( shin kanaso na bude taaga?)
    • I have got no money. What shall I do? ( what do you suggest?) – Ban samu kudi ba. Me zanyi ne? ( meka shawar ka?)
    • Shall we go? I’m not ready yet – Shin zamu tafi ne? Ban shirya ba tukun.
    • Where shall we go this evening? – Ina ne zamuje awanan yammacin?

    Idan zamu kwatanta Shall I? dakuma Will you?

    • Shall I shut the door? ( do you want me to shut it?) – Shin zan rufe kofan ne? ( kanaso na rufe kofan ne?)
    • Will you shut the door? ( I want you to shut it) – Shin zaka rufe kofan ne? ( inaso kai karufe kofan)

    Idan zamuyi amfani da “Shall” sai muce (I shall/we shall)
    Idan kuma “will” ne sai muce (he will/it will/she will/you will/they will)
    Kuma kada kace (he shall/she shall/it shall/you shall/they shall)
    Barkan mu da warhaka, idan akwai abinda baka fahimta ba yimana comment aka domin samun amsarka

    Karatunturanci

    I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

    Related Articles

    Leave a Reply

    Back to top button