Koyon TensesTenses

Me ake nufi da future continuous tense a cikin karatun turanci?

Me ake nufi da Future continuous tense a cikin turanci?

LEARN TENSES: FUTURE CONTINUOUS TENSE

Darasin mu akan Tenses, kuma a karkashin Future tense, a darasin da ya gabata munyi shine akan simple future tense, inda mukayi bayani cewa duk wani aiki da zai faru nan gaba to lallai wannan aikin future tense ne, saboda haka a wannan darasin zamuyi bayani ne akan Future continuous tense

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci
Sunayen Bishiyoyi/Itatuwa (Trees) da turanci zuwa harshen hausa

Menene Future Continuous Tense?

Anayin amfani da Future continuous tense ne lokacin da akeson nuna cewa aiki zai cigaba da faruwa lokaci mai zuwa, kamar kanaso kace “zamu dinga yin rawa a wajen bikin gobe da yamma” kaga idan ka lura da wannan, ana nuna wani aiki ne da zai ta faruwa wani lokaci da zai zo.

Ana samar da future continuous tense ne kawai ta hanyar amfani da kalmar “will” ko “shall”, sai a hada shi da kalmar “be” daga nan kuma sai a hada shi da kalmar “present participle” (present perticiple kalmomin aiki ne wanda a kowani lokaci suke karewa da -ing), ga formula a takaice Will + be + present participle

ALSO READ: Yadda ake amfani da Apostrophe a cikin jimla (Possessive S)
Me ake nufi da Dis prefix a cikin darasin turanci?

Yadda ake hada future continuous tense a positive

Da farko zaka saka “subject” ne a farkon jimla, sannan sai ka saka kalmar “will” ko “shall”, sannan kuma sai ka saka “be”, sai kuma kalmar “present participle” yazo a karshe, ga dai formula a takaice: S + wil/shall + present participle, bari mu kawo misali a cikin jimla

We shall be dancing at the occasion tomorrow afternoon = Zamu dinga yin rawa a wajen bikin gobe da yamma

My sister will be studying at the college of education kano next year = ‘Yar uwata zata dinga yin karatu a makarantar horar da malamai ta kano shekara mai zuwa

ALSO READ: Kalmomin Turanci masu haruffa uku (Three letters words)
Hira tsakanin ‘yan uwa guda biyu (Ahmad da Fatee) a turanci zuwa Hausa – Conversation

Yadda ake hada future continuous tense a Negative sentence

Da farko zaka saka “subject” (mai aiki) a farkon jimla, sai ka saka “wil/shall”, sai ka saka “not”, sai kuma ka saka kalmar “present participle” a karshe, ga formula a takaice: S + wil/shall + not + be + present participle + … bari mu kawo misali a cikin jimla

We shall not be dancing at the occasion tomorrow afternoon = Ba zamu dinga yin rawa ba a wajen bikin gobe da yamma

Yadda ake hada future continuous tense a Question form

Da farko zaka fara saka kalmar “will” ko “shall” a farkon jimla, sai ka saka “subject”, sai ka saka kalmar “be”, sai kuma “present participle” a karshe, ga formula a takaice: Wil/shall + s + be + present participle (V -ing) bari mu kawo misali a cikin jimla

Shall we be dancing at the occasion tomorrow afternoon? = Shin zamu dinga yin rawar a wajen bikin gobe da yamma?

Wadannan sune misalan future continuous tense a cikin jimla, a takaice dai future continuous tense aiki ne da ake hasashen zai ta faruwa wani lokaci da zai zo, da fatan kun fahimci wannan darasin, wanda kuma bai gane ba kofa a bude take don yin mana tambaya

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button