LearnKalmomiKaratun Turanci

Bambancin kalmomin dake karewa da -NCE da kuma -NT

Different Between Nt And Nce Words.

BAMBAMCIN KALMOMIN DAKE KAREWA DA -NCE DA KUMA -NT

Akwai kalmar dake karewa da -nce, wani lokaci kuma takare da -nt. Misali, dependence da dependent, ko importance da important, ko arrogance da arrogant, ko assistance da assistant.
Wadannan kalmomi kan rikita mutum har ya kasa bambamce da wacce ya kamata ya yi aiki a cikin rubutunsa.

ALSO READ: HANYOYI (3) DA SUKE HANA MUTUM YA IYA TURANCI DA WURI


Kalmomin dake karewa da -nce, kalmomine na suna. Sannan yawancinsu basu da plural, wato arrogance ba a cewa arrogances. Amma importance tanada plural wato importances.

Misali,

  • Arrogance – girman kai
  • Assistance – taimakawa/tayawa
  • Importance – amfani/mahimmanci
  • Patience – hakuri/jinya
  • Difference – Bambanci
  • Consequence – Saka mako

Su kuma wadanda ke karewa da -nt sifface ta suna.

Misali,

  • Arrogant – mai girman kai
  • Arrogants – masu girman kai
  • Assistant – mataimaki/maitayawa
  • Assistants – masu taimakawa/tayawa
  • Important – mai amfani
  • Importants – masu amfani/mahimmanci
  • Patient – mai hakuri/majinyaci

ALSO READ: Me ake nufi da Regular Plural Noun a cikin karatun turanci


Misalai a cikin jumla

1. Aliyu is a self-reliance person.❌

Aliyu is a self-reliant person.✅
Aliyu mutumne mai dogaro da kansa

2. Fahad is a self-sufficient guy.
Fahad matashine mai wadatar zuci

3. Self-sufficience makes you zero-minded.
Wadatar zuci na sa ka rashin damuwa

4. We need his assistance.
Muna bukatar taimakonsa

5. He is my assistant.
Shine mataimakina

6. Eating fresh food is important to the health.
Cin lafiyaiyen abinci na da mahimmanci ga lafiya

7. Some of the importances of water, are: drinking, washing, cooking.
Wasu daga cikin amfanonin ruwa sune: sha, wanki da girki

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button