Kalmomi

Yadda ake amfani da kalmar SINCE a Turanci

Masu kallo da bibiyar wannan tasha, Assalamu alaikum, barkanmu da yau da kuma sake kasancewa da mu a wani sabon darasi, wanda acikinsa za mu yi bayanin mece ce kalmar SINCE tare da misalanta.Kalmar SINCE ɗaya ce daga cikin kalmomin da ake kira ADVERB OF TIME. Wato kalmomin da ke bayar da ƙarin haske game da lokacin da aka yi wani aiki ko kuma wasu ayyuka.SINCE na nufin tun wani lokaci a baya har zuwa yanzu aikin da ake yi ko ake magana akansa ya na faruwa. Wato a na amfani da ita domin nuna wani aiki da aka fara yinsa tun wani lokaci a can baya, wanda har zuwa yanzu da ake magana aikin bai kammala ba, ko kuma ba a kammala shi ba.Kalmar SINCE a na amfani da ita tare da perfect tenses ne kaɗai. Sannan kuma ba a amfani da ita tare da past simple. Domin shi past simple aikine wanda aka kammala shi a wani lokaci a can baya, kuma bai ci gaba da faruwa ba zuwa yanzu. Shi kuma perfect tense aikine da aka fara tun wani lokaci a baya kuma har yanzu da ake magana ba a kammala shi ba.Mu dubi waɗannan misalai da ke tafe domin bambance tsakanin past simple da kuma perfect tense. Misali na farko past simple ne, na biyun kuma perfect tense ne.Misali:

1. I travelled to Kano last year.

Na je Kano shekarar da ta gabata.2. I have been living in Kano since 2020.

Ina rayuwa a Kano tun shekarar 2020.Misali na farko shine past simple. Wato aiki ne da na yi a wani lokaci da ya wuce a baya. Kuma aikin ya kammala tun da yanzu na dawo garinmu.Misali na biyu kuma shine perfect tense. Wato wani aiki ne da na fara tun shekarar 2020, amma har zuwa yanzu ban dawo garin mu ba.Kafin mu ci gaba. Idan wannan shine zuwanka na farko wannan tasha, ya na da kyau ka yi subscribe tare da taɓa alamar ƙararrawa. Domin yin hakan shi zai sa ka ke samun saƙonnin e-mail a duk lokacin da mu ka ɗaura sabon darasi a wannan tasha ta koyan turanci.Sai kuma mu dawo, mu ci gaba da darasin mu. Since a kan yi amfani da shi ne kaɗai tare da perfect tenses – ban da past simple kaman yadda bayani ya gabata. Yanzu kuma za mu ci gaba da kawo misalai game da yadda ake amfani da wannan kalma.

Misali:

3. I have been teaching English on YouTube since 2021.

Ina koyar da English a YouTube tun shekarar 2021.Koyar da English a YouTube aiki ne da na fara tun 2021, wato shekarar da ta wuce. Yanzu mu na 2022, kuma har yanzu ina koyar da English ɗin a YouTube.4. President Muhammadu Buhari has been ruling since 2015.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya na mulki tun shekarar 2015.Wato ya fara tafiyar da mulki tun shekarar 2015 har zuwa yanzu da mu ke 2022 shine ke mulki. Ya fara aikin tun wani lokaci a can baya kuma har yanzu shike tafiyar da mulkinsa.5. It has been raining since morning.

Ana yin ruwan sama tun da safe.A nan kuma tun da safe aka fara yin ruwan saman, amma har yanzu ruwan bai tsaya ba. Mu ɗauka cewa yanzu dare ne. Ruwan tun wani lokaci a ka fara kuma har yanzu bai tsaya ba.6. ASUU has been on strike since March.

Kungiyar ASUU ta na yajin aiki tun watan Maris.Yanzu muna watan Agusta wato wata na takwas. Ita kuma ƙungiyar ta fara yajin aiki tun watan uku, kuma har yanzu yajin aikin bai ƙare ba.7. They have been studying at B.U.K Kano since 2019.

Su na karatu a jami’ar B.U.K Kano tun shekarar 2019.A nan kuma sun fara karatu a B.U.K Kano tun shekarar 2019, yanzu muna 2022 kuma har yanzu ba su kammala karatun ba.8. We have watched football matches since we were teenagers.

Mu na kallon wasan ƙwallon ƙafa tun muna yara ‘yan shekaru goma sha.Teenager shine yaron dake tsakanin shekaru 13 zuwa 17.

Kallon wasan ƙwallon ƙafa tun mu na yara mu ke yi, amma har yanzu ba mu dai na ba. Wato mun fara aikin wani lokaci a baya kuma har yanzu ba mu dai na yin aikin ba.Ku ma ku na iya kawo naku misalan tare da wannan kalma. Hakan zai nuna mana cewa a na fahimtar darusan da ake gani a wannan tasha.Wannan shine bayanin yadda ake amfani da kalmar since tare da misalan yadda ake aiki da ita. Domin samun ƙarin wasu darusan sai a kasance da wannan tasha tamu. Idan kuma da mai tambaya sai ya rubuta zai samu amsa idan Allah ya sa mun sani.

Mun gode.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

One Comment

Leave a Reply

Back to top button