Yanda zaka iya turanci

Shawarwari gamasu son koyon harshen turanci

Shawarwari gamasu son koyon harshen turanci

Ga shawara ga mai son koyon turanci.

Wannan aji namu dai ajine na masu koyo.

Wasu yanzu ne suka fara, wasu kuma sun fara kuma suna fahimta idan akayi musu magana ko idan sun karanta, to amma mayarwa itace matsalar su saboda karancin kalmomin da zasuyi amfani dasu wajen mayarwar.

Wasu kuma suna iya mayarwar to amma basa rarrabe ka’idojin turancin abisa tsarin yadda suke.

Wasu kuma suna fahinta to amma idan akayi musu magana sai kalmomin su bace.

Amma inda za ace surubuta to zasu iya yin shi arubuce,
amma amaganace sai yayi wuya.

To ga shawara kowa sai yadauki wadda zata taimaka masa akan irin tasa matsalar.

1 Nafarko shine hakuri.

Duk mai koyo sai yayi hakuri. Kuma duk wanda yayi hakuri zayyi nasara. Amma idan kayi gaggawa to sai koyon yayi maka wuya kuma bazaka samu karfin gwiwa ba.

(2) Mayar da hankali ko bada himma.

Saboda duk abinda kanuna dagaske kakeyin sa, to Insha-Allah bazakaga wahalar sa ba. Don kuwa ba yadda za ayi kana son koyo kuma ka nuna rashin kula akan koyon kuma sai bukatar abin ta taso kuma ka nuna lokacin kake son sa.

(3) Kayi kokarin sanin kalmomin turancin dayawa.

Saboda sanin kalmomin zai iya taimaka maka wajen fahimtar me akace koda kuwa bazaka iya mayarwa ba alokacin. Kuma kada ka tsaya ko ka dogara akan ma’ana guda daya. Saboda akwai kalmomi dayawa yadda ake rubutasu duk dayane amma sunada ma’ana daban- daban.
Don wasu kawai ana kula da ma’anar su ne ta hanyar yadda sukazo a cikin jimla. {Zan kawo misalin su adarasi na gaba}

(4) Karinka yawan karanta littafi ko duk wani abu da aka rubuta da turanci.

Saboda ta hanyar karantawa ne zaka samu damar sanin yadda kalmar take arubuce. Saboda jin kalmar turanci a kunne bazai baka damar iya rubuta shi ba, kamar yadda Hausa take. Saboda akwai kalmomin turanci dayawa yadda fadar take abaki daban da yada zaka ganta arubuce. Akwai wasu kalmomin kuma fadar abaki iri dayace amma rubutun yasha banban. Haka kuma idan kana yawan karanta rubutun turanci zaka rinka cin karo da jimloli daban- daban. Kuma hakan zai sa ka kara fahintar yadda kalmomi suke fitowa da ma’ana daban-daban cikin mabanbantan jimloli. {Zan kawo misalin su a darasi na gaba}

5) Sai kuma jarraba magana da turanci ko cikin magana ko arubuce.

Saboda yin magana da turanci yana taimaka maka wajen yin magana kai tsaye ba tare da kalmomi suna makale maka ba. Kuma zai taimaka maka wajen iya furta haruffan.

(6) Kada kaji kunyar wai idan kayi za ace baka iya ba tunda ai dama koyo kakeyi.

Kuma kada ka damu don anyi maka dariya don kayi kuskure. Saboda duk wanda kaga yana yiwa mai koyo dariya, to shima bai iya ba. Saboda duk wanda ya iya idan anyi kuskure ba dariya yakeyi ba saidai ya gyara. Kuma kar kayi fushi idan ance kayi kuskure, kawai kace to agyara ma.

(7) Karinka yawan tambaya akan abinda baka gane ba.

Kuma kana iya tambayar duk wanda kake zaton yafika fahintar abin. Amma idan zaka koya to ka koya wajen wanda ya iya. Saboda idan ka koya wajen wanda bai iya sosai ba to sai ka tashi cikin kuskure. Kuma gyara kuskure idan har ya zauna to yafi sabon koyo wahala. Haka kuma idan kaga kalma ta fito da wata ma’anar da bada ita kasanta ba a cikin jimla, to kar ka dauka badaidai bane har sai ka tambaya anyi maka karin bayani.

To wadannan sune mahimman shawarwarin da zan kawo ga duk mai son koyon turanci wadanda idan anbisu Insha-Allah zasu taimaka.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Back to top button