Karatun Turanci

Fassara daga turanci zuwa Hausa

Do you speak English? Kana magana/kana jin turanci?
*Do you study English? Kana karatun turanci?
*Do think it will rain today? Kana tunanin za’a iya yin ruwa yau?
*Do you think it is possible? Kana tunanin zai yiwu kuwa?
*Do you think you will be back by 2:30? Kana tunanin zaka iya dawowa wajan karfe 2:30 kuwa?
*Do you understand? Ka fahimta?
*Do you want me to come and pick you up? Kana son nazo na dauke ka ne? (A abin hawa).
*Do you want come with me? Kanason ka tawo tare da ni?
*Do you want go with me? Kasason/kinason ki/ka tafi tare Dani?

*Does anyone here speak English? Akwai Wanda yake jin turanci anan kuwa?
*Does she like the school? Shin tanason makarantar kuwa?
*Does this road go to market? Shin wannan hanyar ce ta zuwa kasuwa?
*Does she came yesterday? Shin tazo kuwa jiya?

*Don’t do that, kada Kayi haka.
*Don’t worry, kada ka damu.
*Don’t bother me, kada ka Dame Ni
*Don’t come near me, kada kazo kusa Dani.
*Don’t take my phone, kada ki/ka daukar min waya ta.
*Don’t touch my money, kada ka tabamin kudina.

*Every week. Kowane sati.
*Everyday I get up at 5am, kowace Rana ina tashi karfe 6 na safe.
*Everyone knows it, kowa ya santa.
*Everything is ready, komai ya kammala.
*Excuse me, what did you said, Dan ji Mana, me kace ne?
*Excuse me, Dan ji Mana/nace ba.
Expiration date, lokacin lalacewar Abu.

*Fill it up, please, cika shi taf, Dan Allah.
*For how many days, zawan kwanaki nawa?
*From time to time, daga lokaci zuwa lokaci.
*From here to there, daga Nan zuwa can.
*Forget her, manta da ita.

I will pray hard, sanyi addu’a sosai..

I will work hard,, zanyi aiki tukuru..

I will study hard, zanyi karatu sosai..

I will make a pilgrimage this year,, zanyi aikin hajji wannan shekarar..

I will pay for you,, zan biya ma kudin..

I will make you proud,, zan Sanya ka alfahari..

I will make you happy,, zan Sanya ka farin ciki..

I will complain to him about the problem,, zan masa korafi a kan matsalar..

I will find a solution,, zan samu mafita..

I will accompany you,, zan raka ka..

I will go and visit the patient,, zan je na ziyarci mara lafiyar..

I will deliver the message,, zan isar da sakon..

I will extend your greetings to him,, zan isar da gaisuwarka gare shi..

I will stop here,, zan tsaya a Nan..

 

Let me tell you the truth,, Bari na fada maka gaskiya..

Let me show the visitors in,, Bari na shigo da bakin ciki..

Let me go and do the washing-up bari na je nayi wanke-wanke..

Let me go and do the cooking,, bari naje nayi girki..

Let me go and do the ironing,, bari naje nayi guga..

Let me go and do the washing,, bari naje nayi wanki..

Let me contact them,, bari na tuntube su..

Let me discuss with you,, bari na tattauna da Kai..

Let me go and apologize to him,, bari naje na nemi gafararsa..

 

Stop blaming me,, daina zargi na..

Stop laughing at me,, daina yimin dariya..

Stop flattering me,, daina kwarzanta Ni..

Stop telling lies,, daina fadin karya..

Stop insulting me,, daina zagina..

Stop talking rubbish,, daina maganar banza..

 

Keep learning,, ci gaba da koyo

Keep trying,, ci gaba da kokari..

Keep moving,, ci gaba da tafiya..

Keep practicing,, ci gaba da gwadawa..

 

Don’t interrupt me,, kar ka katseni..

Don’t rely on me,, kar ka dogara da Ni..

Don’t insult me,, kar ka zage Ni..

Don’t deceive me,, kar ka yaudare Ni..

Don’t be rude to me,, kar ka Yi min rashin kunya..

Don’t approach him now,, kar ka tunkare shi yanzu..

Don’t make me angry,, kar ka fusata Ni..

Don’t be angry with me,, kar ka yi fushi da Ni..

Don’t be afraid of speaking English, karka ji tsoron yin turanci

 

TURANCI DA HAUSA

I want to buy something for you, ina so na siya maka wani wani.
*I want to give you a gift, ina so na baka kwaita.
*I want to show you something, inason na nuna maka wani abu.
*I was about to leave the restaurant when my friends arrived, na kusa na bar gidan cin abincin a yayin da abokai na suka shigo.
*I was going to library, naje dakin karatu ne.
*I went to the supermarket, nace shagon siyayya ne.
*I wish I had one, naso ace ina da wani.
*If you like it I can buy more, idan kina son ta zan iya siyo wasu.
*If you need my help, please let me know, idan kina bukatar taimako na, dan Allah ki sanar Dani

*I’ll call back later, zan kirawo daga baya.
*I’ll call you on Friday, zan kira ka ranar juma’a.
*I’ll call you when I leave, zan Kira ka yayin dana tafi.
*I’ll come back later, zan dawo nan gaba.
*I’ll give you a call, zan kira ka.
*I’ll pay for dinner, zan biya kudin abincin daren.
*I’ll pay for the ticket, zan biya kudin tikitin.
*I’ll pay, Zan biya.
*I’ll take it, zan dauke ta.
*I’ll take that one also, zan dauki wancan ma Kuma.
*I’ll take you to the bus stop, zan Kai ka zuwa wajan Hawa mota.
*I’ll talk to you soon, zanyi magana da Kai Nan bada jimawa ba.
*I’ll tell him you called, Zan fada masa ka kira.
*~ill teach you, zan koya muku.
(I’ll = I will)

*I’m 26 years old, Ni dan shekara 26 ne.
*I’m 32, ina da shekara 32
*I’m 61, Ina da shekara 61.
*I’m a beginner, ni Dan koyo ne.
*I’m a teacher, Ni malami ne.
*I’m a student, Ni dalibi ne.
*I’m Nigerian, ni Dan Nigeria ne.
*I’m cleaning my room, ina goge daki na ne.
*I’m Cold, ina da mura.
*I’m coming right now, ina zuwa yanzu haka.
*I’m coming to pick you up, zanzo na dauke ki yanzu haka (a abin Hawa).
*I’m fine, and you? Ina lafiya kefa.
*I’m from kano and you, Ni Dan kano ne kefa/kaifa?
*I’m full, na koshi.
*I’m getting ready to go out, na shirya fita waje.
*I’m going to kano next week, zanje kano wani satin.
*I’m going to bed, Zan je na kwanta.
*I’m going to have a dinner, zanje naci abincin dare.
*I’m good, ina lafiya.
*I’m happy, ina farin ciki.
*I’m hungry, Ina jin yinwu.
*I’m just looking, kawai Ina nema ne.
*I’m lost, nayi asara/nayi Rashi.
*I’m married, ina da aure.
*I’m not afraid, bana jin tsoro.
*I’m not married, bana da aure.
*I’m not going, bazan tafi ba.

*I’m leaving now, zan tafi yanzu.

Who are you? Waye kai?
Who are you looking for? Wa kake nema?
Who are they, su waye su?
Who is it? Waye ita?
Who is that? Waye wancan?
Who sent this letter? Waye ya turo da wannan wasiƙar?
Who taught you that? Waye ya koya maka haka?
Who taught you? Waye ya koya maka?
Who was your teacher? Waye ya kasance malamin ka?
Who won? Waye yayi nasara?
Who would you like to speak to? Da waye ka ke son kayi magana?
Who’s calling? Waye yake kira?
Who’s that man over there? Waye wancan mutumin da yake tsaye a can?
Whose book is that? Littafin waye wancan?

Why are you laughing? Meyasa kake dariya?
Why aren’t you going? Meyasa baka tafi ba?
Why did you do that? Meyasa kayi haka?
Why did you say that? Meyasa kace Haka?
Why not? Meyasa ba haka ba?

Will you call me a keke napep Please? Zaka iya kirawo min adaidaita sahu dan Allah.
Will you hand me a towel please? Zaka iya muƙomin tawul dan Allah?
Will you put this in the car for me? Zaka iya saka min wannan a cikin mota?
Will you remind me? Zaka tunamin?
Will you take me home? Zaka kaini gida?

Would you ask him to call me back please? Zaka iya tambayarsa ya kira Ni daga baya dan Allah?
Would you ask him to come here? Zaka iya tambayarsa yazo nan?

*where have you been long time,
Ina ka shiga ne kwana biyu.

*he helped us to do this assignment,
Ya temakemu wajan yin wannan aikin

*She will see them tomorrow,
Zata gansu gobe.
*you broke that window, I saw you,
Kai ka karya waccan tagar na ganka.
*I asked her to come and see me,
Na tambayeta tazo ta ganni.
*we couldn’t do the assignment until the teacher told us how to do it,
Bazamu iya yin aikin ba harse malamin ya fada mana yaya zamuyi shi.
*they played us at football and we beat them,
Sunyi wasan kwallon kafa damu kuma mun ci su.

I taught you, na koyar da kai.
He saw me, ya ganni.
We knows us, mun san su.
We know her, mun san ta.
She thanked me, tagode min.
He threw it, ya jefar da ita.
He broke the window, ya karya taga.
They blamed him, sun zarge shi
Why did you go there, meyasa kaje can?.

*her kindness is beyond compare,
Kirkinta ya wuce a kwatanta
*I feel bit under the weather,
Bana jin dadin jikina
*we might live to see the day,
Allah ya nuna mana ranar.
*I’m sick of your behaviour.
Halayyarka tana damuna.
*I meet her gaze, mun hadu ido da ido
*I was taken unawares, an shammace ni.
*I will keep a close eye on him,
Zan sa ido sosai a kansa.
*I’m no Match for you at football,
Ni ba sa’anka bane a kwallon kafa.
*She gave me the money on her own accord,
Ta ba ni kudin don ra’ayin kanta.
*Sit down and make yourself at home,
Zauna ka saki jikin ka.
*I will part company with aminu,
Zan daina mu’ala mula da aminu.

*Identify yourself, yi bayanin kanka.
*Can I borrow your phone, zan iya aran wayarka?
*why you do you come late,?
Meyasa kazo a makare.
*what do you expect? Me kake tammani.
*she request me to help her,
Ta roke ni na taimake ta.
*She followed my instruction,
Tabi umar ni na.
*She disgrace him, ta wulakanta shi.
She asked me for money,
Ta roke ni kudi.

I can’t hear you,, bana iya jinka.
I don’t feel well,, baba jin dadi.
I don’t have a girlfriend,, bani da budurwa.
I don’t have any money,, bani da ko sisi.
I don’t have enough money,, bani da ishashshen kudi.
I don’t know,, ban sani ba.
I don’t like him,, bana kaunar sa.

I still have a lot of things to buy,, har yanzu ina da abubuwan siya da yawa.
I want brush my teeth and take a bath,, ina so nayi burosh din hakorana sannan kuma nayi wanka.
I still haven’t decided,, har yanzu ban yanke shawara ba.
I think I need to see a doctor,, ina tunanin ina bukatar ganin likita.
I think so,, ina tunanin haka.
I think those shoes are very good looking,, ina tunanin wayan nan takalman suna da matukar kyan gani.
I think you have too many clothes,, ina tunanin kana da kaya masu yawa. (Kayan sawa)
I thought the clothes were cheaper,, na dauka kayan sun kasan ce masu sauki.
I trust you,, na aminta da kai.

I need to change clothes,, ina bukatar canza kaya.
I need to go home,, ina bukatar tafiya gida.
I need to go now,, Ina bukatar tafiya yanzu.

I only have 500 naira,, naira dari biyar ce kawai dani.
I speak three language,, ina ji/magana da yare uku.

I’m coming to pick you up,, ina nan zuwa na dauke ka (a abin hawa).
I’m fine and you,, ina lafiya kaifa?
I’m full/I’m full up,, na koshi.
I’m getting Ready to go out,, ina yin shirin fita waje.
I’m from kano,, ni dan kano ne/daga kano nake.
I’m going to bed,, zan tafi na kwanta.

She wants to know when you are coming,, tana so ta sani yaushe kake zuwa.
She is going with me tomorrow,, zata tafi tare dani gobe.
She is older than me,, ta girme ni.
She’s pretty,, kyakykyawa ce ita.
Should I wait? Ya kamata najira kuwa?

Everything went according to plan,, Komai ya tafi Kamar yadda aka tsara.
She will pass the exam in all likelihood,, zataci jarrabawar bisa ga dukkan alamu. He can’t barely write his name,, da kyar zai iya rubuta sunan sa.
Don’t you dare come out in the rain,, kar ka kuskura ka fito a cikin ruwa….

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button