Verb

Menene ma’anar regular verb? (Aikatau mai bin tsari)

Kalmomin regular verbs

A wannan darasin zamu yi shine akan yanda ake samar da past tense ko past participle na regular verbs

Menene regular verbs?

Regular verbs sune jerin wasu kalmomin Verbs da ake samar da Past Tense dinsu ko kuma past participle nasu ta hanyar sanya haruffan “d, ied, ko kum ed” a karshen su

Hanyoyin da ake samar da regular verbs

1. Ana kara haruffan “ed” a karshen kalmar Aiki (verb) domin samar da past tense nasu. Bugu da kari, Idan kalmar aiki (verb) ta kare da harafin “e”, kawai zamu karawa kalmar “d” ne domin ta zama past tense. gamisali:

  • Bake – yana nufin “gasa abinci”
  • Baked – an riga an gasa abincin
  • Work – yana nufin “Aiki”
  • Worked – an riga anyi aikin

ALSO READ: Bambanci tsakanin It’s da kuma Its a cikin karatun turanci


2. Idan kalmar aiki (verb) ta kare da harafin “y”, to zamu canza harafin y din, sai mu sanya harafin “i”, sannan kuma sai mu sanya haruffan “ed” a karshen kalmar. misali:

  • Dry – yana nufin “bushe”
  • Dried – wanda ya riga ya bushe
  • Apply – yana nufin “yin amfani da abu”
  • Applied – abinda akayi amfani dashi

3. Idan kuma kalmar aiki (verb) wasali ne ya zo a bayan “y” din, kawai zamu kara haraffan “ed” ne, ba tare da mun cire harafin y din ba. Misali:

  • Destroy – yana nufin “lalata”
  • Destroyed – An lalata
  • Play – yana nufin “wasa”
  • Played – anyi wasa

Idan kuka lura da wadannan kalmomin dake sama zakuga wasali ne yazo kafin harafin “y” shiyasa ba’a canza y din ba gurin samar da past tense nasu

4. Idan kalmar aiki yazo da ga6a daya (one syllable), kawai zaka sanyawa kalmar irin harafin da take dauke dashi, su zama guda biyu, sannan sai ka sanya haruffan “ed” a karshe. Misali:

  • Ban – yana nufin “hana”
  • Banned – An hana
  • Trap – yana nufin “tarko”
  • Trapped – abinda aka samu sa’an shi

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci


5. Idan kuma kalmar aikatau yana da ga6o6i guda biyu (two syllables), to shima zamu sanyawa mishi irin harafin da yazo dashi na karshe su zama guda biyu (double consonants) tare da sanya haruffan “ed” a karshe. Misali:

  • Permit – yarda ko amince
  • Permitted – an yarda
  • compel – Tilasta
  • Compelled – an tilasta

Jerin Kalmomin regular verb tare da fassarar su a harshen hausa

Words Regular verbs
Accept – yarda Accepted – an yarda
Accuse – zargi Accused – wanda ake
Zargi
Achieve – Samu Achieved – An samu
Act – aiki Acted – anyi aikin
Add – kara Added – an kara
Admire – martaba Admired – an martaba
Admit – amince Admitted – an amince
Adopt – amsar raining
Yara
Adopted – mutumin da aka
Raine shi
Affect – ta6a Affected – an ta6a
Advise – Shawara Advised – anyi shawara
Agree – amince ko
Yarda
Agreed – an amince
Allow – bari Allowed – an bari
Announce – sanar Announced – an sanar
Appreciate – yabawa Appreciated – an yaba
Approve – amince Approved – an amince
Argue – yin gardama Argued – Anyi gardama
Arrive – iso Arrived – an iso
Ask – tambaya Asked – an tambaya
Assist – taimaka Assisted – an taimaka
Attack – farmaki Attacked – an Kai farmaki
Attempt – yinquri Attempted – anyi yunquri
Attend – halarta Attended – an halarta
Avoid – gujewa Avoided – an guje
Back – komawa baya Backed – an koma
Baya
Bake – gasa abinci Baked – an gasa abincin
Banish – kora Banished – an kora
Decide – yanke shawara Decided – an yanke shawara
Deliver – isar Delivered – an isar
Demand – bukata Demanded – an bukata
Design – tsara Designed – Wanda aka
Tsara
Destroy – lalata Destroyed – lalatacce
Develop – bunqasa Developed – Wanda ya bunqasa
Die – mutuwa Died – matacce
Disappoint – 6atawa wani
Rai
Disappointed – idan ran mutum
Ya 6aci
Discover – gano Discovered – an gano
Discuss – tattauna Discussed – an tattauna
Disregard – halin ko in kula Disregarded – Wanda ba’a damu
Dashi ba
Disturb – takura Disturbed – takurarre
Divide – raba Divided – Wanda aka raba
Drag – ja Dragged – Wanda aka ja
Dress – sanya tufafi Dressed – Wanda ya sanya
Tufafi
Dry – bushe Dried – Busashshe
Dunk – tsoma Dunked – an tsoma
Eliminate – kauda Abu
A doron kasa
Eliminated – wanda aka kashe
Earn – samu riba Earned – ribar da
Aka samu
Emigrate – yin hijira Emigrated – anyi hijira
Employ – daukar wani
Aiki
Employed – Wanda aka
Dauka aiki
Encourage – karfafa gwiwa Encouraged – an karfafa gwiwa
End – karke Ended – na karke
Enjoy – more Enjoyed – an more
Escape – ku6uta Escaped – ku6utacce
Beg – roqa Begged – an roqa
Behave – nuna halayya Behaved – Mai hali
Believe – imani Believed – Mai imani
Belittle – nuna cewa
Abu bashi da muhimmanci
Belittled – abinda aka nuna bashi da
Muhimmanci
Blame – daurawa wani
Alhakin faruwar kuskure
Blamed – Wanda aka dora masa
Alhakin faruwar kuskure
Boil – tafasa Boiled – tafasashshe
Borrow – aro Borrowed – an ara
Bother – damu Wanda aka dameshi
Bound – tsalle Bounded – wanda yayi tsalle
Brake – taka birki Braked – an taka birki
Bury – burne Burried – an burne
Call – kira Called – an kira
Carry – dauka Carried – an dauka
Cause – sanadi Caused – Wanda yayi sanadi
Celebrate – yin shagali Celebrated – Wanda ake
Matukar girmamawa
Change – canji Changed – an canja
Chase – guje-guje Chased – Anyi guje-guje
Chat – hira Chatted – anyi hira
Cheat – cuta Cheated – anyi cuta
Check – bincika Checked – an bincika
Chew – tauna Chewed – an tauna
Clap – tafa Clapped – an tafa
Clean – tsafta Cleaned – tsafta tacce
Clear – sarai Cleared – Wanda yake sarai
Climb – hawa Climbed – an hau
Close – rufe Closed – an rufe
Coax – lallashi Coaxed – anyi lallashi
Collect – tattara Collected – an tattara
Compare – kwatanta Compared – an kwatanta
Compete – yin takura Competed – an takura
Complain – korafi Complained – anyi korafi
Concoct – girka abinci da
Kayan abinci iri iri
Concocted – abincin da aka girka
Da kayan abinci iri iri
Confess – amsa laifi Confessed – an amsa laifi
Construct – gina abubuwa Constructed – abubuwan da
Aka gina
Contact – tuntu6a Contacted – an tuntu6a
Cook – dafa Cooked – an dafa
Copy – kwaikwaya Copied – an kwaikwaya
Cough – tari Coughed – anyi tari
Count – irga Counted – an irga
Crash – yin hatsari Crashed – anyi hatsari
Create – kirikira Created – kirkirarre
Cry – kuka Cried – anyi kuka
Curse – zagi Cursed – an zagi
Damage – ta’adi Damaged – an lalata
Dance – rawa Danced – anyi rawa
Estimate – kiyasta Estimated – an kiyasta
Expand – fadada Expanded – an fadada
Explain – yi bayani Explained – anyi bayani
Fish – kamo kifi Fished – an Kama kifi
Fix – gyara Fixed – an gyara
Flush – daure fuska Flushed – an daure fuska
Follow – bi Followed – an bi
Force – karfi Forced – karfaffa
Fry – soya Fried – soyayye
Gather – tattara Gathered – tatta rarre
Grab – damqe Grabbed – an damqe
Greet – gaisa Greeted – an gaisa
Guess – cinka Guessed – an cinka
Happen – faru/auku Happened – wanda ya faru
Harass – takura Harassed – an takura
Harm – illata Harmed – an illata
Hate – tsana Hated – wanda aka tsana
Heal – warkar Healed – an warkar
Help – taimako Helped – an taimaka
Hesitate – yin shakku Hesitated – wanda akayi
kokwanto
Hope – tsammani Hoped – abinda akayi
tsammani
Hunt – farauta Hunted – abinda akayi
farautar sa
Hurry – yi sauri Hurried – anyi sauri
Identify – bayyanar da
mutum
Identified – an bayyanar
da mutum
Imagine – tunani Imagined – anyi tunani
Include – kunsa Included – abubuwanda
ya kunsa
Insist – nacewa Insisted – an nace
Intend – kudurta Intended – abinda aka
kudurta
Interest – sha’awa Interested – abinda kake
so
Interrupt – katse hanzari Interrupted – an katse hanzari
Introduce – gabatar Introduced – an gabatar
Invent – kirkiro Invented – an kirkiro
Investigate – bincika Investigated – an bincika
Initate – fusata Initated – an fusa ta
Join – hade Joined – an hade
Jump – tsalle Jumped – anyi tsalle
Kick – buga abu da
kafa
Kicked – an buga abu
da kafa
Kill – kashewa Killed – an kashe
Knock – kwankwasawa Knocked – an kwankwasa
Kiss – sumbata Kissed – anyi sumbata
Laugh – dariya Laughed – anyi dariya
Learn – koyo Learned – an koya
Lie – karya Lied – anyi karya
Lift – daga Lifted – an daga
Link – hada Linked – an hada
List – jera abubuwa Listed – an jera abubuwa
Listen – sauraro Listened – an saurara
Live – rayu Lived -an rayu
Locate – sanya abu
a wani guri
Located – gurin da
abu yake
Lock – kulle Locked – an kulle
Love – kauna Loved – abin so
Measure – gwadawa Measured – an gwada
Murder – yin kisan
kai
Murdered – anyi kisan
kai
Mix – gauraya Mixed – an gauraya
Move – matsa Moved – an matsa
Note – rubutu Noted – rubutacce
Notice – lura Noticed – an lura
Obey – biyayya Obeyed – anyi biyayya
Offer – samar Offered – an samar
Open – bude Opened – budadde
Paint – fenti Painted – anyi fenti
park – pakin na abun
hawa
Parked – gurin da akayi
pakin na abin hawa
Pick – zabq Picked – an zaba
Phone – waya Phoned – anyi waya
Place – sanya abu
a wani guri
Placed – idan an sanya abu
a wani guri
Play – wasa Played – anyi wasa
Please – gamsar Pleased – an gamsu
Pluck – tsifa Plucked – an tsefe
Praise – yaba Praised – an yaba
Pray – addu’a Prayed – anyi addu’a
Prefer – son wani abu
fiye da wani
Prefered – abinda aka soshi
fiye da wani
Print – buga rubutu Printed – rubutun da
aka buga
Promise – alkawari Promised – alkawarin da akayi
Pull – janyo Pulled – an janyo
Punch – naushi Punched – idan akayi
naushi
Punish – hukuntar Punished – an hukunta
Purchase – siyayya Purchased – siyayyan da
akayi
Question – tambaya Questioned – an tambaya
Race – yin gasa Raced – anyi gasa
Rain – ruwan sama Rained – anyi ruwan
sama
Reduce – ragi Reduced – anyi ragi
Reply – mayar da
martani
Replied – an mayar
da martani
Request – Roko Requested – an roka
Retire – dena aiki saboda
tsufa
Retired – wanda ya dena
aiki saboda tsufa
Return – dawo Returned – an dawo
Scare – tsoratar Scared – an tsorata
Select – zabi Selected – zababbe
Share – raba abu
ga wasu
Shared – abinda aka
raba ga wasu
Shop – siyayya a
shago
Shopped – abinda aka
siya a shago
Sign – sa hannu Signed – an sa hannu
Slap – mari Slapped – anyi mari
Succeed – samun nasara Succeeded – an samu
nasara
Suggest – hasashe Suggested – abinda akayi
hasashen sa
Talk – magana Talked – anyi magana
Thank – gode Thanked – an gode
Touch – ta6a Touched – an ta6a
Try – kokarta Tried – an kokarta
Turn – juya Turned – an juya
Twist – murza Twisted – an murza
Type – rubuta Typed – an rubuta
Use – amfani Used – mai amfani(past tense)
Vary – Bambanta Varied – wanda ya bambanta
Vote – zabe Voted – zababbe
Wait – jira Waited – an jira
Walk – tafiya Walked – anyi tafiya
Want – bukata Wanted – wanda aka
bukata
Warn – gargadi Warned – wanda akayi
gargadi
Wash – wanke Washed – wankakke
Wish – bukata Wished – wanda aka
bukata
Work – yin aiki Worked – anyi aikin
Worry – damu Worried – an damu

ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU


Wadannan wasu ne daga cikin kalmomin Regular verbs, amma kalmomin regular verb suna da yawa sosai,

Idan da akwai wani abu da baka gane ba a cikin wannan darasin kofa a bude take gurin yin mana tamba, domin yin maga tamaya saika duba comment section dake kasan wannan posting din, mukuma insha Allahu zamu yi kokarin baka amsarka alokacin daya dace

Mene ne regular verb a turanci?
Menene regular verb?

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Leave a Reply

Back to top button