EnglishKaratun TuranciLearn

Menene Possessive Case a cikin karatun turanci?

 

In my lesson today, I am going to talk on “Possessive Case”
A darasi na na yau, zanyi magana ne akan yadda ake bayyana mallaka.

{Possessive Case}
Itace kalmar da zanyi bayani akanta. Amma kafin nazo kanta bari nayi ƙarin haske daga inda kalmar ta taso. “Possessive”tazo ne daga-
(Possess) ko (Possession)

Possess-
Tana nufin mallaka.
Misali-
All what he possessed has been seized.
Dukkan abinda ya mallaka an ƙwace.

The flood destroyed everything he possessed.
Ambaliyar ruwan ta ɓata duk abinda ya mallaka.

Sai kuma-
Possession-
Tana nufin mallakar..
Misali-
This house is in her possession.
Wannan gidan mallakar ta ne.

He was found in possession of stolen phone.
An same shi da mallakar wayar da aka sato.

Can you fully explain on how this phone came into your possession?
Zaka iya cikakken bayani ta yadda wannan wayar tazama mallakar ka?

Haka kuma akwai (Possessive)
Possessive-
Tana nufin sonkai, ko haɗama.
Misali-
This child is too Possessive.
Wannan yaron yanada haɗama, ko sonkai.
(Anan ana nufin duk abinda yaron ya ɗauka baya bari wani yaron ya ɗauka. Zai ƙanƙame kome awurinsa)

You are too Possessive.
Ka cika son kanfa.

To yanzu mun iso kan kalmar da zamuyi magana akanta, itace-

(Possessive Case)
Wannan a nahawun turanci, (English grammar) tana nuna hanyar da ake nuna mallakar abu.
Misali-
Akwai hanya biyu da ake nuna mallakar abu da turanci.
Misali idan zance-
Wannan gidan na Khadijah ne.
Da turanci zance-
This is the house of Khadija.
To ammafa duk da za agane abinda ake nufi, to a “English grammar” wannan ba daidai bane.
Ga yadda za ace-
This is Khadijah’s house.

Duk lokacin da za a nuna mallaka to za ayi ƙyatile ne (‘)tare da harafin (s) atsakanin suna da abinda aka mallaka. Kamar haka-

Ahmad’s car – motar Ahmad.
Usman’s house — gidan Usman.
Hafsat’s husband =mijin Hafsat
Jameelah’s son – ɗan Jameelah

Ga ƙarin misalai.

Book of boy ×
Littafi na yaro ×
Boy’s book ✓
Littafin yaro ✓

This is the phone of Ahmad ×
Wannan waya ta Ahmad ×
This is Ahmad’s phone ✓
Wannan wayar Ahmad ce ✓

That is the room of Maryam ×
Wacan ɗakin Maryam ×
That is Maryam’s room ✓
Wancan ɗakun Maryam ne ✓

Amma ida masu mallakar dayawa ne, to ana ƙara harafin (s) akan sunan. Amma idan akayi ƙarin (s)akan sunan to basai anƙara wata (s) ɗin ba. Saidai asa (apostrophe) wato alamar ƙyatile (‘) sai kuma abinda aka mallakar.
Misali
Boys’ house
Gidan yara
Girls’ mother.
Uwar yara mata
Teachers’ office.
Ofishin Malamai

Amma idan ba (s)ake ƙarawa ba awajen jam’in suna, to shima anayin sa ne kamar na abu ɗaya. Kodayake irin waɗannan kalmomin basu da yawa a turanci.
Misali-
Men’s house
Gidan mazaje
Women’s school.
Makarantar mata.
Children’s mother
Uwar yara.
Anayin hakane tareda jam’in sunan da harafi ne ake canzawa ba (s) ake ƙarawa ba.

Zanso na ƙara gaba, to amma saboda ku samu sauƙin karatun zan tsaya anan sai mun haɗu a darasi na gaba.
Da fatan dogon rubutun bazai ƙosar daku ba.
Nagode.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button