KalmomiKaratun TuranciWords

What is the difference between come, coming, and came? (Hausa)

Darasinmu na yau shine zai bambance maka ban-bancin wadannan Kalmomin na “Come” da kuma “Came”

Sannan kuma zamuyi bayani akan yanda ake amfani da wadannan Kalmomin a cikin Jimla, Wanda da yawan Dalibai suna samun kura-kurai wajen amfani dasu

Come and coming 

Ana iya amfani dasu ne a lokacin da ake aikata Aikin ko kuma anaso a aikata ko kuma an bada umarni a aikata 

Come

Kalmar “Come” tana aiki biyu, zaka iya amfani da “come” ne lokacin da ake bada umarni ko kuma za’a aikata Aikin ba’a riga an aikata ba 

Misali:

i. Come here – zo nan/ kazo nan / kizo nan 

Dukkaninsu umarni ne 

ii. Come and give me spoon – Zo ka bani cokali. 

iii. Come let go – Zo mu tafi 

iv. Come and seat here – Zo ka zauna a nan. 

Haka zalika zaka iya amfani da Kalmar “come” Idan zaka aikata Aikin da ba’a riga an aikata ba. 

Misali:

i. I will Come to your house tomorrow – Zan zo gidanku gobe 

ii. She will come next week – Zata zo sati mai zuwa. 

Sannan kuma ana karawa “come” “ing” domin nuna cewa anayin aiki yanzu-yanzu 

Coming 

ana iya amfani da “coming” a lokacin da ake aikata Aikin (present continuous tense) 

Misali :

I am coming to your house now – gani nan ina zuwa gidanku yanzu. 

Came 

Shikuma Kalmar “Came” anayin amfani dashine idan har an riga an gama aikata Aikin to za’ayi amfani da “came” ne. 

Misali:

i. He came here this morning – yazo nan da safen nan 

ii. I came to visit you – Nazone domin na ziyarceka. 

iii. She came here to investigate – Tazo nan ne domin tayi bincike. 

iv. I came early today – Nazo da wuri yau. 

Wasu kura-kurai da Dalibai ke aikatawa har ‘yan Secondary school. 

Idan umarni zaka bada Bazakayi amfani da “Came” ba, sai dai “Come”

Misali:

Bazakace “Came here” ba (yin haka kuskure ne), sai dai kace “Come here – Zo nan”

Idan kuma an riga an aikata Aikin, Bazakayi amfani da “come” ba, sai dai “Came”

Misali:

Bazakace “I come to greet you” (yin haka kuskure ne), sai dai kace “I came to great you – Nazo ne domin na gaida ka”

Haka zalika Bazakace  “I come late today” ba sai dai kace “I came late today – Nazo a makare yau/Nazo latti yau” ko kuma kace “I came early today – Nazo da wuri yau”

Zan dakata anan, sai kuma a darasi na gaba idan Allah ya sake hadamu zamu cigaba, idan kanada tambaya ko neman Karin bayani sai kayi mana comment a kasan Wannan posting din

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button