KalmomiKaratun Turanci

Bambanci tsakanin Sometime, Some time, da kuma Sometimes a turanci

Yadda zakayi amfani da sometime, da some time da kuma sometimes a cikin karatun turanci

Barka da sake shiguwa cikin wannan shafin mai albarka, Mutane da dama sukan dauka wadannan kalmomin na sometime, some time, da kuma Sometimes duk iri daya ne, sai dai kuma akwai bambanci, bambancin kuwa shine kamar haka:

ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU


SOMETIME: Da hausa, wannan kalmar tana nifin (“Wani lokaci”) Amma ‘wani lokacin’ dazezo kokuma yawuce. Atakaice dai bawai wani takaitaccen lokaci bane.

Example;
Everything will be okay sometime.
Komai ze daidaita wani lokaci.

She should inform him sometime later.
Ya kamata ta sanar da shi wani lokaci nan gaba.

Study hard friends, sometime you won’t have chance to.
Kuyi karatu tuƙuru abokai, wani lokaci baza ku samu dama ba.

ALSO READ: Bambanci tsakanin It’s da kuma Its a cikin karatun turanci


SOME TIMES: Wannan kuma a hausance yana nifin (“Wani dan lokaci”)

Examples;.

They commanded us to wait for some time.
Sun umarce mu da mu jira na ɗan wani lokaci.

It took me some time to draw a human skeleton.
Ya ɗauken wani ɗan lokaci dan zana ƙwarangwal ɗin mutum.

She spoke to him for some time before she left the house.
Ta yi magana da shi na ɗan wani lokaci kafun ta bar gidan.

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci


SOMETIMES: Wannan kalmarma tananifin (“wani lokacin”) kunga kenan a wannan fagen lokaci bayan lokacine bawai lokaci gudaba

Examples ;

Sometimes they visit us once a week.
Wani lokacin suna ziyartar mu sauɗaya a sati.

Sometimes I drive the car myself.
Wani lokacin Ina tuƙa motar da kaina.

She sometimes does’t want to speak.
Bata son yin magana wani lokacin

Bambanci tsakanin Sometime, Some time, da kuma sometimes
Sometime, Some time, da kuma sometimes in Hausa

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button