Kalmomi

Kalmar WEAR ma’anarta da kuma yadda ake aiki da ita

Kalmar WEAR ma’anarta da kuma yadda ake aiki da ita

Barka da warhaka, fatan kuna jin dadin kasancewa da wannan shafin namu na karatun turanci, a cikin wannan darasin zamuyi bayani ne akan kalmar turanci guda daya kawai wato “Wear”

Kalmar WEAR na nufin sanya kaya ko sanya sutura. Kaman sanya hula, tabarau, takalma, wando, hijabi, takunkumin fuska, safar hannu da dai sauran. Ga misalan wannan kalma na tafe.

    1. Aikin da za a yi nan gaba:

      I shall wear hand gloves.
      Zan sanya safar hannu.

The bride will wear her wedding dress after their marriage.
Amaryar za ta sanya kayan amarenta bayan aurensu.

Wedding dress shine kaya ko sutura da aka siyo ko ɗinka domin mata amare su sanya a ranar aurensu.

    1. Aiki sabau ko wanda ke faruwa a maimace

      I usually wear sandals.
      Na kan sanya sandal.

      She often wears hijabs.
      Ta kan yawaita sanya hijabi.

 

  1. Aikin da aka yi a wani lokaci da ya wuce a baya:

    We wore Rolex wristwatch.
    Mun sanya agogon hannu na kamfanin Rolex.

    They wore hats at the college.
    Sun sanya malafa a kwalejin.

Ga wasu hanyoyi da ake aiki da WEAR:

  • wear a cap – sanya hula
  • wear a face mask – sa takunkumi
  • wear a t-shirt – sa rigar tishat
  • wear a wristwatch – sa agogon hannu
  • wear clothes – sanya sutura
  • wear dress – sanya sutura
  • wear glasses – sanya tabarau
  • wear hand gloves – sa safar hannu
  • wear hijab – sanya hijabi
  • wear jeans – sanya wandon jins
  • wear shoes – sanya takalma
  • wear socks – sanya safa
  • wear trousers – sanya wando
  • wear veil – sanya niƙabi

Misali:

Amina wears veil when she goes to school.
Amina kan sanya niƙabi idan ta je makaranta.

I will wear new T-shirt.
Zan sanya sabuwar rigar tishat.

The guys wore jeans at the party.
Matasan sun sanya wandunan jins a taron.

Abin lura anan shine: Past tense na kalmar “wear” shine “wore”.

Ku na iya kawo naku misalan tare da kalmar wear. Haka kuma ka da dai a manta ayi subscribe na channel ɗin mu mai suna Nura Mahadi dake YouTube domin koyan turanci a sauƙaƙe.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button