HANYOYI (3) DA SUKE HANA MUTUM YA IYA TURANCI DA WURI
HANYOYI (3) DA SUKE HANA MUTUM YA IYA TURANCI DA WURI
Harshen Turanci (English language) ya zama yaren da Duniya ta Amince dashi kuma ake mu’amala dashi a kowacce kasa da ke kowacce Nahiya daga cikin Nahiyoyin Duniya guda 7, a yayin da a halin yanzu sama da Mutane Biliyan 1 da Miliyan 35 su ke magana da Yaren na Ingilishi a fadin Duniya, Sai dai duk da irin wannan daukaka da Yaren na turanci ya samu da kuma kasancewarsa yaren da Hukumomi ke mu’amulantar Al’umma da shi a Kasar nan, har ya zuwa yanzu kaso mafi yawa daga cikin Al’ummar da ke yankin mu na Arewacin Najeriya basa iya magana da Yaren na Turanci duk kuwa da irin muhimmanci da tumbatsa tare da kimar da Yaren ke da shi a Idon Duniya,
ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU
Ban taba gani ko jin yare mai sauki kamar turanci ba. wadannan sune hanyoyi guda uku da suke sa mutane suke kasa yin magana da turanci
(1) TSORO: dole sai ka cire tsoron gyara. Idan kana jin tsoro ace kayi Kuskure ko baka iya ba to fa baza ka taba iyawa ba. Wanda ya koya maka shine malaminka, amma babban malaminka shine wanda ya gyara kuskurenka.
(2) KUNYA: Sau da yawa mutane ba wai basu iya turanci bane kawai dai suna jin kunya ne saboda basu saba ba ko kuma sun raina kadan daga abinda suka sani.
ALSO READ: Menene Internet slang words da kuma yanda ake amfani dashi a social media (Yaren chatting)
Menene homophones a turanci?
Kalmomi masu alaka da sassan jikin mutum a turanci da hausa
(3) KIN TURANCIN: Dole sai ka so abu kafin ka iya shi. Babu wanda ya koyawa kowa cin abinci saboda abu ne wanda rashin cinshi na da hukunci yayinda babu mai koyar dashi. Dan haka kamar yadda ka koyi yin amfani da waya ba wai dan tana waya ba sai dan kana son yin amfani da ita; haka muka koyi cin abinci saboda muna son ci.
ALSO READ: Menene antonyms a cikin karatun turanci? (Antonyms words)
Me ake nufi da Regular Plural Noun a cikin karatun turanci
Me ake nufi da Noun suffix a cikin karatun turanci?
Dole kana bukatar kaso turanci kamar waya da abinci a wancan misalin, sannan ka daina tsoron yi koda a gaban proffessor ne, kuma ka cire kunyar kar ace baka iya ba. Sai kayi sannan a gyara maka, ba gyara babu iyawa.