EnglishHow to improve your EnglishKaratun Turanci

Yanda ake anfani da Capital letter (Using Capital Letters)

 

 

 
How to use capital letters? 
Assalamualaikum ‘yan uwana Dalibai, yau zamuyi darasine akan Capital letters?. Capital letter yana nufin Babban harafi.

Misali kamar  “A” wannan itace capital letter , idan munaso mu rubuta karamin harafin “A”  shine “a”.

Darasin namu zamuyi  magana ne akan wuraren da akeyin amfani da capital letters.

Proper noun

Yawancin proper noun akan fara rubuta kalmar shine da babban harafi, Saboda proper noun sunaye ne na mutane, gurare (places), Kamfanuka (Companies), Littattafai (Books), Masana’antu, watanni (Months), Yawancin waɗannan sunayen da muka lissafa duka akan rubuta farkon haruffan su ne da Babban harafi (Capital letter). Misali

Names
  • Abdulmaleek
  • Abdullahi
  • Usman
  • Mohidden
  • Ahmad
  • Auwal
  • Khadijah
  • Fatima
  • Maryam
  • Rukayya

Places

  • Kaduna
  • Zaria
  • Bauchi
  • Katsina
  • Kano
  • Adamawa

Companies

  • Facebook
  • Twitter
  • Google
  • Amazon
  • Mercedes

Books

  • In Search of Lost Time
  • One Hundred Years of Solitude
  • To Kill a Mockingbird
  • Harry Potter and the Chamber of Secrets

Movies

  • Captain America
  • Love Actually
  • Baywatch

Months/Days

  • January
  • February
  • March
  • Monday
  • Tuesday
  • Wednesday

Kamar dai yanda kaga mun jero sunayen dake sama wanda dukkan su Proper noun ne da ake fara rubuta su da Capital letter, Sai dai kuma idan kun lura zakuga idan muka haɗa gungun kalmomi guri guda zakuga akan samu wasu kalmomi a cikin su waɗanda ba’a fara rubuta su da Capital letter, Bari muyi misali da sunan wannan littafi na “The Lord of the Rings” zakuga yana da kalmomi guda biyu da ba’a fara rubuta farkon kalmar da Capital letter wato “of” da kuma “the” dalilin da yasaka ake rubuta su da small letters saboda sun zo ne a tsakiya, sannan kuma basu da wani muhimmanci a cikin Tittle din

Ga wasu daga cikin guraren da ake amfani da capital letters.

1. Anayin amfani da Capital letter a kowani farkon Jimla (sentence). Misali:

The boy is eating – yaron yana cin abinci.

A wannan Jimlar “T” itace capital letter.

2. Anayin amfani da capital letter akowani farkon Sunayen mutane. Misali:

Abdulmaleek
Tijjani
Ibrahim
Nafisat
Basma.
Da dai sauransu.

3. Anayin amfani da capital letter idan za’a rubuta sunan ubangiji (wato Allah).

bazaiyiwu kace g “god” ba sai dai “God”
Ko kuma “Lord”
Da dai sauran su.

4. Anayin amfani da capital letter a Haruffan abbreviation. Abbreviation yana nufin kamar takaita doguwar kalma ko Jimla ko sunan wani Abu, kamar sunan kungiya, Ma’aikata, makarantu, da dai sauran su. Misali:

.

A.B.U yana nufin (Ahmadu Bello University)

U.S.A yana nufin (United State of America)

5. Anayin amfani da capital letter a farkon harafin direct speech (direct speech shine maganar da aka kawota kamar yanda mai maganar ya fada ba canza koda harafi). Misali :

I must visit my friend”, Ibrahim said – “Lallai zan ziyarci abokina” Ibrahim yace

She has not paid her school fees”, the teacher said – “Bata biya kudin makaranta ba “, malamin yace

6. Anayin amfani da capital letter a farkon Sunayen littafi Mai tsarki. Misali:

Al-qura’an.
Bible
Da dai sauran su.

7. Anayin amfani da capital letter a kowani farkon Sunayen garuruwa. Misali:

Kaduna
Zaria
Nigeria
da dai sauran su.

8. Anayin amfani da capital letter a farkon Kalmar gaisuwar bude wasika. Misali :

Dear sir
Dear father
Dear Ibrahim.
Da dai sauran su

9. Anayin amfani da capital letter a  harafin kalmar gama wasika. Misali

                   Yours sincerely
                    Yours loving son
da dai sauransu

10. Anayin amfani da capital letter a kowani farkon Sunayen ranaku da watanni. Misali:

Monday
Tuesday
Wednesday
Thursday
Friday
January
February
March
Da dai sauran su

11. Anayin amfani da capital letter a Tittle/heading na rubuta wasikar formal letter. Wato a Formal letter Kafin ka fara rubuta wasikar, sai ka fara fadin abinda yasa zaka rubuta wasikar. To akan rubutane da capital letter, wani lokaci kuma akan ja masa layi akasanshi. Misali :

APPLICATION FOR EMPLOYMENT AS A SCHOOL TEACHER.

12. Anayin amfani da capital letter a farkon harafin Kalmomin proper nouns (proper noun shine Sunayen kebabbun abubuwa na musamman na mutane da gurare, kamar garuruwa, kasashe wanda ko yaushe yake farawa da babban harafi). Misali:.

Zaria
Kaduna
Nigeria
Africa
Khadija
Da dai sauran su.
Alhamdulillah, anan zan dakata sai kuma a darasi na gaba idan Allah ya sake hadamu zamu cigaba. Idan kanada tambaya sai kayi mana comment

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button