punctuation

Menene Apostrophe a cikin karatun turanci?

Menene Apostrophe a cikin karatun turanci?

‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ yana ɗaya daga cikin ‘𝗣𝘂𝗻𝗰𝘁𝘂𝗮𝘁𝗶𝗼𝗻 𝗺𝗮𝗿𝗸𝘀’. Wato irin su 𝗳𝘂𝗹𝗹 𝘀𝘁𝗼𝗽, 𝗰𝗼𝗺𝗺𝗮, 𝗵𝘆𝗽𝗵𝗲𝗻 da dai sauran su. Amma shi ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ yawanci ana amfani ne da shi don nuna mallaka (possession). Sannan ana amfani da shi wajan samar da ‘𝗰𝗼𝗻𝘁𝗿𝗮𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻𝘀’. Dadai sauransu…..

Menene Contractions?

‘𝗖𝗼𝗻𝘁𝗿𝗮𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻𝘀’ wani salon rubutu ne da ake taƙaita kalmomi su dawo kaɗan ta hanyar jona ɓangarorin jikin kalmomi biyu mabambanta domin samar da kalma ɗaya da za ta yi aiki a matsayin cikakkun kalmomi guda biyun. 𝗖𝗼𝗻𝘁𝗿𝗮𝗰𝘁𝗶𝗼𝗻𝘀 su na da yawa sosai. Zan yi darasi na musamman a kan yadda ake amfani da ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ wajan samar da su nan gaba insha Allah.


𝗔𝗸𝘄𝗮𝗶 𝘄𝗮𝘀𝘂 𝗱𝗼𝗸𝗼𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗮 𝗸𝗶𝘆𝗮𝘆𝗲 𝗶𝗱𝗮𝗻 𝘇𝗮 𝗮 𝘆𝗶 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝘇𝗮𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝘀𝘂𝗻𝗮 (𝗻𝗼𝘂𝗻) 𝗺𝗲 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗮 (𝗽𝗼𝘀𝘀𝗲𝘀𝘀𝗶𝗻𝘃𝗲 𝗻𝗼𝘂𝗻)

Yawanci dai akan sanya ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲‘ ne tare da harafin ‘𝗦’ a ƙarshen kalmar ‘𝗡𝗼𝘂𝗻‘ domin nuna cewa wannan kalmar ‘𝗡𝗼𝘂𝗻’ ɗin ta mallaki wani abun.

𝗠𝗶𝘀𝗮𝗹𝗶;

Idan dan’uwanka ya mallaki littafi kai kuma kana son ka faɗi cewa littafin na ɗan’uwankan ne, se ka ce.

  • It is my brother’s book.
    Littafin ɗan’uwana ne.

Idan kuma 𝗽𝗿𝗼𝗽𝗲𝗿 𝗻𝗼𝘂𝗻 (sunan yanka) ne, wato kamar ‘𝗔𝘂𝘄𝗮𝗹’ ya mallaki wani abu, kamar Ƙur’ani, maimakon cewa —‘𝗧𝗵𝗲 𝗤𝘂𝗿’𝗮𝗻 𝗯𝗲𝗹𝗼𝗻𝗴𝘀 𝘁𝗼 𝗔𝘂𝘄𝗮𝗹’ kawai sai a ce—𝗜𝘁 𝗶𝘀 𝗔𝘂𝘄𝗮𝗹’𝘀 𝗤𝘂𝗿’𝗮𝗻..

Kun ga an yi amfani da 𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲 (‘) haɗe da 𝗦 a ƙarshe ‘𝗰𝗼𝗺𝗺𝗼𝗻 𝗻𝗼𝘂𝗻’ (brother) da ”𝗽𝗿𝗼𝗽𝗲𝗿 𝗻𝗼𝘂𝗻’ (Auwal) domin nuna me sunan ya mallaki Alƙur’ani. Toh kalmar ‘𝗻𝗼𝘂𝗻’ ɗin da ke da mallakin ita ce ake kira da ‘𝗽𝗼𝘀𝘀𝗲𝘀𝘀𝗶𝘃𝗲 𝗻𝗼𝘂𝗻’

𝘄𝗮𝘀𝘂 𝗺𝗶𝘀𝗮𝗹𝗮𝗻;

  1. 𝗙𝗮ɗ𝗶𝗺𝗮’𝘀 car is good. = Motar Faɗinsa na da kyau.
  2. My 𝘁𝗲𝗮𝗰𝗵𝗲𝗿’𝘀 phone is stolen. = An sace wayar malami na.
  3. 𝗠𝗮𝗿𝘆𝗮𝗺’𝘀 house is next to mine. = Gidan Maryam na bagan nawa.
  4. Our 𝗻𝗲𝗶𝗴𝗵𝗯𝗼𝘂𝗿’𝘀 wife passed away. = Matar maƙwabcina ta mutu.

A cikin jimloli guda huɗun da su ka gabata na yi amfani da ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ haɗe da ‘𝗦’ domin nuna abun da yake mallakin 𝗙𝗮ɗ𝗶𝗺𝗮 , 𝗠𝗮𝗿𝘆𝗮𝗺, 𝘁𝗲𝗮𝗰𝗵𝗲𝗿 da kuma 𝗻𝗲𝗶𝗴𝗵𝗯𝗼𝘂𝗿.

Ga 𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲👉 ‘

𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲 haɗe da harafin 𝗦 👉 ‘s

𝗚𝗮 𝗱𝗼𝗸𝗼𝗸𝗶𝗻 𝗱𝗮 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝘁𝗮 𝗮 𝗸𝘂𝗹𝗮 𝗱𝗮 𝘀𝘂 𝘆𝗮𝘆𝗶𝗻 𝗮𝗺𝗳𝗮𝗻𝗶 𝗱𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝘄𝗮𝗷𝗮𝗻 𝘇𝗮𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗞𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 𝗻𝗼𝘂𝗻 𝗺a𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗶𝘆𝗮𝗿 𝘄𝗮𝗻𝗶 𝗮𝗯𝘂.

1.
Dokar farko; 𝗔 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 𝗦 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 ‘𝗻𝗼𝘂𝗻’ ɗ𝗶𝗻 𝘁𝗮 𝘁𝗮𝗸𝗲 𝗱𝗮 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗶 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗺𝘂𝗸𝗮 𝗴𝗮𝗻𝗶 𝗮 𝗯𝗮𝘆𝗮.

Wannan dokar itace mafi shahara a fagen amfani da ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ domin nuna mallaka.

𝗠𝗶𝘀𝗮𝗹𝗮𝗶:

  1. That 𝗽𝘂𝗽𝗶𝗹’𝘀 pencil. = Wancan fensir ɗin ɗaliban.
  2. The 𝗰𝗵𝗶𝗹𝗱’𝘀 ball. = Ƙwallon yaran
  3. My 𝗺𝗼𝗺’𝘀 bag.
    Jakar mahaifiyata.

2.
Doka ta biyu; 𝗜𝗱𝗮𝗻 ‘𝗡𝗼𝘂𝗻’ 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝘀𝗮𝗻𝗰𝗲 ‘𝗽𝗹𝘂𝗿𝗮𝗹’ 𝗻𝗲 𝘀𝗮𝗻𝗻𝗮𝗻 ‘𝗽𝗹𝘂𝗿𝗮𝗹’ ɗ𝗶𝗻 𝘄𝗮𝗻𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲 ƙ𝗮𝗿𝗲𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 ‘𝗦’ 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 𝘀𝗵𝗶, 𝘁𝗼𝗵 𝘀𝗲 𝗮 𝘀𝗮𝗻ƴ𝗮 𝗶𝘆𝗮𝗸𝗮𝗰𝗶𝗻 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝗯𝗮 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 ‘𝗦’ 𝗯𝗮 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 ‘𝗡𝗼𝘂𝗻’ ɗ𝗶𝗻.

𝗠𝗶𝘀𝗮𝗹𝗮𝗶:

  1. I am going to renovate my 𝗽𝗮𝗿𝗲𝗻𝘁𝘀’ house.
    Zan gyara ma Iyayena gidan su.
  2. They have torn my 𝗯𝗿𝗼𝘁𝗵𝗲𝗿𝘀’ clothes.
    Sun yaga ma ƴan’uwana kayan su.
  3. You will sweep 𝘀𝘁𝘂𝗱𝗲𝗻𝘁𝘀’ classes.
    Za ki share ma ɗalibai azuzuwansu.

Kalmar 𝗽𝗮𝗿𝗲𝗻𝘁𝘀, 𝗯𝗿𝗼𝘁𝗵𝗲𝗿𝘀 da 𝘀𝘁𝘂𝗱𝗲𝗻𝘁𝘀 duk an ƙara mu su ‘𝗦’ a ƙarshen su sun zama ‘𝗽𝗹𝘂𝗿𝗮𝗹’.Toh sabi wannan harafin 𝗦 da suke da a ƙarshen su, se aka sanƴa mu su iyakacin ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ ba tare ‘𝗦’ ba don zamar da su ma su mallaka.

3.
Doka ta uku; 𝗜𝗱𝗮𝗻 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 ‘𝗡𝗼𝘂𝗻’ ɗ𝗶𝗻 𝘁𝗮 𝗸𝗮𝘀𝗮𝗻𝗰𝗲 ‘𝗽𝗹𝘂𝗿𝗮𝗹’ 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗯𝗮 ‘𝗽𝗹𝘂𝗿𝗮𝗹’ 𝗺𝗲 ƙ𝗮𝗿𝗲𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 ‘𝗦’ 𝗯𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿 ‘𝗜𝗿𝗿𝗲𝗴𝘂𝗹𝗮𝗿 𝗻𝗼𝘂𝗻’, 𝘁𝗼 𝘀𝗲 𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 𝗦 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗼𝗻 𝗻𝘂𝗻𝗮 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗮.

𝗠𝗶𝘀𝗮𝗹𝗮𝗶:

  1. 𝗖𝗵𝗶𝗹𝗱𝗿𝗲𝗻’𝘀 homework should be easy.
    Asament ɗin yara ya kamata ya zama me sauƙi.
  2. Many 𝗽𝗲𝗼𝗽𝗹𝗲’𝘀 houses were destroyed.
    Gidajen mutane da dama sun hallaka.
  3. Don’t eat that! It’s 𝗺𝗶𝗰𝗲’𝘀 cheese.
    Karka ci wannan! awarar ɓeraye ce.

𝗰𝗵𝗶𝗹𝗱𝗿𝗲𝗻, 𝗽𝗲𝗼𝗽𝗹𝗲 da 𝗺𝗶𝗰𝗲 duk ‘𝗽𝗹𝘂𝗿𝗮𝗹’ ne amma basu ƙare da ‘𝗦’ ba, hakan ya sa aka sanƴa mu su ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ tare da harafin ‘𝗦’.

4.
Doka ta huɗu; 𝗜𝗱𝗮𝗻 ‘𝗡𝗼𝘂𝗻𝘀’ 𝗴𝘂𝗱𝗮 𝗯𝗶𝘆𝘂 𝗻𝗲 𝗸𝗼 𝗳𝗶𝘆𝗲 𝗸𝗲 𝗱𝗮 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗶𝗻 𝗮𝗯𝘂: 𝘄𝗮𝘁𝗼 𝘀𝘂𝗻 𝘆𝗶 𝘁𝗮𝗿𝗮𝘆𝘆𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗮𝗻 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗮𝗿 𝗮𝗯𝘂𝗻, 𝘀𝗲 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 ‘𝗦’ 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 ‘𝗡𝗼𝘂𝗻’ 𝗻𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 𝗸𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗱𝗼𝗺𝗶𝗻 𝗻𝘂𝗻𝗮 𝗱𝘂𝗸𝗸𝗮𝗻𝘀𝘂 [𝗺𝘂𝘁𝗮𝗻𝗲𝗻/𝗮𝗯𝘂𝗯𝘂𝘄𝗮𝗻] 𝘀𝘂𝗻 𝘆𝗶 𝘁𝗮𝗿𝗮𝘆𝘆𝗮 𝘄𝗮𝗷𝗮𝗻 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗮𝗿 𝗮𝗯𝘂𝗻.

𝗠𝗶𝘀𝗮𝗹𝗶:

  1. 𝗠𝗮𝗿𝘆𝗮𝗺 and 𝗔𝗯𝘂𝗯𝗮𝗸𝗮𝗿’𝘀 wedding is next week.

    Bikin Maryam da Abubakar satin sama ne.
  2. Is that not 𝗔𝗹𝗶 and 𝗠𝘂𝘀𝗮’𝘀 car?
    Waccar ba motar Ali da Musa ba ce?

5.
Doka ta biyar ; 𝗜𝗱𝗮𝗻 𝗡𝗼𝘂𝗻𝘀 𝗴𝘂𝗱𝗮 𝗯𝗶𝘆𝘂 𝗻𝗲 𝗸𝗼 𝗳𝗶𝘆𝗲, 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝘆𝗮 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗶𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗻 𝘀𝗵𝗶 𝗱𝗮𝗯𝗮𝗻, 𝘀𝗲 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 ‘𝗦’ 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲 𝗸𝗼𝘄𝗮𝗻𝗻𝗲 𝗱𝗮𝗴𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 ‘𝗡𝗼𝘂𝗻𝘀’ ɗ𝗶𝗻.

𝗠𝘂𝘀𝗮𝗹𝗶:

  1. I like reading 𝗨𝗺𝗺𝗲𝗲’𝘀 and 𝗠𝘂𝗸𝘁𝗮𝗿’𝘀 books.
    Ina son karanta litattafan Ummee da na Muktar.
  2. 𝗕𝗮𝗹𝗸𝗶𝘀𝘂’𝘀 ans 𝗔𝗵𝗺𝗮𝗱’𝘀 phones are not of the same brand .
    Wayoyin Balkisu da ta Ahmad ba kamfanin su ɗaya ba.

Akwai maganganu biyu da masana Turanci su ka yi cewa Idan aka samu kalmomin ‘𝗽𝗿𝗼𝗽𝗲𝗿 𝗻𝗼𝘂𝗻’ da suke da harafin ‘𝗦’ a ƙarshen su. Kamar irin su 𝗜𝗹𝘆𝗮𝘀 ,𝗕𝗮𝗹𝗸𝗲𝗲𝘀, 𝗡𝗮𝘄𝘄𝗮𝘀 dadai sauransu…
Wasu suka ce 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 𝗦 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲 𝘀𝘂𝗻𝗮𝗻. Wasu kuma suka ce 𝗶𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗰𝗶𝗻 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝗮𝗸𝗲 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮𝘄𝗮 𝗮 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 𝘀𝘂𝗻𝗮𝗻 𝗯𝗮 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 ‘𝗦’ɗ𝗶𝗻 𝗯𝗮.

Za’a iya cewa kowanne a ciki aka yi daidai ne,amma yawanci anfi ƙara iya kacin ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ ɗin indai har an samu ‘𝗽𝗿𝗼𝗽𝗲𝗿 𝗻𝗼𝘂𝗻’ da ƙarshensu ke da harafin ‘𝗦’ ɗin.

6.
Doka ta shida; 𝗜𝗱𝗮𝗻 𝘆𝗮 𝗸𝗮𝘀𝗮𝗻𝗰𝗲 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 ‘𝗡𝗼𝘂𝗻’ ɗ𝗶𝗻 ‘𝗰𝗼𝗺𝗽𝗼𝘂𝗻𝗱 𝗻𝗼𝘂𝗻’ 𝗰𝗲, a 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝗱𝗮 𝗵𝗮𝗿𝗮𝗳𝗶𝗻 𝗦 𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 ƙ𝗮𝗿𝘀𝗵𝗲𝗻 . 𝗕𝗮 𝗸𝗮𝗺𝗮𝗿 𝘆𝗮𝗱𝗱𝗮 𝗮𝗸𝗲 𝘄𝗮𝗷𝗮𝗻 𝘇𝗮𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗮 ‘𝗰𝗼𝗺𝗽𝗼𝘂𝗻𝗱 𝗻𝗼𝘂𝗻’ ɗ𝗶𝗻 ‘𝗽𝗹𝘂𝗿𝗮𝗹’ 𝗯𝗮.

Na yi jawabi a kan hakan a darasin da na yi na ‘𝗖𝗢𝗠𝗣𝗢𝗨𝗡𝗗 𝗡𝗢𝗨𝗡’. Idan ku na buƙatar karantawa se ku yi magana a wajan comment na tura muku.

Faɗakarwa; 𝗔𝗻𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗮𝗯𝘂𝗻 𝗱𝗮 𝗮𝗸𝗮 𝗺𝗮𝗹𝗹𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗮 𝗴𝗮𝗯𝗮𝗻 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 ‘𝗽𝗼𝘀𝘀𝗲𝘀𝘀𝗶𝘃𝗲 𝗻𝗼𝘂𝗻’ ɗ𝗶𝗻 (𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗿 𝗱𝗮 𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗺𝗮 ‘𝗔𝗽𝗼𝘀𝘁𝗿𝗼𝗽𝗵𝗲’ 𝗱𝗮 ‘𝗦’ ɗ𝗶𝗻) 𝗯𝗮 𝘁𝗮𝗿𝗲 𝗱𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗸𝗼𝗱𝗮 ɗ𝗶𝗴𝗼 𝗮 𝘁𝘀𝗮𝗸𝗮𝗻𝗶𝗻 𝘀𝘂 𝗯𝗮.

Allah shine mafi sani
Allah ya bamu ikon fahimta
Hussain Abdullahi



Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Leave a Reply

Back to top button