[Mukoyi tenses] Menene Ma’anar Simple Present Tense a turanci? | Karatun turanci
Simple present tense in Hausa
LEARN TENSES: SIMPLE PRESENT TENSE
Shi simple present tense shine Aikin da mukeyi yau da kullum, wato aikin da muka dabi’antu da yinsu. galibi anayin amfani da simple present tense ne ta wadannan hanyoyin masu zuwa:
i. anayin amfani da simple present tense ga ayyukan da ake yawan mai-maitasu da abinda da yazama Al’ada. ga Misali:
She goes to bed at ten o’clock everyday – takan tafi kan gado da karfe goma kowace rana
Karin bayani: abinda wannan Jimlar take nufi shine “ta riga ta saba”
kullum da karfe goma tana tafiya kan gado
They visit us every month – Suna ziyartarmu a kowace wata
Khamisu eats every night – Khamisu yakanci (abinci) kowane dare
Sannan kuma anayin amfani da simple present tense ga ayyukan da zasu faru nan gaba. Misali:
If he does the job I shall pay him – in yayi aikin zan biyashi
iii. anayin amfani da simple present tense don bayyana gaskiyar magana (wato abinda babu karya aikinsa). Misali:
Goats are animals – Akuyoyi dabbobi ne
Kaga wannan Jimlar tayi mana bayanin tabbas cewa Akuyoyi dabbobi ne, kuma kowa yasan haka, to kaga gaskiyar magana kenan
Shuger is sweet – Sukari yanada zaki
The sun shines during the day – Rana ta kanyi haske tsawon yini
akanyi amfani da simple present tense
don bayyana aikin da yake faruwa yanzu. Misali
I understand you – ina fahimtar ka
He is my friend – Shi abokina ne.
Aisha dances well – Aisha takanyi rawa da kyau
Haka kuma, akanyi amfani da SIMPLE PRESENT TENSE da lokuta irin su:
everymorning = kowace safiya
everyafternoon = kullun da rana
everyevening = kowace yamma/dare
everyday = kowace rana
everyminute = kowane minti ɗaya
everyhour = kowane awa ɗaya
everyweek = kowane sati
everymonth = kowane wata
everyyear = kowace shekara
always= koda yaushe
everytime = kowane lokaci
often/frequently = yawanci
seldom= jefi-jefi
dasauransu.
ga misali a cikin jimlar
I always eat food. = Ina cin abinci koda yaushe.
We see her every morning. = Muna ganin ta kowace safiya.
They always ask me. = Suna tambaya ta koda-yaushe.
You eat food every evening. = Kana/kina/kuna cin abinci kowace yamma.
Ali and Ja’afar eat food. = Ali da Ja’afar suna cin abinci.
He calls Ali every Monday. = Yana kiran Ali duk/kowace litinin.
She pays the boy every year. = Tana biyan yaron duk shekara.
It eats food. = Tana/yana cin abinci. (banda mutum)
Abdul sweeps the class frequently. = Abdul yana share ajin a yawancin lokuta.
To, baya ga bayanin ƙara (s) idan anyi amfani da SINGULAR (Abdul) dakuma PRONOUN (he, she, it), Sedai…
Idan wannan VERB ɗin ya ƙare da kowanne ɗaya daga cikin waƴannan harufan (ss, sh, ch, x, z), to sai ka ƙara (es) sannan kuma furucin wannan (es) ɗin shine /iz/.
misali:
impress – impresses = burgewa
He impresses me.
wash – washes = wankewa
Shewashes the plates.
touch – touches = tabawa
Abdul always touches my books.
fix – fixes = gyara
Hefixes phones, it is his job.
quiz – quizes = yawan tambaya
Shequizzes me if she comes.
SIMPLE PRESENT TENSE POSITIVE QUESTION
Positive Question (Tambaya ta tabbatarwa)
A duk lokacin da kake so ka tambayi wani cewa: shin yana yin wani abu kuwa, to zakai amfani da SIMPLE PRESENT TENSE POSITIVE QUESTION.
- Do + I + verb
- Do + we + verb
- Do + they + verb
- Do + you + verb
misali
Do I play? = (Shin) Inayin wasa kuwa?
Do we play? = Muna yin wasa ne?
Do they play? = (Shin) Suna yin wasa?
Do Abdul and Tijjani play? = Abdul da Tijjani suna yin wasa?
DOES + HE, SHE, IT + VERB… +?
- He + does + verb
- She + does + verb
- It + does + verb
Does Ali play? = (Shin) Ali yana yin wasa kuwa?
Does he play? = (Shin) yana yin wasa kuwa?
Does she play? = Tana yin wasa ne?
Does it play? = (Shin) yana/tana yin wasa? (abinda ba mutum ba)
Abin lura: idan kai amfani da (does) to VERB ɗin ka ba sai ka ƙara mishi (s) ba.
He plays. – Does he play? (karkace… Does he plays?) (tunda ka saka (does), to karka ƙara (s, es, ies)
She plays. – Does she play? (karkace… Does she plays?) (tunda ka saka (does), to karka ƙara (s, es, ies)
It plays. – Does it play? (karkace… Does it plays?) (tunda ka saka (does), to karka ƙara (s, es, ies)
Ali plays. – Does Ali play? (karkace…Does Ali plays?) (tunda ka saka (does), to karka ƙara (s, es, ies)
SIMPLE PRESENT TENSE NEGATIVE QUESTION
Ana amfani da SIMPLE PRESENT TENSE a jaridu, finafinai, sharhin kwallo, labarai da sauran su, domin a taƙaice maganganu. Sannan ana amfani da shi domin bada labarin abinda ya faru a baya domin ƙara fito da wannan labari ta yadda zaifi sauƙin fahimtuwa dakuma daukar hankalin mai sauraro.
Negative Question (Tambaya ta korewa)
Ana yin amfani da SIMPLE PRESENT TENSE NEGATIVE QUESTION domin yin tambaya akan cewa ko ba’ayin wani abu? (ma’ana yin tambaya ta korewa):
- DO + I + not + verb?
- DO + WE + NOT + VERB?
- DO + YOU + NOT + VERB?
- DO + THEY + NOT + VERB?
Misali
Do I not play? = Shin Bana yin wasa ne?
Do we not play? = Shin bama yin wasa?
Do they not play? = shin basu yin wasa?
Do you not play? = shin bakuyin wasa?
Do Tijjani and Abdul not play? = shin Tijjani da Abdul basu yin wasa?
- HE + DOES + NOT + VERB?
- SHE + DOES +NOT + VERB?
- IT + NOT + VERB?
Misali
Does he not play? = Baya yin wasa ne?
Does she not play? = Wai bata yin wasa kuwa?
Does it not play? = shin (abu) bayayin wasa?
Does Ali not play? = Shin Ali baya wasa kuwa?
Karin bayani
Idan kai amfani da “does not”, to VERB ɗinka bazaka ƙara masa (s) ba dalili kuwa shine.
Kalmar (do) itace ake ƙarawa (es) se ta koma (does) idan akai amfani da suna guda ɗaya (Ali) da kuma wakilin suna (He, She da It), hakan yasa indai an saka (does), to basai an ƙara (s) ko kuma (es) a kalmar VERB ɗin da zai zo a gaba ba.
Wannan shine ake kira simple present tense , dafatan an fahimci Wannan Darasin, zaka iya yi mana tambaya a comment
Site: Karatunturanci.com.ng
Email: Info@karatunturanci.com.ng
i thank you so much to the learning is very benefit