Me ake nufi da Article a cikin karatun turanci
Barka da sake kasancewa a cikin wannan shafin, a wannan darasi zamuyi shine akan Article da kuma rabe raben sa
ALSO READ: BAYANAI AKAN YADDA AKEYIN AMFANI DA LOKUTA ACIKIN HARSHEN TURANCI
Bari yau mu wargaje batun wadannan kalmomin guda ukku: A, An, The. Wadannan kalmomin ana kiransu da articles a harshen Ingilishi.
In sha Allah a wannan rubutun zan yi kokarin tattauna wuraren da ya da ce a rinka amfani da su. Ba lallai a ce komai sai an fassara shi daga harshen Ingilishi zuwa harshen Hausa ba. Akwai kalmomin da ba su bukatar hakan, sai dai kawai a fahimci amfaninsu da muhallinsu.
Su wadannan kalmomin guda ukku sun rabu zuwa gidaje biyu: Indefinite articles da kuma definite article.
Zan fara da indefinite articles ne, wadanda su ne “A” da “An”
Dalilin da ya sa ake kiransu da indefinite articles shi ne; ana yin amfani da su ne a yayin da a ke son bayyana wani sabon abu da bai zama sanan ne a wajan mai sauraro ko karatu ba. Zan bada misalai tare da fassara kafin tattauna wuraren da ya da ce a rinka amfani da su.
- A boy will come here. Yaro zai zo nan.
- A teacher will be transfered to another school. Za a canza wa wani malami makaranta (ba a fayyace malamin ba)
- A book on the table. Litattafi a kan teburin. (Ba a fayyace littafin ba)
- I want to buy an orange. Ina son sayen lemu.
- He bought an egg. Ya sayo kwai.
- It is an umbrella. Lema ce.
Idan aka lura sosai za a ga cewa dukkanin jimlolin suna gabatar da wani sabon abu ne. Sannan za a ga cewa ita “A” ana sanya ta ne kafin kalmar da ta fara da baki ba wasali ba: b, k, d, z, r, s, t, m, n, y da sauransu. A dayan bangaren kuma ana sanya “An” ne a kafin kalmar da ta fara da wasali: e, i, o, u, a. A kara duba misalan.
Haka kuma idan kalma ta fara da wasali amma a furucinta baki a ke furtawa to wannan ma tana tafiya ne da “A” misalai: University, Union, European da sauransu. A dayan bangaren ma haka idan kalma ta fara da baki amma furucinta wasali ne to “An” ake yin amfani da ita, misalai: Honest, honourable da sauransu.
Definite article (The): ana kiranta da definite article ne saboda a kodayaushe ana amfani da ita don fadar abin da yake sannan ne ga mai sauraro ko karatu. Sannan ita ana iya amfani da ita da kowace kalma. Ma’ana ko kalma ta fara da baki ko wasali ba damuwa in dai har tana bukatar article a kan iya saka “the”
Misalai:
- The president of Nigeria is from Daura. Shugaban kasar Najeriya dan Daura ne.
- The boy who came here yesterday has died. Yaron da ya zo nan jiya ya rasu(mutu).
- The teachers praised the effort made by Aisha in her examinations. Malaman sun yaba a kan kokarin da Aisha ta yi.
- I ate the egg you brought yesterday. Na cinye ‘kwan da ka kawo Jiya.
- The man you met yesterday is my uncle. Mutuman da ka hadu da shi Jiya kawuna ne.
- The oil you poured in the food was too much. Man da ka zuba a abincin ya yi yawa.
Fatan alkhairi gare ku masu karanta wadannan rubuce-rubuce. Fatana shi ne ku cigaba da sani a addu’a. Allah Ya cigaba da karfafar gwiwarta na cigaba da wannan aikin. Allah Ya kara mana ilimi da basira da kuma hikimomin isar da sako.