Meaning of cycle in Hausa
Cycle (regular verb)
Cycle na nufin tuƙin keke. Wannan kalma a na amfani da ita domin nuna yin tuƙin keke kaɗai. Haka kuma idan za a yi amfani da ita, ba a yawan rubuta sunan keken. Domin ita kalmar ta ƙunshi ababe guda biyu: na farko yin tuƙi, na biyu kuma keken da aka tuƙa.
Misali:
1. I cycle to school every day.
Na kan tuƙa keke zuwa makaranta kowace rana.
2. He cycles to school every day.
Ya kan tuƙa keke zuwa makaranta kowace rana.
3. You are cycling right now.
Yanzu haka ka na tuƙa keke.
4. She cycled to market yesterday.
Jiya ta tuƙa keke zuwa kasuwa.
5. We will cycle to the supermarket.
Za mu tuƙa keke zuwa babban kantin siyayya.
Sannan kuma ma’anar kalmar cycle zai iya zama “zagaye” wato abinda ke faruwa daki daki. Misali
The life cycle of butterfly. Yadda filfilo yake sauyawa daga lokaci zuwa lokaci kafin ya girma
Ku kawo na ku misalan tare da wannan kalma. Haka kuma ka da a manta domin koyan turanci cikin harshen Hausa sai a je YouTube, a yi subscribe ɗin channel ɗin mu mai suna Nura Mahadi.