Yanda zaka iya turanci

Dalilan da yasa kake tsoron magana da turanci

Dalilan da yasa kake tsoron magana da turanci

•~ MAI TSORON KUSKURE, BAYA ZAMA GWANI A TURANCI ~•

Asalamu’alaikum ƴan uwa da abokan arziki barkan mu da wannan lokacin fatan kowa na cikin ƙoshin lafiya, Allah yasa hakan Ameen.

Darasin mu na wanan lokacin kamar yadda kuka gani a saman wanan Post, Insha’allahu yau zamu tattauna ne akan (Tsoron yin kuskure a turanci)

Toh! Kamar yadda duk dai muka sani cewa, shi KUSKURE yana kan kowa, ma’ana kowa zai iya yi. Duk yadda mutum ya kai ga kiyayewa, watarana dole sai ya kwapsa koh da kaɗan ne.

Dan haka tsoron yin kuskure duk bai taso ba, tinda daman mun san da sanin cewa shi ɗan adam ajizi ne, zai iya kuskure a kowane lokaci. Kuma babu wanda ya iya daidai face Allah (S.W.A).

TAMBAYA

Me yasa dayawan ɗaliban turanci ke tsoron yin kuskure?

AMSA

A iya nawa hasashen na lura cewa ɗaliban turanci da yawa suna tsoron yin kuskure ne sabida:-

  • Kada ayi musu dariya.
  • Kada a dinga yi musu kallon basu waye ba.
  • Dan kada kuskuren ya janyo musu tsangwama da raini.
  • Dan kada kuma su kunyatar da kan su.
  • Da dai sauran su.

TAMBAYA

Micece mafita akan wannan ɗabi’ar ta TSORON yin KUSKURE a turanci?

AMSA

Mafitar ita ce, duk wani ɗalibi mai irin wannan ɗabi’ar ta tsoron yin kuskure, yana da kyau ya dinga sakawa zuciyar sa salama, ya bi komi a sannu, ya yarda cewa turanci ba yaren sa bane, dan haka dan yayi kuskure a cikin sa hakan ba komi bane.

Kuma ka saka wannan a zuciyar ka, Shi KUSKURE abokin tafiyar NASARA ne, tare suke tafiya. Dole idan kana son cimma wata nasara, toh sai ka yarda ka amince zaka iya yin kuskure, idan kayi kuskuren sai ka gyara, sa’anan ka cigaba.

Babu wanda ya taɓa cima burin sa, face sai da ya sha gwagwarmaya a kan hanyar sa ta gina burin nasa. Yayi kuskure, ya gyara, ya sake yin wani kuskuren ya sake gyarawa har ya kai ga nasara.

SHAWARWARI GA DUKA ƊALIBAN DAKE FUSKANTAR IRIN WANAN MATSALAR TA TSORON YIN KUSKURE A TURANCI.

1. Mu rage son nuna burga da ƙarya da kai kan mu inda ba mu kai ba. (Musaman mata)

So da dama, son burge junan mu, wallahi shi ke ja mana tsoron yin kuskure. Domin kuwa mun san cewa muna yin kuskuren toh fa tamu ta ƙare. An samu abun tsokanar mu. (An samu Topic of discussion )

Mu rage ƙarya da cutar kawunan mu ta hanyar koyon grammar da matakin mu bai kai ba, wai dan kawai mu nuna mun iya grammar. (Sannu Sarakan ingila😂……Ah! Toh! Mun ga su Queen Elizabeth😏)

Lovely students, zai fi kyautuwa ku koyi grammar daidai matakin ku, (Mai sauƙi) kada aje a kinkimo wacce zata saka mutane duba Dictionary.

Ku yi turancin ku yadda ku ka iya kuma yadda kowa zai fahimce ku, kada ku ji tsoro, kada kuyi fargaba.

2. Mu daina jin tsoro kuma mu daina fargabar yin kuskure.

Mu sani mu fah ƴan koyo ne, idan ba mu cire tsoro muka yi turancin da muka iya ba, toh taya ne za’a yi mana gyara, koh kuma tayaya ne zamu ƙware kulum baki a rufe sabida muna gudun muyi turancin ba daidai ba ayi mana dariya…😶🙄🤔

Lovely students, kada ku ji tsoron kowa, kuyi turancin ku yadda kuka iya, idan kuka yi kuskure sai a gyara muku.

Masha’Allah Ƴan uwa da abokan arziki anan muka kawo ƙarshen wanan darasin na wanan lokacin fatan kowa ya amfana da wanan darasin.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button