punctuation

Menene Ma’anar Punctuation Mark a cikin karatun turanci?

Meaning of punctuation Mark in Hausa

Meaning of Punctuation in Hausa

a wannan darasin Insha Allahu zamu yi shine akan Ma’anar punctuation Mark da yanda ake amfani dashi a turanci

 

Menene Punctuation Mark?

Punctuations  :-
Abinda ake kira “punctuation” shine kamar alamin dakatawa ko kuma tambaya ko kuma motsin rai da dai sauransu Yanzu zamu kawo wasu daga cikin punctuation sannan kuma muyi bayani akan amfaninsu, gasu kamar haka:

1. FULL STOP (.) :-

Wato (.) wannan shine ake kira “full stop” anayin amfani dashine a ƙarshen jima, ba’ayin amfani dashi wajen tambaya ko wajen abin ban mamaki, sannan kuma anayin amfani dashi wajen abbreviation (taƙaita kalma)
Ga misali

1. The boy is good. – yaron kirkine.
2. A.B.U (Ahmadu Bello University)

ALSO READ: Kalmomin da akafi amfani dasu ta bangaren auratayya (marriage) a turanci zuwa hausa

 

2. COMMA (,):-

Anayin amfani da comma (,) wajen warware kalmomin da sukazo a jere, sannan kuma anayin amfani da comma (,) don warware phrases da kuma clauses

Misali

1. My father bought me a book, pen, ruler and eraser – Mahaifina ya sayomin littafi, fensiri, rula da kuma abin share rubutu.

2. Maryam, the must intelligent girl in the class, is sick – maryam, da tafi kowa ƙwaƙwalwa a ajin, bata da lafiya

Karin bayani:- agaskiya comma anfi yin amfani da ita fiye da sauran, shiyasa zamu kawo wasu daga cikin anfanin comma

1. Zaka iya yin amfani da comma a “direct speech”
Wato abinda ake nufi da “direct speech” shine maganar da aka kawota kamar yadda mai maganar ya faɗa ba’a canza ba. Misali

“I must visit my friend”, Jamilu said – “Dole na zayarci abokina,” Jamilu yace

“He has not paid her school fees”, the teacher said – “Bai taɓa biyan kuɗinmakaranta ba,” malamin yace

3. Anayin amfani da comma wajen rubuta “yes” ko “No”
Misali

Yes, I will help you – E, zan taimakeka

No, she never goto school – A’a, bata zuwa makaranta

4. Ana kuma yin amfani da comma bayan buɗe gaisuwar wasiƙa
Misali

Dear sir,
Dear Abdul,
Dear father,
Dear mother,
Dear madam,

5. Sannan kuma zaka iya yin amfani da comma domin rarrabe tsakanin rana da shekar, a kwanan wata
Misali

Tuesday,5th November, 2019
Monday, 2th December, 2019

3. COLON (:)

It is used to introduce the details of list things.

Anayin amfani da colon (:) wajen gabatar da wani abu da sukazo a jere
Misali

He give me the following items: books, shoes, money and bags – ya bani waɗannan abubuwan: littafai, takalma, kuɗi da jakunkuna

ALSO READ: Kalmomin turanci da fassarar Hausa
Yadda ake cewa Ƙato, Jibgege, Lafkeke da turanci
SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU
[Learn how to read] Sirrin yanda zaka koyi karatu cikin sauki

4. SEMI-COLON (;)

Anayin amfani da semi-colon (;) ne a tsakanin “main clauses” waɗanda ba’a haɗasu da “conjunction” ba

Misali

I did not read much; never the lesd, i am sure i will pass – Banyi karayu da yawa ba; duk da haka na tabbata zanci

5. QUESTION MARK (?)

Shikuma “question mark” (?) wato alamar tambaya anayin amfani da ita a ƙarshen tambaya.
Misali

How? – yaya?

What is your name? – menene sunanka?

Did you see the boy? – ko kaga yaron?

6. EXCLAMATION MARK (!)

Shikuma “exclamation mark” ana amfani dashi a ƙarshen jimla wajen nuna abin ban mamaki, murna, jin yunwa, ko kuma wajen jin daɗi.
Misali

Oh! They have killed it – wayyo sun kasheta

Oh my God! – wayyo Allah!

Oh no! – ayya ba haka ba!

7. QUOTATION MARK/INVERTED COMMAS (” “)

Shikuma “Quotation mark” ko kuma “Inverted commas” anayin amfani dashine domin nuna haƙiƙanin maganar da wani ya faɗa, sannan anayin amfani dashi wajen rubuta suna na fina finafinai, littafi, wasa da sauransu
Misali

“He is still alive” she said – “yana nan dai anan”, ita tace

“I can’t go any where”, the police said – “Bazan iya zuwa ko ina ba” Ɗan sandan yace.

“The student dictionary”

“Mastering English”

ALSO READ: Me ake nufi da Interjection a cikin karatun turanci?

 

8. APOSTROPHE (‘)

Anayin amfani da “apostrophe” wajen nuna alaman mallaka.
Misalii.
Abdullahi’s property has found – anga kayan Abdullahiii.
This car is belong to Aisha’s husband – wannan motar mallakan mijin Aisha ne

Ƙarin bayani:- akan sanya harafin “s” ne kawai a gaban kalma domin nuna alaman mallaka idan kalmar ta ƙare da harafin “s” akan sanya apostrophe (‘) ne kawai domin nuna alaman mallaka misali

Boy’s book – yana nufin littafin yaron
Sannan kuma anayin amfani da apostrophe (‘) wajen taƙaita kalma
Misali

Don’t – yana nufin “do not”

Can’t – yana nufin “can not”

They’ll – yana nufin “They will”

She’d – yana nufin “She had”

She’d – yana nufin “She would”

Won’t – yana nufin “will not”

We’ve – yana nufin “we have”

They’d – yana nufin “They would”

You’re – yana nufin “you are”

I’ll – yana nufin “I will”

Da dai sauransu

ALSO READ: Yanda (had/have/has/were/was) suke zuwa ko yadda ake amfani dasu a cikin magana
Menene subject da object personal pronoun?
Menene homophones a turanci?

 

9. HYPHEN (-)

Anayin amfani da “Hyphen” ne wajen haɗa kalma biyu ko fiye da biyu domin su zama ɗaya. Misali

i. Mother-in-law – suruka

ii. Father-in-law – suruki

iii. Sister-in-law – ƴar uwar abokin aure

iv. Mail-box – akwatin sako

v. Summing-pool – Ruwan wanka

vi. Thirty-six – Talatin da shida

Da dai sauransu

Sannan kuma anayin amfani da “Hyphen” yayin da kalma ta fara a wani layi ta kuma ƙare a wani layin da ban (Ma’ana kamar kaniyin rubutu a littafi sai kazo rubuta wata kalma aloƙacin da layin ya ƙare to zakayi amfani da “Hyphen”

Misali
i. They did not under-
stand the work – Basu fahi-
mci aikin ba

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci
Menene antonyms a cikin karatun turanci? (Antonyms words)
Menene Internet slang words da kuma yanda ake amfani dashi a social media (Yaren chatting)

 

10. BRACKETS ()

Wato bracket ( ) shine ake kira “baka biyu” a hausa
Anayin amfani da bracket ( ) wajen yin ƙarin bayani akan abunda ya wuce wanda bai zama dole ayishi ba.

Misali

i. Last week the boy wrote five letters a day (That is he wrote five letter each day) – A satin daya wuce yaron ya rubuta wasiƙa biyar a rana (hakan yana nufin ya rubuta wasiƙa biyar a kowace rana)

ii. I have a book (one book) – inada littafi (Littafi ɗaya)

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

3 Comments

Leave a Reply

Back to top button