Yadda ake rubuta informal letter a turanci (letter writing)
Mukoyi rubutun wasika
Yadda ake rubuta wasikar Informal letter da turanci cikin sauki
Muna maraba da sake ganinka a cikin wannan shafin mai albarka, a wannan darasin zamu kawo shine akan yanda ake rubuta wasikar Informal letter a cikin sauki
What is Informal letter?
Informal letter :- are those Letters which we write to our parents, relatives, friends, and acquaintances in their private capacities.
Menene Informal letter?
Informal letter : Wasikune da muke rubutawa iyayenmu, makotanmu, Abokanmu, da dai sauran makamantan haka.
KA’IDOJI NA YANDA ZAKA RUBUTA WASIKAR INFORMAL LETTER:
Shima dai Informal letter yanada nashi ka’idojin da ake rubuta wasikar shi,
Ka’idojin kuwa Sune kamar haka:
1. Address Of The Writer
2. Date
3. The Salutation
4. Introduction
5. Body Of The Letter
6. Conclusion
7. Subscription
8. Name Of The Writer.
Ga bayaninsu daya-bayan-daya :
1. Address Of The Writer:- The address is very important and this should be written at the top right-hand corner of the answer paper.
Idan kaji ance address of the writer a turanci to ana nufin adireshin shi kanshi Mai rubutun,
Adireshin Mai rubutu yana daya daga cikin abubuwan da ya zama dole kasanyashi aduk lokacin da zaka rubuta wasika , ana sanya adireshin Mai rubutune a saman paper, a bangaren dama,
Abubuwan da zaka rubuta shine: Sunan layi, Lambar gida, da kuma unguwar ku, Sunan gari, ko kuma sunan kasar da kake (idan ya kasance zaka aika wasikarka zuwa wajene)
2. The Date: The Date is another important element and it should be correctly written on the line immediately after the address. The forms below are acceptable
2nd May, 2020
May 2, 2020
Kwanan wata: ana rubuta kwanan wata ne akasan adireshi, sannan kuma anaso a duk lokacin da zaka sanya kwanan wata ka rubuta shi yanda yakamata
Kada kazo rubuta kwanan wata ka rubuta haka: 02/05/2020 ko kuma 02-05-2020, duk in kayi haka, to kayi kuskure
yanda ake bukatar ka rubuta kwanan wata shine kamar haka:
2nd May, 2020
May 2, 2020.
Duka wadannan guda biyun an amince ka rubutasu a matsayin kwanan wata,
Abin Lura: zakaga a kwanan wata na farko na sanya “2nd” sannan kuma ana biyu na cire “nd” sai na sanya “2” dukkaninsu in kayi haka babu kuskure a cikinsu (zaka iya yin amfani da na farkon, haka zalika zaka iya yin amfani da na biyun)
TSARIN YANDA AKE RUBUTA ADIRESHI.
Shima informal letter ba ko yaya ake rubuta adireshi ba, yana da kyau kabi ka’idojin yanda ake rubuta adireshi.
Tsarikan yanda ake rubuta adireshi na informal letter ya rarrabu har uku (3), Sune kamar haka:
1. Slanting Style
2. Block Form.
3. Unpunctuated form
Bari muyi bayaninsu daya-bayan-daya
1. Slanting Style: Slanting Style ana kiran shi da “Slanting Form” ko kuma “Indented Style”
Shi wannan adireshin, adireshine Wanda zaka sanyashi a Karkace wato ta hanyar karkatar dashi ta hanyar sakin layi daya ko biyu daga kasa, sai yazama a Karkace. Ga misali
Gazikiya Villa,
25, kowa-de-kowa Avenue,
Galadima Estate,
Kano.
Wannan shine adireshin shine ake kira “Slanting Style”
2. Block Form:- akan kirashi da “Block Style” ko kuma “Non Slanting Style” shikuma wannan adireshine Wanda zaka rubuta shi a Mike ba tare da karkata ba. Ga Misali:
Gazikiya Villa,
25, kowa-de-kowa Avenue,
Galadima Estate,
Kano.
Wannan adireshin shine ake kira “Block Form”
3. Unpunctuated:- wato shi Unpunctuated duk kusan iri daya ne da sauran adireshin da muka bayar a sama, Banbancinsu kawai shine idan kun Lura adireshin da muka kawo a sama zakaga muna sanya alamar comma (,) akowani karshen layi, to shi adireshin Unpunctuated ba’a sanya alamar Comma (,) a kowani layi,
Shi Unpunctuated kawai zallar adireshin ake rubuta wa, saboda idan baku manta ba a karatun mu na Formal Letter Munce dole ne mutum ya riqa sanya comma aduk lokacin da zaka rubuta adireshi, to amma shi informal letter bai zama dole mutum ya sanya comma (,) ba. Ga Misali:
Gazikiya Villa
25, kowa-de-kowa Avenue
Galadima Estate
Kano
Idan kun Lura kowanne daga cikin adireshin dana rubuta na sanya alamar comma a karshen layin, amma shi Unpunctuated ba’a sanya shi ba.
Ina fatan Mai karatu ya fahimci Wannan :
3. Salutation:- wato Ban girma, shikuma ana rubutashine a hagun takarda, a kasan adireshinka, Sune kamar haka:
Idan zaka aikawa iyayenka wasikar ne sai kayi amfani da wadannan Kalmomin
Dear Father, (Baba)
Dear Mother, (Mama)
Dear Dad, (Baba)
Dear Mummy, (Mama)
Idan kuma matarkace zaka rubuta mata wasika, sai kayi amfani da wadannan Kalmomin :
My Darling Wife,
My Darling,
Idan kuma mijinki ne zaki rubuta mashi wasikar, sai kiyi amfani da wadannan Kalmomin:
Dear Husband,
My Dearest Husband,
My Darling,
Idan kuma abokanka ne zaka aikawa wasikar sai kayi amfani da wadannan Kalmomin:
My Dear Basma,
My Dear Tijjani,
Dear Ibrahim,
Dear Nafisat,
Idan kuma zaka aikawa wasikar zuwa ga wani dan uwanka ko makocinka ne, to sai kayi amfani da wadannan Kalmomin :
My Dear Brother,
Dear Sister Nafisat,
Dear Auntie,
Dear Uncle Tijjani,
Abin Lura: anaso kowani farkon harafi yakasance da babban harafine, Misali kamar kace “Dear Father, ka kace zaka rubuta da karamin baki kamar haka : “dear father” ko kuma “dear nafisat”
4. Introduction:- wato Kalmar “introduction” yana nufin “Gabatarwa ”
Shikuma abinda ake nufi da gabatarwa shine zaka rubuta Dan gabatarwa game da wasikar naka Kafin kafara rubuta “Body of the letter”
Wato zaka iya tambayar yaya lafiyarsa Wanda Kake rubuta masa wasikar, Sannan kuma kafada masa taka Lafiyar (cewa kana lafiya lau), ko kuma idan wanda zaka rubuta mashi wasikar ya rigaka rubutawa, to sai kafada masa cewa ka sami tashi wasikar, ina fatan an fahimci Wannan
5. Body Of The Letter – Gangar Jilin Wasika.
The body of the letter should be written in paragraphs, each paragraph containing one major idea
Wato shikuma Gangar Jikin wasika shine dukkanin wasikar ka, anada bukatar yakasance akwai sakin layi a ciki wato paragraph, idan kana sakin layi a rubutunka zai sanya rubutun naka ya Kara kyau, haka zalika shi Mai karanta rubutunnaka zaiyi mashi dadin karantawa, ina fatan duk za’a kiyaye wannan
6. Conclusion:- wasu sukan kirashi da “The end of the letter” wato karshen wasika ko kuma ince maku rufe wasika, ana rufe wasikane bayan an gama dukkanin wani rubutu na wasikar ka, akanyi wani irin nau’in rubutune na nuna alamar cewa wasikarka tazo karshe, Bari in kawo maku Misalin rubutun Conclusion :
Please help me greet Tijjani
Salute grace for me
Ko kuma wasu kalmomi makamancin haka, Wanda zasu nuna cewa rubutunka yazo karshe
7. The Subscription:- The Subscription is the end of the letter and it should be written correctly thus :
Your Loving Son,
Abdulmaleek .
Your Affectionately,
Tijjani
Subscription shine “Rufewar bankwana” shikuma ana rubuta shine a karshen wasika, Sannan kuma anada bukatar karubutashi da kyau kamar wadannan.
Your Loving Son,
Abdulmaleek.
Your Affectionately,
Tijjani.
Abin Lura: anayin amfani da comma (,) a karshen layin Subscription, Sannan kuma anaso farkon harafin yakasance da babban baki ka rubuta shi. Ga Misali:
Your Friend,
Your Loving Friend,
Yours Sincerely,
Your Sever,
Yours Friendly,
Yours Brotherly,
Yours Sisterly,
Yours Son,
Yours Brother,
Da dai sauran su.
8. Name Of The Writer:- wato sunan marubuci
Shikuma sunan marubuci ana rubutashine akasan subscription, kamar yanda mukayi darasi a formal letter munce ana rubuta cikakken suna (wato sunan ka da na mahaifi), amma shi informal koda baka rubuta cikakken sunanka ba ba matsala bane, zaka iya ka rubutashi kamar haka :
Your Loving Son,
Tijjani.
Yours Friend,
Ibrahim.
Yours Loving Wife,
Basma.
Salon Rubutun Informal Letter:- a karatun mu na formal munyi bayanin cewa ba’a yin wani irin nau’in rubutu kamar irin su Karin magana da sauransu, amma shi informal letter duk zaka iya yinsu, zaka iya yin proverb (Karin magana) da kuma Idiom (Salon magana)
BAMBANCIN YANAYIN RUBUTUN FORMAL LETTER DA KUMA INFORMAL LETTER.
Kamar yanda na fada maku yanayin rubutunsu ba daya bane, shi formal letter anaso ka fitar da kowani harafi yanda yake, ba’a so ka rika yin abbreviation a rubutunka na formal letter, amma shi informal duk zaka iya yinsu, Ga dai misalansu a kasa.
Informal. Formal.
I’m. I am
I’v. I have
There’ll There will
He’d. He would
He won’t. He will not
I shan’t. I shall not
It’s. It is
It isn’t. It is not
He doesn’t. He does not
You can’t. You can not
What’s the matter. What is the matter.
Sannan akwai wasu yanayin rubutu wanda karka kuskura kayi su a formal letter, musamman ma a wajen rubuta jarabawa na WAEC ko NECO, saboda nasan wasu sukanyi Hakane saboda wai su suna sauri, to agaskiya yin haka kana janyowa kanka asara ne, domin tasanadiyyar haka, koda ka cinye jarabwar naka to za’a rage maka maki, sakamakon rubuta wadannan Kalmomin, GA irin Kalmomin tare da yanda yakamata ka rubuta su
Kuskure: ‘Cos
Dai-dai: Because
Kuskure: Smth
Dai-dai: Something
Kuskure: ‘Out
Dai-dai: Without
Kuskure: Std
Dai-dai: Standard
Kuskure: Sb
Dai-dai: Somebody
Kuskure: Estb
Dai-dai: Establishment
Kuskure: B4
Dai-dai: Before
Kuskure: illustn
Dai-dai: illustration
Ina fatan mai karatu zai rika kiyaye wadannan a rubutunsa, Sannan kuma ina fatan an fahimci Wannan Darasin namu, idan kuma kanada tambaya sai kayi mana comment,
- Karku manta bayan ka karanta kuma ka fahimci Darasin namu sai kayi mana shiyaring domin wasu ma su karanta, kuma su amfana.