Letter writing in Hausa

Yadda ake rubuta wasikar semi-formal letter

Koyon rubutun wasika (semi-formal letter)

Yadda ake rubuta wasikar semi-formal letter da turanci

Ita dai wannan Wasikar itace wasikar da take tsakanin Formal Da kuma Informal, zamu iya rubuta Wannan wasikar ne ga mutanen da bamu da wata alaka dashi ta musamman, 
amma kuma sai dai munada kusanci dasu, yawanci irin wannan wasikar na Semi-formal Letter  wasikace wanda zamu rubutashi zuwa ga mutanen da muke masu ganin mutunci, MISALI: kamar Dalibi ya turawa malaminsa wasika ko kuma Limamin garinku (Wanda yake janku Sallah) 

ALSO READ: [Learn how to read] Sirrin yanda zaka koyi karatu cikin sauki

Ko kuma na wata ma’aikata Wanda zaka turama wani oganka a office da dai sauran makamancin haka
Sannan kuma kamar yanda nace maku wasikar Semi-formal letter wani bangare tanada siffofin Formal letter da kuma Informal letter, eh tabbas Hakane, karanta Wannan Darasin namu da kyau domin fahimtar haka.

KA’IDOJI NA YANDA ZAKA RUBUTA WASIKAR SEMI-FORMAL. 


1. The address (adireshi) 
2. The Date (kwanan wata) 
3. Salutation 
4. Introduction 
5. Body Of The Letter 
6. Conclusion 
7. Subscription 
8. Name & Signature 



ALSO READ: Yadda ake rubuta informal letter a turanci (letter writing)

1. The address:- Matukar ka fahimci Darasin mu na Formal letter da kuma informal letter to duk dayane ake rubuta adireshin su, Dukkaninsu ana rubutawa a sama, sannan kuma a bangaren dama.

2. The Date:- shima dai kwanan wata duk dayane, ana rubuta shine a kasan adireshi, kuma duk a bangaren dama ne, sai dai kuma wajen rubuta adireshi ya rabu gida biyu, ta wani 6angaren yayi Kama da Formal letter, amma kuma tawani bangaren yayi Kama da Informal letter, dalili kuwa shine :

Idan yakasance wanda zaka tura mashi wasikar baya office  (Ma’ana bashi a wajen aiki) kaga dole a aika masa da wasikar gida, to anan dole kayi amfani da irin adireshin Formal letter (Ma’ana zaka rubuta adireshin ne da naka da kuma na wanda za’a Kai mashi wasikar)

Ga Misalin adireshin

                              Masses champion Area, 
                             3/4 God’s Grace Way, 
                            P.M.B 05010
                            Bauchi.
                           22nd April, 2020

Block 13,
Paradise Avenue, 
Festal Village, 
Lagos State. 

Dear Sir. 

Kaga Wannan adireshin yayi Kama da Formal letter, amma kuma idan yakasance a makaranta ne kuke gaba dayanku, to anan kai bazaka rubuta adireshin kaba, Haka zalika bazaka rubuta adireshin shi malamin naka ba, kawai adireshin makaranta ne ake da bukatar kasanyashi, sannan kuma anaso kasanya adireshin makarantar ne a sama, ku a bangaren dama, Ga Misali :

                    Aminu Kano college,
                    Of Islamic and Legal, 
                    BUK Road, 
                    P.O Box 6032,
                    Kano. 


Kaga shima wannan adireshin yaso yayi Kama da Informal letter.

ALSO READ: Kalmomin da akafi amfani dasu a watan azumi (Ramadan) a turanci zuwa Hausa

3. Salutation:- shikuma Salutation yana da bambanci da Informal letter kadai, idan har kasan sunan wanda zaka aikawa da wasikar to sai ka rubuta Kamar haka:

Dear Professor Tijjani. 
Dear Mrs Nafisat 
Dear Sir 
Dear Mr Ahmeed 
Dear Alhaji Ibrahim 
Dear Uncle Bukar
Da dai sauran su

A takaice dai abinda ake nufi da Kalmar Salutation shine gaisuwan ban girma, kamar yanda nayi maku bayani a baya (Wato acikin gaisuwar akan bayyana matsayin sa ko mukamin sa) Sune irinsu “Mrs” “Sir” “Mr” “Professor”
Ina fatan an fahimci Wannan

ALSO READ: Yadda ake rubuta wasikar formal letter | Formal letter in Hausa

4. Introduction:- introduction na Semi-formal letter Yasha bamban dana Informal letter, Saboda shima Semi-formal letter Kusan iri daya ne dana Formal letter, zaka danyi rubutune game da abinda zaka rubuta, idan yakasance shine ya fara rubuto maka wasikar to zaka fara bayyana mashi cewa ka samu wasikar shi, idan kuma kaine zaka fara rubuta masa wasikar to sai kafara rubuta dalilin rubuta wasikar naka.

ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci

5. Body Of The Letter:- wato Gangar jikin wasika, shikuma ananne zaka rubuta dukkanin wasikar naka, sannan kar amanta a rika yi ana hadawa da sakin layi (paragraph), domin yin hakan shine zai sanya rubutunka yayi kyau Sosai-Sosai.

6. Conclusion:- kamar dai yanda muka yi bayani a baya, Conclusion yana nufin rufewa, wato bayan ka kammala rubuta wasikar naka, akwai wani irin nau’in magana da akeyi domin a fahimci cewa wasikar naka tazo karshe, kamar kace “Daga karshe ina gaishe da kowa da kowa”

ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU

7. Subscription:- Subscription shine Rufewar bankwana, kamar dai yanda idan kanayin hira da mutum, bayan kungama hiran kukanyi wani irin gaisuwa na bankwana, to shima haka a rubutun wasika, a rubutun Wasika zaka rubuta ne kamar haka:

                                 Yours Sincerely 
                                 Yours Faithfully 
Sannan kuma Shima Semi-formal letter  in San samu ne anaso ka rubuta Subscription tare da cikakken sunanka a kasa, ga Misali :

                    Yours Sincerely 
                      Tijjani Lawan Kolo 

Menene semi-formal letter a hausa?
Koyon rubutun wasika

 



Alhamdulillah, ananne mukazo karshen wannan darasin namu na LETTER WRITING, Ina fatan yanzu kowa zai iya rubuta kowace irin nau’in wasika ba tare da wata matsala ba, idan kuma kaga gyara ko kuma abinda baka fahimta ba sai kayi mana comment a kasa 


Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Leave a Reply

Back to top button