Menene bambanci tsakanin kalmar Where da kuma Were?
Bambanci tsakanin
(Where and were)
Where
‘Where’ shi kalmar “Adverb” ne. Sannan kuma “Interogative adverb” ne wanda ake amfani dasu wajan yin tambaya kodai kaitsaye kokuma akasin hakan.
Idan muka zo kan “Adverb” zefi armashin ganewa dakyau.
Misali
- Where is your brother?
Ina ɗan uwanka? - Where are you going?
Ina zuwa? - Where did you grow up?
A ina ka girma?
a cikin darasin da muka gabatar akan “Adverbs” munyi cikakken bayani akan wannan
sannan kuma wannan kalmar ”Conjunction” ce. ‘Conjunction’ kalmomi ne da ake amfani da su wajan jona wasu jimloli ko kuma kalmomi da waɗansu kalmomin kokuma jimlolin daban.
Misali
Keep the remote control where we can find it easily.
Ajiye Ramot ɗin a inda zamu iya nemoshi cikin sauƙi
This is where Hassan and I live.
Nan-ne inda ni da Hassan muke zama.
Sai kuma Were;
Wannan kuma kalmar “Auxiliary verb” ce, wadda suke aiki tare da “ Main verb” kokuma nace suke temakawa “Main verb” wajan bayar da cikakkiyar ma’ana da kuma nuna lokacin da abu ya auku, kokuma yake kan faruwa.
Sannan kalmar “Were ” “Past form” ce sannan kuma “Plural”ce. Wani ze ce kalmar “Verb” kuma ance ‘plural’? Eh tabbas ana amfani ne da ita yayin da abu yariga yafaru kokuma yake kan faruwa amma waɗan da sukayi aikin sai sun kasance mutane fiye da ɗaya (Plural)
Misali
- He is…..
- They are……
- They were……..
Dukkanin waɗannan da na kawo, idan aka saka musu kalmar (Coming) zeyi aiki dasu, amma sedai akwai bambanci tsakanin lokutan-aukuwar lamuran.
Misali
- He is + Coming
(simple continuous singular) - They are +Coming
(Present continuous plural) - They were +Coming
(Past continuous)
a cikin darasin mu da mu.kayi a cikin wannan shafin na “Tenses ” munyi jawabi SOSAI-SOSAI.
Ku huta lafiya