Bambanci tsakanin “Borrow” da kuma “Lend” a turanci
Mutane da dama kan kuskure wajen amfani da waɗannan kalmomi biyu masu kamanceceniyar ma’ana. Muhallin da ya kamata a yi amfani da kalmar farko, sai su yi amfani da kalma ta biyu. Ko kuma inda ya kamata a yi amfani da kalma ta biyun sai su yi amfani da kalma ta farko.
Haka na faruwa ne saboda rashin sanin cikakkiyar ma’anar kowace daga cikin waɗannan kalmomi biyu. Waɗannan kalmomi a na amfani da su domin karɓa ko bayar da bashin kuɗi ko aron wani abun daban.
Banda waɗannan kalmomin akwai wasu kalmomin da ke rikitar da dalibai wajen fahimtar muhallin da ya kamata a saka su a cikin wata jimla ta turanci. Bari mu dubi yadda ake aiki da waɗannan kalmomi yadda ya kamata a ƙa’ida.
Misali, kai da abokinka kun je restaurant (shagon abinci) gashi kuma kai ba ka da kuɗi. Sannan kuma ka na son siyan wani abu ka ci, abokinka ya na da kuɗi. Sai ka tambaye shi ya arama wani abu daga kuɗin gurinsa, za ka siya abinci. Idan mu ka dubi wannan misali, za mu ga:
Na farko kai a gurinka wannan tambayar kuɗin da ka yi ita ce borrow.
Na biyu kuma amincewar da ya yi zai baka aron kuɗin shine lend.
Na uku kai ne mai karɓan aron kuɗin.
Na huɗu shine mai bayar da aron kuɗin.
Mene ne borrow?
Borrow na nufin karɓan aro daga wajen wani.
Misali:
Would borrow me ₦10, please?
Shin za ka bani aron Naira 10?
He asks me to borrow him my phone.
Ya kan tambayeni na aramasa wayata.
She will ask him to borrow his pen.
Za ta tambayeshi ya bata aron bironsa.
They borrowed $200 from us.
Sun karɓi aron Dala 200.
Mene ne lend?
Lend shine bayar da bashin kuɗi ko aron wani abu daga wani mutum zuwa wani.
Misali
I will lend you ₦10, when are you going to pay me back?
Zan ba ka aron Naira 10, amma yaushe za ka dawo mun da kuɗi na?
I lend my phone sometimes.
Wasu lokutan na kan bashi aron wayata.
We don’t lend them our pencils.
Ba ma ba su aron fensiranmu.
I can’t lend you $250.
Ba zan iya baka aron Dala 250 ba.
Borrow shine karɓan bashin kuɗi ko aro. Lend kuma bayar da bashin kuɗi ko aron wani abu.
Would you borrow me your new pair of jeans?
Shin za ka bani aron sabon wandon jins na ka?
Yes. I will lend it to you.
Eh, zan ba ka aronsa.