Ma’anar kalmar “Light” a cikin karatun turanci
Meaning of light in Hausa
Kalmar light kamar sauran kalmomin turanci, ta na da ma’anoni daban daban. Ma’anarta a matsayin suna ta bambanta da ma’anarta a matsayin siffa. Bari mu dubi waɗannan bayanai mu gani.
1. Light (Noun)
Light a matsayin suna ya na nufin haske.
Misali:
The Sun provides the light we use to see during the day.
Rana ce ke bamu hasken da muke gani da rana.
This lamp has a dim light.
Wannan fitilar haskenta ya rage.
2. Light (Adjective 1)
Kalmar light a matsayin siffa ta na da ma’anoni daban daban, na farko ta na nufin maras nauyi.
Misali:
You can lift that box because it is light.
Ka na iya ɗaga wancan kwalin domin ba shi da nauyi.
Matress is a light substance.
Katifa abu ce maras nauyi.
3. Light (adjective 2)
Kalmar light a matsayin siffa, a ma’ana ta biyu ta na nufin abu mai haske.
Misali:
I normally don’t sleep in a light room.
Ba na kwanciya a ɗaki mai haske.
We study in light classrooms at nights.
Mu kan yi karatu a azuzuwa masu haske da dare.
Ku na iya kawo naku misalan tare da wannan kalma.
Sannan kuma ka da dai a manta ayi subscribe ɗin channel ɗin mu mai suna Nura Mahadi da ke YouTube domin koyan turanci cikin sauƙi.