Me ake nufi da Regular Plural Noun a cikin karatun turanci
Meaning of regular plural Noun in Hausa
Barka da sake kasancewa a cikin wannan shafin na Karatunturanci, awannan darasin zamu kawo Ma’anar Plural Nouns ne tare da yanda ake samar dashi, shafin karatunturanci shafine da kokarin kawo darussan turanci a cikin sauki.
ALSO READ: Menene antonyms a cikin karatun turanci? (Antonyms words)
Menene Noun?
Kafin mu shiga cikin darasin yakamata musan Menene Noun , Atakaice dai Noun shine sunan kowani abu, idan mukace kowani abu kenan ya hada da sunan mutum, sunan dabba, sunan gurare, har ma da sunayen abubuwa (things)
ALSO READ: Yadda ake amfani da kalmomin “were” da kuma “was” a cikin darasin turanci
ALSO READ: Me ake nufi da Dis prefix a cikin darasin turanci?
Menene singular Noun?
Singular Noun shine sunan da yake nuni ga mutum, guri, dabba, kowani abu guda daya tilo , Atakaice dai Singular Noun yana nufin abinda yake guda daya ne. Bari mu kawo misali:
There is one book on my table and one pen on my chair – Da akwai littafi guda daya akan teburin da kuma abin rubutu guda daya akan kujera ta.
Kaga a wannan jimlar kalmomin “book”, “Table”, “pen”, da kuma “Chair” duk singular Noun ne, saboda dukkannin su kalmomine da suke nuni ga abu kwara daya tilo
ALSO READ: Menene Ma’anar compound Noun da Hausa?
1. Singular Noun zai iya kasance wa sunan mutum, misali:
- Abdullahi
- Maryam
- Father
- Mother
2. Singular Noun zai iya kasance wa sunan guri, Misali:
- City – birni
- Town – gari
- Country – kasa
- Sea – teku
3. Singular Noun zai iya kasance wa sunan abubuwa, Misali:
- Bicycle – Keke
- Computer – na’ura mai kwakwalwa
- Letter – wasika
Menene Plural Nouns?
Plural Noun shine sunan Mutane, gurare, dabbobi, ko kuma abubuwa wanda yake sama da guda daya
Atakaice dai plural Noun shine sunan da yake guda biyu ko sama da haka
Yawanci ana karawa kalmar Singular Noun wasu haruffa ne domin su zama plural Noun, Misali ana karawa Singular Noun harafin “S” don ya zama plural Noun. Misali:
- Girl – yarinya Girls – ‘yan mata
- Boy – yaro. Boys – Yara (masa)
- Rat – bera. Rats – beraye
- Town – birni Towns – butane
ALSO READ: Yadda ake gane singular and plural na verb a turanci
Yanda ake samar da plural Noun
1. Wasu daga cikin plural Noun ana samar da sune ta hanyar karawa Singular Noun harafin “s”, kamar dai yanda nakawo Misali a sama,
Singular Nouns | Plural Nouns |
---|---|
Car – mota | Cars – motoci |
Bag – jaka | Bag – jakuna |
Table – teburi | Tables – tebura |
House – gida | Houses – gida je |
Dog – kare | Dogs – karnuka |
ALSO READ: Yadda ake furta kalmomin turanci a cikin sauki
2. idan karshen Singular Noun ya kasance yana fitar da sautin “Sh” a karshe (wato irin Kara da lasifika take yi), Atakaice dai irin wadannan sautin /s/, /z/, /ʃ/, /ʒ/, /tʃ/ or /dʒ/ , ana samar da plural dinsu ne ta hanyar karawa kalma “es”, Idan kuma kalmar ta kare da “e” ne sai a karawa kalmar “s” kawai. Misali
- kiss – kisses – /ˈkɪsɨz/
- dish – dishes – /ˈdɪʃɨz/
- witch – witches – /ˈwɪtʃɨz/
- judge – judges – /ˈdʒʌdʒɨz/
3. Idan kalmar Singular Noun ta kare da harafin “f” ko kuma “fe” , ana samar da plural din su ne ta hanyar canza harafin “f” ko kuma “fe” din, sai a sanya haruffan “ves” ko kuma “es” . Misali:
Singular Noun | plural Noun | Fassara |
---|---|---|
Life | Lives | Rayuwa |
Wife | Wives | Mata |
Wolf | Wolves | Kerkeci |
Thief | Theives | barayi |
Leaf | Leaves | ganyayyaki |
Knife | Knives | wukake |
Hoof | Hooves | Kofa to |
Scarf | Scarves | Kallabi |
Amma da akwai wasu kalmomin masu karewa da “Fe” ko kuma “f” wanda kawai harafin “s” ake kara masu, ba tare da an cire harafin “f” ko “Fe” ba. Misali:
Singular Noun | Plural Nouns | Fassara |
---|---|---|
Roof | Roofs | Rufin saman daki |
Chief | Chiefs | mutum mai Babbar matsayi |
Belief | Beliefs | Imani |
ALSO READ: Menene Bambanci tsakanin Present participle da kuma Past participle a turanci?
4. Idan singular Noun ya kare da harafin “o” kuma harafin dake bayan “o” din harafine (consonant), kawai za’a kara haruffan “es” ne a karshen kalma, Misali:
Singular Noun | Plural Nouns | Fassara |
---|---|---|
Potato | Potatoes | Dankali |
Hero | Heroes | Jarumi |
Mosquito | Mosquitoes | Sauro |
Tomato | Tomatoes | Tumatur |
Amma kuma da akwai kalmomin da suke karewa da “o” wanda kawai harafin “s” ake karawa. Misali:
Singular Noun | Plural Noun | Fassara |
---|---|---|
Photo | Photos | Hoto |
5. Idan singular Noun ya kare da harafin “o” kuma harafin da yake bayan “o” din wasali be (vowel), to kawai zamu kara harafin “s” a karshen kalmar. Misali:
Singular Noun | Plural Noun | Fassara |
---|---|---|
Radio | Radios | Rediyo |
Video | Videos | Bidiyo |
ALSO READ: Kalmomin Turanci masu haruffa uku (Three letters words)
6. Idan singular Noun ya kare da harafin “y” , sannan kuma letter da yake bayan ” y” din harafi ne, kawai zaka canza harafin “y” dinne, sai mu sanya haruffan “ies” a karshe. Misali:
Singular Noun | Plural Noun | Fassara |
---|---|---|
Party | Parties | Bidiri/walima |
Lady | Ladies | mata |
City | Cities | Birane |
Country | Countries | kasashe |
Puppy | Puppies | kananun karnuka |
Family | Families | Iyalai |
Amma kuma idan harafin dake bayan “y” din wasali ne (vowel), kawai zaka kara harafin “s” ba tare da ka cire harafin “y” din ba. Misali:
Singular Noun | Plural Noun | Fassara |
---|---|---|
Day | Days | Ranaku |
Toy | Toys | Yatsu |
Boy | Boys | Yara(maza) |
Key | Keys | Mukullai |
Donkey | Donkeys | Jakai |
Holiday | Holidays | Hutu |
Wadannan kalmomin sune ake kira da regular plural Noun, zamu dakata anan, sai kuma a darasi na gaba zamuci gaba Insha Allahu