Kalmomi

Yadda ake aiki da kalmar FOR a turanci

Assalamu alaikum, masu kallo da bibiyar wannan tasha ta koyan turanci. Mu na fatan kowa da kowa ya na lafiya, tare jin daɗin kasancewa da wannan tasha. A wannan bidiyo za mu yi bayani tare da misalai akan yadda ake aiki da kalmar FOR.



Kalmar FOR ana amfani da ita a gurare dadama a turanci. Saboda haka ba za mu iya kawo gaba ɗaya hanyoyin da ake aiki da ita ba. Sai dai za mu yi ƙoƙarin kawo hanyoyin da akafi amfani da wannan kalma a harkokin yau da kullum.



Na farko ana amfani da FOR domin nuna tsawon lokacin da aka shafe ko aka ɗauka ana yin wani aiki ko kuma tsawon lokacin da aka ɗauka aka yi wani aiki.



Misali:

1. She has been writing for 1 hour.

Ta na ta rubutu na tsawon sa’a ɗaya.



2. I have been here for 5 minutes.

Ina nan na tsawon mintuna 5.



3. He lived in Sokoto for 10 years.

Ya zauna a Sokoto na tsawon shekaru 10.



Ka da a shagala, idan ba ayi subscribe ba, ayi ƙoƙari ayi domin hakan shi zai ba ka damar samun saƙonnin e-mail a duk lokacin da muka ɗaura sabon darasi a wannan tasha.

Na biyu ana amfani da FOR domin nuna dalilin yin wani abu. Wato an yi wannan abun ne saboda kaza kaza.



Misali:

4. A pencil is for pupils.

Fensir an yi shi saboda ‘yan firamare.



5. The school for the blinds.

Makarantar makafi. Wato makarantar dan makafi aka yi ta.



6. She made this dinner for you.

Ta yi wannan girkin ne saboda kai.



Na uku kuma ana amfani da FOR domin nuna yin wani aiki a maimakon wani ko a madadin wani.



Misali:

7. I cooked for her.

Na yi girki a maimakonta.



8. They taught the class for us.

Sun koyar da ajin a maimakonmu.



9. He washed the clothes for me.

Ya wanke kayan a madadina.



Na hudu kuma ana amfani da FOR domin nuna aikin da akeyi da wani abu.



Misali:

10. Pen and paper are for writing.

Akan yi aiki da biro da fefa domin rubutu.



11. A phone is for making phone calls.

An yi waya ne domin kiraye kiraye.



12. A school is a place for learning.

Makaranta waje ne na koyon karatu.



Na biyar kuma gareku yake masu kallo. Ku kawo naku misalan tare da wannan kalma kamar yadda muka yi bayani.



Haka kuma idan da mai tambaya, sai ya je wajen comment ya rubuta tambayarsa, zai samu idan Allah ya sa mun sani.



Domin ci gaba da kasancewa da wannan tasha sai ayi subscribe, ku na iya bayar da gudunmawarku ta hanyar gayyato mana abokanku zuwa wannan tasha.



Mun gode.

Karatunturanci

I, Abdulmaleek Abubakar, am the founder and writer of Karatunturanci.com.ng. I have always been intrigued by the English language. Since the time when I feared it and could not speak without making a ton of mistakes to the time when most people think I'm a native English speaker and has mind-blowing knowledge of the language, my love for the English language has been intact. I come from a crowd street of Zaria, Nigeria. Except teaching and exploring the English language, I love cooking, writing poems, and watching and practising. Thank you for giving it a read!

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button