Menene Ma’anar WH question word da hausa? (Kalmomin tambaya a harshen turanci)
Ma'anar WH words a hausa
Menene Ma’anar Wh_words a turanci?
a wannan darasi insha Allahu zamuyi shine akan Wh words, da kuma yanda ake amfani dasu acikin jimla
ALSO READ: Menene ma’anar conditional sentence? (Koyon Turanci)
Menene Wh_words?
Wh_words:- wasu kalmomine da ake amfani dasu wajen gudanar da tambayoyi
akwai kalmomi da yawa dake farawa da “Wh” a cikin yaren English, amma kuma ba duka bane ake cewa “Wh words” ba.
Atakaice dai wannan darasi zamu yishi ne akan kalmomin tambaya kawai
ALSO READ: Me ake nufi da Affixation a cikin darasin turanci?
wadannan kalmomi yana da matukar muhimmanci ga dalibin turanci ya fahimce su, sannan kuma yakamata ya iya amfani dasu.
1. WHAT
What:- kalma ce da ake amfani da ita wajen neman karin bayani dangane da wani ko wani abu. Misali
- What is your name? – yaya sunan ka?/ki?
anan dai tambayace data danganci wani, kuma a farkon tambayar zakuga nafara ne da kalmar “What” wacce kalma ce mai farawa da “Wh” kamar yanda na sanar maku a farkon darasin.
- What is it? – Menene?
- What is this – menene wannan?
- What time is it? – karfe nawa ne?
2. What…for
ana yin amfani da wannan kalmar gurin “tambayar meyasa?”
Misali:
What did you do that for? – me yasa kake yin haka?
3.WHO
Who:- itama tana daya daga cikin kalmomin da akewa lakabi da Wh- words”, saboda ana amfani da ita wajen tambayar wa?. Misali:
- Who is this? – Waye wannan?
- Who is that woman? – waye wancan matar?
- Who told you? – Waya fada maka?
ALSO READ: Menene Ma’anar Pronoun (wakilin suna) da turanci?
4. WHOM
ita kuma wannan ana amfani da itane a yayin da ake son ayi tambayar wa? ko kuma wane?
Sai dai wannan tambayar ana danganta mutum ne kawai, kuma ta bambanta da “Who” da kuma “which”. Misali
ALSO READ: Bambanci tsakanin Sometime, Some time, da kuma Sometimes a turanci
Idan kana son kayi tambayar “Wane daga cikin su?”
A lokacin da tambayar ka take da dangantaka da mutane a maimakon kace “who?” ko kuma “which one?”, sai kace “Whom”. ma’ana “wane ko kuma wa?
Atakaice dai anayin amfani da “whom” ne a maimakon “who” domin yin nuni ga object (mutumin da aiki ya fadawa a cikin jimla).
Misali:
- To whom should I write? – zuwa ga wa yakamata na rubuta?
- Whom did you see? – wa kake gani?
ALSO READ: Menene Internet slang words da kuma yanda ake amfani dashi a social media (Yaren chatting)
5. WHEN
When:- itama wannan kalmar ana amfani da ita ne wajen yin tambayar yaushe?. Misali:
- When can I see you? – yaushe zan iya ganin ka?
- When are you coming? – yaushe zaka zo? zaki zo?
- When is your birthday? – yaushe ne birthday dinka?
ALSO READ: Menene Gerund Verbs a Hausa?
6. WHICH
Wannan kalmar ita ana amfani da ita ne wajen tambayar wane? ko wane iri?. Misali:
- Which one do you want? – wane iri kake so? kike so?
- Which of them is yours? – wane daga ciki naka? naki?
7. WHY
Why:- itama wannan kalmar ta wh words ana amfani da ita ne, alokacin da kake son ka tambayi mutum “Meyasa?”. Misali:
- Why were you late? – meyasa kukayi latti
- Why was he late? – meyasa yayi latti?
- Why are you crying? – meyasa kake kuka?
- Why is everyone silent? – meyasa kowa yayi shiru?
ALSO READ: Menene Ma’anar Verb da turanci da kuma rabe raben sa?
8. WHERE
Where:- yana nufin “Ina?” ko kuma “a ina?”, wato tambayar wani guri. Misali:
- Where did you bought this? – Ina ka sayo wannan?
- Where did you know that? – A ina kasan haka?
- Where do you live? – A ina kake da zama?
- Where are my boots? – Ina takalma na?
ALSO READ: Yanda ake amfani da kalmar “CAN” a turanci
9. WHOSE
Whose:- Ana amfani dashi ne domin tambayar “shin abun wanene?”, wato tambayar mallakin wani abu. Misali:
- Whose are these keys? – makullan wanene wadannan?
- Whose house is this? – shin gidan wa nene wannan?
ALSO READ: SHAWARWARI GUDA 14 DA ZASU TAIMAKA WA MUTUM YA IYA TURANCI RANGADADAU
10. How Questions
How question yana daga cikin kalmomin da ake amfani dasu gurin tambayar wani al’amari da ya faru ko zai faru. Misali:
- Did you know how this website work? – ko kasan yanda wannan shafin yake aiki?
- Can you teach me how to read? – Ko zaka iya koya mini yanda zanyi karatu?
ALSO READ: Yanda Karin “Ly” a karshen kalma yake canza ma’anar kalmar – Karatun Turanci
11. HOW MUCH
How much:- ana amfani da wannan kalmar ne gurin tambayar farashin abu ko kuma nuna yawan abu, galibi anayin amfani da wannan kalmar ne tare da Uncountable noun, wato sunan da bazai kirgu ba. Misali:
- How much are those earrings? – nawane wadannan dan kunnin azurfan?
ALSO READ: Learn English, Yadda ake amfani da “Could” a turanci
12. HOW MANY
How many:- ana amfani da wannan kalmar ne gurin tambayar adadin yawan abu, shikuma wannan yana zuwa ne tare da Countable noun (wato suna mai kirguwa). Misali:
- How many children do you have? – yara nawa gare ka?
- How many people were there? – Mutane nawa ne anan gurin?
13. HOW FAR
ana amfani da wannan kalmar gurin tambayar nisan da wani abu yake dashi. Misali:
- How far is it from your house to your school? – yaya nisan gidanka zuwa makarantar ka?
14. HOW OLD
ana amfani da How old ne gurin tambayar shekaru. Misali:
- How old are you – Shekarunka nawa ne?