Ma’anar kalmar Although da Hausa
A cikin wannan darasin zamuyi ɗan taƙaitaccen bayani ne akan ma’anar kalmar Although da Hausa
Wannan kalma na nufin duk da cewa kaza …, amma sai da kaza … ya faru. Sannan ba a sa waƙafi (comma) a gabanta, kuma a farkon jimla kaɗai ake amfani da ita. Although na nufin duk da cewa.
Misali:
Although Kande Gao is a Chinese, she speaks Hausa fluently.
Duk da cewa Kande Gao ‘yar kasar Sin (China) ce, amma ta na magana da harshen Hausa a wadace.
Although he is not well, he plays the match.
Duk da cewa ba ya jin daɗi, ya buga wasan.
Although P.S.G has Mbappé, Neymar and Messi, Real Madrid defeated it.
Duk da cewa ƙungiyar P.S.G ta na da ‘yan ƙwallo kamar su Messi, Mbappé da Neymar, amma Real Madrid ta doke ta.
Although he had never been to Katsina, he didn’t get lost when he visit Gobarau minaret.
Duk da cewa bai taba zuwa Katsina ba, amma bai yi ɓatan kai ba a lokacin da ya ziyarci Hasumiyar Gobarau.
Although the recent fuel scarcity, he gets his tank full.
Duk da ƙarancin mai da ake da a kwanan nan, ya kan samu ya cika tankin abun hawansa.
Ku ma ku kawo naku misalan tare da wannan kalma dake sama.
Ka da dai a manta ayi subscribe na channel ɗin mu mai suna Nura Mahadi dake YouTube domin koyan turanci.