Banbanci tsakanin lorry da kuma truck a turanci
Banbanci tsakanin lorry da kuma truck a turanci
Maraba da sake shiguwa shafin Koyon Turanci A Saukake. A cikin wannan darasin zamuyi ne akan banbanci dake tsakanin kalmar “lorry” da kuma “truck” a cikin turanci
Wasu kan yi tambaya cewa su kan karanta a littattafai, jaridu, da mujallu; babbar mota akan kirata lorry, a wasu littattafan kuma akan rubuta truck. To wai ya ya abun yake ne?
Wannan ba wani abu ne mai wahalar ganowa ba. Domin a turanci akwai kalmomi da ake kira synonymous. Wato mabambanta kalmomi masu ma’ana iri ɗaya. To waɗannan kalmomin ma haka suke, sai dai inda abun yake shine:
LORRY 🇬🇧 (BrE)
Lorry na nufin babbar mota kaman Daf, Iveco, Man diesel, Mark da makamantansu. Amma fa a turancin Birtaniya.
TRUCK 🇺🇸 (AmE)
Hakama, truck na nufin babbar mota kaman Daf, Iveco, Man diesel, Mark da makamantansu. Amma fa a turancin Amurka.
🇬🇧 Lorry 🚛 lorries🚛🚛🚛
🇺🇸 Truck 🚛 trucks 🚛🚛🚛
MISALI:
🇬🇧 We have delivered the goods by lorry.
🇺🇸 We delivered the goods by truck.
🇳🇬 Mun kai kayan da babbar mota.
🇬🇧 In Nigeria mostly goods are transported between South to North in lorries.
🇺🇸 In Nigeria mostly goods are transported between South to North in trucks.
🇳🇬 A Nigeria mafi akasarin kayayyaki a kan ɗakkosu daga kudu zuwa arewa a manyan motoci.
Ka da dai a manta ayi subscribe na channel ɗin mu mai suna Nura Mahadi dake YouTube.