Menene ma’anar kalmar “Pleasure” da Hausa
AMFANI DA KALMAR “PLEASURE”
Kalmar “pleasure” tana nifin Nishaɗi/Jindaɗi.
Amma ana amfani da kalmar “pleasure” a wajaje masu yawa. Amma Yau zanyi magana akan uku / huɗu a cikinsu. Insha Allah.
1). Ana amfanida shi wajan nuna amincewa da wani abu da aka nema a wajanka. Kokuma aka umarceka kayi.
Example.
Could you borrow me your pencil?’ Yes, with pleasure.
“Yes, with pleasure ” ya nuna amincewa.
2) Ana amfanida shi wajan faɗa wa wani cewa, wani aiki da ka aikata domin temakon shi, ko wani abu makamancin haka, kayi ne sabida hakan yana maka daɗi, bawani abu bane kai a gareka.
Example
Sir, Thank you very much for your help .’ It’s my pleasure.
Note. “Sir” ɗin ne yace ( It is my pleasure)
3) Ana amfanida shi a wajan nuna wini abu da yake nishaɗantar da mutum, wato aikin da kakeyi dan samun nishaɗi.
Example.
Reading is my pleasure.
4) Haka kuma ana iya amfanida shi a matsayi ‘Idiom’. “ Idioms” wasu nau in maganganune waɗanda abunda aka rubuta dakuma ma’anar da zai bayar sun banbanta.
Example.
Admin Nafisat serves the group at my pleasure.
“At my pleasure ” Na nifin yadda nakeso.
Muƙarashe yini lafiya.