Hira tsakanin Ameenat da kuma Jameelah ta waya (English to Hausa)
Hello, good evening to you all.
Barkan ku da wuni.
I am welcoming you to the class.
Inayi muku barka da zuwa aji.
In our lesson today, there is a conversation through phone call between two friends. (Ameenat and Jameelah)
A darasin namu na yau, akwai hira ne ta waya a tsakanin ƙawaye biyu.
(Ameenat and Jameelah).
Without any delay, if you are ready, let us go.
Ba tare da jinkiri ba, idan kun shirya, muje zuwa.
Ameenat
Hello Jameelah.
Barka Jameelah.
Jameelah
Yeah, who is calling?
Yauwa, wake kira?
Ameenat
Don’t you recognize the number?
Baki gane lambar bane?
Jameelah
Yes, this is because the number seems to be new to me.
Eh, saboda lambar ce kamar sabuwa agareni.
Ameenat
Okay I am Ameenat.
To nice Ameenat.
Jameelah.
Ameenat are you? Have changed your number?
Ameenat kece? Kin chanza lambar ki ne?
Ameenat
Yes, I lost my phone
Eh, wayar tawa ta faɗi.
Jameelah
Sorry, what is happening?
Yi haƙuri, to me ke faruwa?
Ameenat.
Everything is going well.
Kome ƙalau.
Jameelah
That is good. But how far?
Yayi kyau. To amma yaya?
Ameenat
I just call to ask you.
Kawai na kira ne na tambaye ki.
Jameelah
No problem, what do you want to ask?
Babu damuwa, me kike son tambaya?
Ameenat
How about the preparation of wedding ceremony of our Friend?
Yaya agame da shirye-shiryen bikin ƙawar mu?
Jameelah
The preparation is going on.
Shirye-shirye yana nan yana cigaba.
Ameenat
Have you decide the marriage attire?
Kun fitar da anko?
Jameelah
It is almost all the marriage attire are completed.
Ai an kusa gama dukkan ankon?
Ameenat
But honestly speaking I am very much disappointed.
Amma maganar gaskiya banji daɗi ba.
Jameelah.
Sorry please, why do you say that?
Kiyi haƙuri, meyasa kika ce haka?
Ameenat
Why I was not informed about that?
Meyasa ba a sanar dani hakan ba?
Jameelah.
I swear we thought you were at school.
Na rantse munyi zaton kina makarata ne.
Ameenat
Even if I was at school why shouldn’t I be informed?
Koda ina makaranta meyasa baza a sanar dani ba?
Jameelah
Don’t worry, the material is there available in shops.
Kada ki damu, kayan yana nan ana samun sa a kantuna.
Ameenat
Which kind of material have decided?
Wane irin kayan kuka fitar?
Jameelah
We decided the white lash to much the bride’s dress.
Mun fitar da farin lesh ne don ya dace da kayan amaryar.
Ameenat
Okay no problem, I will be there with you in two days.
To babu damuwa, zan kasance tare daku cikin kwana biyu.
Jameelah
Is alright, we are waiting for your arrival.
To shikenan, muna jiran isowar ki.
Ameenat
Thank, please kindly extend my special greetings to the bride.
Nagode, don Allah a isar min da gaisuwata ta musamman ga amaryar.
Jameelah
No problem by the grace of God.
Babu damuwa insha-Allah.
Ameenat
Okay bye.
To sai anjima.
Jameelah
Is alright, thank you bye.
To shikenan, nagode, sai anjima.