Amfani da Kalmomin “Can” da “Could” da kuma “would
Amfani da Kalmomin “Can” da “Could” da kuma “would”
yau kuma zamuyi bayani ne akan wadannan Kalmomin na “CAN” da “Could” da kuma “Would”
galibi anayin amfani dasune kamar haka (Don roko, Don yin tayi, Don neman izini, Don gayyata)
Idan zamu tambayi wasu domin yin wani abu sai muyi amfani da “Can” da kuma “could”. Misali:
Can you wait a moment, please? (Could you wait a moment, please?) – Shin zakayi hakuri kadan jira kadan?
I wonder if you could help me – Zanyi mamaki idan har ka taimakeni.
Idan zamuce “do you think you” sai muce “could” kada muce “can” ga Misali:
Do you think you could lend me some money until next week – Shin kana tunanin zaka ranta mini wasu kudi har sai wani sati?
Zamu iya yin amfani da will da kuma would domin tambaya, amma amfiye amfani da can da kuma could. Misali:
Would you please be quite? I’m trying to concentrate – Shin zakayi hakuri kayi shiru? Ina kokarin tattarewa
Idan kuma zamu tambayi wani Abu a wurin wasu kuma sai muyi amfani da (can I have) ko (could I have). Misali:
Could I have the salt? please – Shin zan samu gishiri kuwa? yi hakuri.
Can I have these books? please – Shin zan samu wadannan littatafan kuwa? yi hakuri
Sannan kuma zamu iya amfani da (may I have); sai dai ba’a cika amfani dashi ba. Misali:
may I have these books? please – Zan samu takardunnan kuwa? yi hakuri
Domin tambaya akan neman izinin yin wani abu sai muyi amfani da can, could, may. Misali:
Hello, can you speak Tijjani, please? – Sannu, shin zan iya magana da Tijjani kuwa, yi hakuri?
Could I use your phone please? yes of course – Shin zan iya amfani da wayar ka? Yi hakuri, eh mana zaka iya mana
Do you think I could borrow your bike? – Shin kana tunanin zan ari keken kane
May I come in? – Shin zan iya shigowa ciki?
Domin bada izini kuma zamuyi amfani da can da may. Misali:
You can use the phone, or you may use the phone – Zaka iya amfani da wayar.
Domin neman bukata kuwa sai muyi amfani da can I. Misali:
Can I get you a cup of coffee? yes, that would be very nice – Shin zan samar maka kofin shayi? Eh, dakuwa yayi kyau irin sosai din nan
Can I help you? No, it’s alright, I can manage – Shin zan iya taimakonka? A’a, Shikenan, zanyi maneji
Domin tayin gayyata kuma sai muce would you like. Misali:
Would you like a cup of coffee? yes, please – Shin kana bukatar kofin shayi? Eh, yi hakuri
Would you like to come to dinner tomorrow evening? yes, I had love too – Shin kana bukatar zuwa wurin cin abinci gobe da yamma? Eh, inaso sosai ma kuwa
ananne zamu dakata da wannan darasin namu, kudai kawai kucigaba da kasancewa a cikin wannan shafin domin koyon harshen turanci a hausa, don neman Karin bayani ko tambaya sai ka/ki/ku yi mana comment. Mungode